Jagora a APC Ya Hango Abin da zai Wargaza Jam'iyya, Ya Bada Shawara tun Wuri

Jagora a APC Ya Hango Abin da zai Wargaza Jam'iyya, Ya Bada Shawara tun Wuri

  • Wani jigo a APC ya ce jam’iyya mai mulki na fuskantar barazanar rugujewa idan ba a kula da lamarin masu sauya sheƙa ba
  • Cif David Sabo Kente ya yi gargadin cewa yayin da ake karban sababbin mutane a APC, ana mayar da na ciki saniyar ware a jam'iyya
  • Gargadin Kente kan barazanar rugujewar jam’iyya na zuwa ne a lokacin da gwamnonin Najeriya, Sanatoci da jiga-jigan adawa ke komawa APC

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – Wani jigo a APC a Jihar Taraba, Cif David Sabo Kente, ya yi gargaɗin cewa jam’iyyar na iya rugujewa.

Ya bayyana cewa wannan barazana za ta tabbata idan ba a tafiyar da yawaitar masu sauya sheƙa zuwa APC cikin hikima da adalci ba.

Kara karanta wannan

Yadda gobara ta tashi a kasuwar Sakkwato, ta shafe shaguna sama da 40

Jagora a APC ya yi gargadi kan rushewar jam'iyya
Shugaban Kasa Bola Tinubu, Shugaban APC Yilwatda Nentawe Hoto: Bayo Onanuga/Prof Yilwatda Nentawe
Source: Twitter

Jaridar The Sun ta wallafa cewa Kente ya bayyana hakan ne a saƙon sabuwar shekara da ya aike wa manema labarai a ranar Litinin.

Jigon APC ya hango wa jam'iyya matsala

Cif David Sabo Kente ya jaddada cewa wasu daga cikin sababbin masu sauya sheka zuwa APC shiga sun karɓi ragamar jagoranci tare da mallakar tsarinta.

Ya nanata cewa wajibi ne su tabbatar da cewa ba a mayar da waɗanda suka gina jam’iyyar tsawon shekaru saniyar ware ba.

Cif Sabo Kente ya shawarci APC ta yi lamarin sauya sheka tufka
Shugaban APC na kasa, Yilwatda Nentawe Hoto: Prof Yilwatda Nentawe
Source: Twitter

A cewarsa, idan aka yi watsi da tsofaffin ‘yan jam’iyya, hakan na iya janyo zanga-zanga da kuma rushewar kwanciyar hankalin da ake da shi a jam’iyyar a halin yanzu.

“Nan gaba kaɗan, muna sa ran waɗanda suka sauya sheƙa daga wasu jam’iyyu zuwa APC, kuma suka karɓi ko suke shirin karɓar tsarin, su kasance masu tausayi, su tabbatar mun zauna lafiya tare, kowa ya samu dama."
“In ba haka ba, jam'iyya na iya rushewa kuma hakan zai zama tashin hankali. Don haka yana da muhimmanci mu yi abin da ya dace domin mu shiga zaɓe mai zuwa da karfinmu."

Kara karanta wannan

An 'gano' wadanda ke zuga Abba Kabir ya yi watsi da Kwankwaso, ya shiga APC

Jagoran APC ya nemi a hada kai

Cif David Sabo Kente ya bayyana cewa, saboda nuna adawa a baya, wasu daga cikinsu sun yi aiki wajen kawo gwamnan da ke kan mulki tun yana jam’iyyar PDP.

Duk da haka, ya ce har yanzu yana da kyakkyawar mu’amala da gwamnan, yana mai fatan akwai damar gyara da sasanci.

A kalamansa:

“Har yanzu alakar tana da kyau, ko da yake wasu mugaye na hura wutar rarrabuwar kai. Ina fatan shugabannin siyasa ba za su faɗa tarkonsu ba."

Haka kuma, ya roƙi gwamnatocin jiha da tarayya da su hanzarta samar da nagartaccen shugabanci da ribar dimokuraɗiyya ga al’umma.

Abin da zai kai gwamnan Kano APC

A baya, mun ruwaito cewa gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, na ci gaba da shirye-shiryen sauya sheƙa daga jam’iyyar NNPP zuwa APC mai mulkin kasa.

Manyan hadiman gwamnan sun tabbatar da cewa shawarar sauyin jam’iyyar ta zama tabbatacciya, kuma babu wata alama ta janyewa kamar yadda ake hasashe.

Ɗaya daga cikin hadiman gwamnan ya shaida cewa batun sauya sheƙar ya wuce siyasar Kano kaɗai, domin yana da alaƙa kai tsaye da fadar Shugaban 'Kasa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng