Dattawan Arewa Sun Kawo Sabon Salo a Tsarin Marawa ’Yan Takara Baya a 2027

Dattawan Arewa Sun Kawo Sabon Salo a Tsarin Marawa ’Yan Takara Baya a 2027

  • Kungiyar dattawan Arewa (ACF) ta bayyana cewa ba za ta mara wa kowane dan takarar shugaban kasa baya ba a zaben badi
  • ACF za ta gayyaci masu neman shugabancin kasa domin jin shirye-shiryensu game da tsaro, talauci, ilimi da bunkasar Arewa
  • Kungiyar ta ce za ta goyi bayan tsare-tsare da manufofi ne kawai, ba jam’iyya ko mutum ba, domin kare hadin kan Arewa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kaduna - Kungiyar Arewa Consultative Forum (ACF) ta bayyana cewa ba za ta mara wa kowane dan takarar shugaban kasa baya a 2027 ba.

Kungiyar ta ce a cikin watanni shida masu zuwa, za ta tattauna da masu neman shugabancin kasa domin tantance shirye-shiryensu na magance matsalolin tsaro da talauci.

Kungiyar ACF ta magantu kan yan takara a 2027
Tsofaffin yan takarar shugaban kasa, Rabiu Kwankwaso, Peter Obi da Atiku Abubakar. Hoto: Kwankwasiyya Reporters, Peter Obi, Atiku Abubakar.
Source: Facebook

ACF za ta kalubalanci ‘yan takara a 2027

Yayin zantawa da Leadership, sakataren yada labarai na ACF ta kasa, Farfesa T. A. Muhammad-Baba, ya ce za a bukaci dukkan masu neman shugabancin kasa.

Kara karanta wannan

An fadi shekarun da mulki zai yi a Kudu kafin ya dawo yankin Arewa

Ya ce za su yi hakan ne domin su bayyana yadda za su tinkari kalubalen tsaro, talauci, ilimi da raya tattalin arziki idan aka zabe su.

Ya bayyana cewa manyan ‘yan siyasar da ake hasashen za su nemi shugabancin kasa a 2027 sun hada da Bola Ahmed Tinubu, Atiku Abubakar, Peter Obi, Chibuike Amaechi, Gbenga Olawepo-Hashim da Adewole Adebayotsarin .

Ko da yake ACF ta ce ba za ta mara wa kowa baya a 2027 ba, kungiyar ta tuna cewa a 2019 ta goyi bayan Muhammadu Buhari na APC, amma ba ta goyi bayan kowa ba a zaben 2015 da 2023.

Kungiyar ta kuma ce ba ta mara wa kowane dan takara baya a 2023 ba, inda aka fafata tsakanin Bola Tinubu (APC), Atiku Abubakar (PDP), Peter Obi (LP) da Rabiu Musa Kwankwaso (NNPP).

Farfesa Muhammad-Baba ya ce ACF za ta ci gaba da tsarinta na gayyatar ‘yan takara domin su bayyana manufofinsu ga Arewa, kamar yadda ta yi a zaben 2023.

Ya ce kungiyar za ta shirya takardar matsayar Arewa wadda za a mika wa wanda ya lashe zaben 2027, domin nuna hanyoyin magance matsalolin yankin.

Kara karanta wannan

Atiku ko Peter Obi?: ADC ta yi magana kan wanda za ta ba tikitin takara a 2027

Ya tunatar da cewa a 2023, Atiku Abubakar da Rabiu Musa Kwankwaso ba su halarci taron ACF ba, duk da gayyatarsu, yayin da Bola Tinubu da Peter Obi suka halarta.

A cewarsa:

“Ba za mu goyi bayan wani dan takara ko jam’iyya ba a 2027, domin kungiyarmu ta kunshi mambobi daga jam’iyyu daban-daban. Abin da za mu goyi baya shi ne tsare-tsare da ra’ayoyin da suka dace da muradun Arewa.”
Tinubu na daga cikin wadanda ACF za ta kalubalanta a 2027
Shugaba Bola Tinubu yayin taro a Abuja. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu.
Source: Twitter

Matsayar ACF game da 'yan takara a Najeriya

Tsohon sakatare janar na ACF, Anthony Sani, ya tabbatar da wannan matsaya, yana mai cewa ACF ba ta daukar bangaren siyasa, domin hakan na iya raba kan mambobinta.

Shi ma shugaban kwamitin amintattu na ACF, Alhaji Bashir Dalhatu, ya ce Arewa ba za ta goyi bayan wani mutum ko jam’iyya ba, illa wadanda suka nuna gaskiya wajen kare muradun yankin Arewa, cewar Daily Post.

ACF ta damu da matsalar tsaro a Arewa

Kun ji cewa kungiyar ACF ta bayyana fargaba kan yadda rashin tsaro ke karuwa a dukkanin sassan Arewacin Najeriya.

Shugaban kwamitin amintattun kungiyar, Alhaji Bashir Muhammad Dalhatu ya ce akwai babbar barazana a yankin.

Ya yi takaicin yadda matakan yaki da rashin tsaro ba su dakile matsalar da ake fama da ita a Arewacin kasar nan.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.