Tuna Baya: Yadda Gwamna Abba Ya Yi Alkawarin Kin Yi Wa Kwankwaso Butulci
- Ana ci gaba da maganganu kan shirin sauya shekar da gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ke yi daga jam'iyyar NNPP zuwa APC mai mulkin kasa
- Wasu dai na kallon shirin sauya shekar a matsayin butulci ga ubangidansa na siyasa kuma jagoran Kwankwasiyya, Rabiu Musa Kwankwaso
- Wani tsohon bidiyo ya bayyana inda ya nuna Gwamna Abba na jaddada biyayyarsa ga Kwankwaso yayin da ake kiran ya tsaya da kafarsa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Kano - Rikicin siyasa na kara kamari a jihar Kano sakamakon rahotannin da ke cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf na shirin ficewa daga jam’iyyar NNPP zuwa APC.
Wani tsohon bidiyo da aka ɗauka kusan a watan Yuli na shekarar 2024, ya fito wanda ke nuna gwamnan yana jaddada biyayyarsa ga Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ya sake bayyana kuma ya yaɗu a kafafen sada zumunta.

Kara karanta wannan
Dalilanmu na son Kwankwaso ya ja Abba zuwa APC inji Hadimin Gwamna Alhajiji Nagoda

Source: Facebook
Jaridar Leadership ta ce tsohon bidiyon da ya sake yaduwa ya ja hankalin jama’a a wannan lokaci da ake kara rade-radin cewa Gwamna Yusuf na iya sauya sheka zuwa APC a cikin wannan watan na Janairu.
An tono tsohon bidiyon Gwamna Abba
A cikin bidiyon, wanda aka ɗauka yayin wata tattaunawa da ’yan jarida da daddare a gidan gwamnati na Kano, Gwamna Abba ya musanta jita-jitar cewa akwai sabani tsakaninsa da Kwankwaso.
A wancan lokacin, ya bayyana maganganun sabani tsakaninsa da Kwankwaso a matsayin cin fuska da yunkurin rarrabuwar kai.
“Idan suka ce in tsaya da kafata, suna zagina ne kuma kai tsaye suna raina duk abin da gwamnatina ta cin ma."
- Gwamna Abba Kabir
Gwamna Abba yana yaba wa Kwankwaso
Gwamnan ya jaddada cewa aminci da biyayya sune ginshiƙan siyasar sa da kuma al’adar mutanen Kano, inda ya ce:
“Allah ne ya ba ni damar zama gwamna, amma goyon bayan Kwankwaso ne ya sa hakan ta tabbata. Me zai sa in ci amanarsa?”
Ya kara da cewa mutanen da ke yaɗa irin waɗannan labarai suna kokarin haddasa rikici ne da gangan, yana mai jaddada cewa hankalinsa yana kan mulki da yi wa al’ummar Kano hidima.
A cikin wannan tsohon bidiyo da ya sake yaɗuwa, Gwamna Yusuf ya kuma karyata rahotannin da ke cewa yana kin ɗaukar kiran wayar Kwankwaso.
Ya bayyana cewa ya guji ɗaukar matakin shari’a a kan wata kafar yaɗa labarai da ta wallafa rahoton, saboda girmamawa ga aikin jarida.

Source: Facebook
Gwamna na shirin rabuwa da Kwankwaso
Sake fitowar bidiyon ya zo ne a lokacin da Gwamna Abba ya ki cewa komai kan jita-jitar sauya sheka da ake danganta masa, lamarin da ya kara jefa siyasar jihar cikin ruɗani da hasashe.
Sai dai kuma jagoran tafiyar Kwankwasiyya kuma tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ya fito fili ya ki amincewa da kiran da ake yi wa Gwamna Yusuf na sauya sheƙa zuwa APC.
Kwankwaso ya aika sako ga masu raina NNPP
A wani labarin kuma, kun ji cewa madugun Kwankwasiyya, Rabiu Musa Kwankwaso, ya aika da sakon gargadi ga masu raina jam'iyyar NNPP.

Kara karanta wannan
Gwamna Abba ya kafe kan komawa APC, an ji adadin jiga jigan da za su tafi tare da shi
Kwankwaso ya gargadi abokan adawar siyasa da ke raina jam’iyyar da su shirya ganin abin mamaki a zaɓen shekara mai zuwa.
Kwankwaso ya bayyana cewa NNPP za ta ba waɗanda suke ganin jam’iyyar ta mutu mamaki ta hanyar sakamakon zaɓen 2027.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
