Mataimakin Shugaban NNPP Ya Tono Wata Doka, Ya Dora Gwamna Abba a Saman Kwankwaso
- Mataimakin shugaban NNPP na kasa, Alhaji Sani Danmasani ya ce Gwamna Abba Kabir Yusuf na Kano ne jagoran jam'iyyar
- Danmasani ya jaddada cewa NNPP ta kori dan takararta na shugaban kasa a zaben 2023, Rabiu Kwankwaso da wasu 'yan Kwankwasiyya
- Ya ce Kwankwaso na da yancin tattaunawa da kowace jam'iyya amma ba shi da hurumin wakiltar jam'iyyar NNPP mai adawa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kano, Nigeria - Manyan jiga-jigan NNPP musamman a Arewacin Najeriya na ci gaba da sauka daga tafiyar tsohon dan takarar shugaban kasa, Rabiu Musa Kwankwaso.
Mataimakin shugaban NNPP na kasa (Arewa maso Yamma), Alhaji Sani Danmasani ya ce Gwamna Abba Kabir Yusuf ne jagoran jam'iyyar, ba Sanata Rabiu Kwankwaso.

Source: Facebook
Danmasani ya bayyana haka ne a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Talata 6 ga watan Junairu 2026, kamar yadda Vanguard ta tattaro.
Dalilin da Abba ya zama jagoran NNPP
Ya ce bisa kundin tsarin mulkin NNPP, gwamnan Kano shi ne jagoran jam’iyyar, kasancewar shi ne gwamaa daya tilo da take da shi a fadin kasar nan.
Jigon ya ce Kwankwaso ya yi takarar shugaban kasa a inuwar NNPP a zaben 2023 ne kawai, kuma wannan tsari ya kare ne bayan kammala zaben.
Ya kuma jaddada cewa jam'iyyar NNPP ta kori wasu daga cikin 'yan Kwankwasiyya, ciki har da Kwankwaso saboda sun aikata laifin da ya saba wa dokokinta.
Danmasani ya ce:
“Ba labari ba ne, mun riga mun kori wasu manyan mambobin Kwankwasiyya, ciki har da Kwankwaso, daga NNPP bisa zargin ayyukan da suka saba wa jam’iyya.”
Tsagin NNPP ya jaddada korar Kwankwaso
Danmasani ya nuna damuwa kan yadda kafafen yada labarai ke ci gaba da kiran Kwankwaso a matsayin jagoran NNPP, yana mai cewa wannan kuskuren bayani ya jawo jam'iyyu na tuntubar Kwankwaso da sunan NNPP.
“Muna sake jaddada cewa ba za mu hana tattaunawar kawancen siyasa da Kwankwaso da tafiyar Kwankwasiyya ba, amma ba da sunan jam'iyyar NNPP ba.
“Dr. Boniface Aniebonam, wanda shi ne wanda ya kafa jam’iyyar kuma mamban kwamitin amintattu (BoT), tare da kwamitin zartarwa na Kasa karkashin jagorancin Dr. Agbo Gilbert, su kadai ke da ikon yin irin wadannan tattaunawa a madadin NNPP."
"Kwankwaso da kungiyarsa suna da ‘yancinsu na yan Najeriya su shiga tattaunawa ko su shiga kowace jam’iyya da suka ga dama, amma ba a matsayin mambobin NNPP ba."
- In ji Alhaji Danmasani.

Source: Facebook
Ya kuma roki Kwankwaso da ya daina amfani da sunan NNPP wajen yin kalamai ko jefa zargi ga jam’iyya mai mulki da kuma shugabancin kasa, cewar Daily Post
Gwamna Abba ya dage kan komawa APC
A wani labarin, kun ji cewa gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya nace kan shawarar da yanke ta fita daga NNPP tare da komawa APC.
Wasu hadiman gwamnan sun jaddada cewa Abba ya riga ya yanke shawara kuma ba gudu ba ja da baya, babu wani abu da zai sa ya janye shirinsa.
Sai dai majiyoyi sun ce ba a kayyade wata rana da gwamnan zai koma APC ba tukuna, suna mai bayanin cewa gwamnan na ci gaba da yin shawarwari da masu ruwa da tsaki.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

