Abin Boye Ya Fito: Dalilan da Suka Sanya Gwamna Abba Zai Rabu da NNPP zuwa APC

Abin Boye Ya Fito: Dalilan da Suka Sanya Gwamna Abba Zai Rabu da NNPP zuwa APC

  • Bisa ga dukkan alamu gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ba zai sake shawara ba kan shirin sauya sheka daga jam'iyyar NNPP zuwa APC
  • Majiyoyi sun bayyana cewa shirin sauya shekar gwamnan ya shafi fadar shugaban kasar Najeriya kai tsaye ba iyaka Kano da yake mulki ba
  • Sun bayyana dalilan da sukan sanya Gwamna Abba ya yanke shawarar rabuwa da NNPP da ubangidansa a siyasance, Rabiu Musa Kwankwaso

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Kano - Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, na ci gaba da shirye-shiryen sauya sheka daga jam'iyyar NNPP zuwa APC.

Manyan hadiman gwamnan sun jaddada cewa shawarar sauya shekar ta zama tabbatacciya kuma ba za a janye ta ba.

Gwamna Abba ya kammala shirin komawa jam'iyyar APC
Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano Hoto: Abba Kabir Yusuf
Source: Facebook

Ɗaya daga cikin hadiman gwamnan ya shaida wa jaridar Daily Trust hakan a ranar Litinin, 5 ga watan Janairun 2025.

Kara karanta wannan

Gwamna Abba ya kafe kan komawa APC, an ji adadin jiga jigan da za su tafi tare da shi

Babu fashi kan sauya shekar Gwamna Abba

Ya bayyana cewa shawarar gwamnan ta sauya sheka zuwa APC ba batun Kano kaɗai ba ne, illa lamari ne da ya shafi fadar shugaban kasa kai tsaye.

Shirin sauya shekar gwamnan ya mamaye tattaunawar siyasa a jihar tun makon da ya gabata, inda rahotanni suka nuna cewa an tsara ranar 5 ga Janairu domin sanar da sauyin a hukumance.

Sai dai majiyoyi sun ce ba a kayyade wata rana ba tukuna, suna mai bayanin cewa gwamnan na ci gaba da yin shawarwari da masu ruwa da tsaki domin tabbatar da cewa sauyin ba zai kawo tangarda ga tafiyar mulki a jihar ba.

Dalilin da ya sa Gwamna Abba zai koma APC

Hadimin ya bayyana cewa shawarar gwamnan ta sauya sheka ta samo asali ne bisa la’akari da tafiyar mulki da walwalar al’ummar jihar Kano, ba wai saboda son rai ko buri na siyasa kaɗai ba.

“Hakika buri na siyasa yana da muhimmanci, amma jam’iyyar NNPP ta zama ba ingantaccen zabin sake tsayawarsa takara ba. Jam’iyyar yanzu tana nan ne kawai a rubuce."

Kara karanta wannan

Gwamna Abba ya dage lokacin komawa jam'iyyar APC, an ji dalili

- Hadimin gwamna

Ya kara da cewa babban burin gwamnan shi ne tsayar da Kano a matsayin jihar da za ta fi cin gajiyar tallafi da ayyukan gwamnatin tarayya.

A cewarsa, manyan ayyuka da dama a jihar na bukatar sa hannun gwamnatin tarayya domin kammala su.

“Kano ita ce jiha mafi yawan al’umma a Najeriya, da mutane sama da miliyan 22. Duk da kasafin kuɗi na Naira tiriliyan 1.47, jihar ba za ta iya warware manyan kalubalen ayyuka ita kaɗai ba."

- Hadimin gwamna

Gwamna Abba na shirin sauya sheka zuwa APC
Mai girma gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf Hoto: Abba Kabir Yusuf
Source: Facebook

Ya ambaci aikin Wujuwuju da aka fara a zamanin mulkin Kwankwaso, inda ya ce duk da an yi masa karin kuɗi na Naira biliyan 47, yanzu aikin na bukatar sama da Naira biliyan 100 domin kammalawa, yayin da tallafin gwamnatin tarayya ya tsaya ne a Naira biliyan 47.

Akwai batun matsalar tsaro a Kano

Haka kuma ya nuna tabarbarewar tsaro a matsayin muhimmin dalili.

“Matsalar ‘yan bindiga babbar damuwa ce. Ba za mu yi wasa da haɗin gwiwa tsakanin gwamnatin jiha da hukumomin tsaro na tarayya ba. Rayuka da dukiyoyi na cikin haɗari."

Kara karanta wannan

"Abin da ya fi mani ciwo game da sauya shekar Gwamna Abba zuwa APC," Kwankwaso

- Hadimin gwamna

A cewarsa, rikicin cikin gida da ke addabar jam’iyyar NNPP, tare da lalacewar dangantaka tsakanin gwamnan da Kwankwaso, su ma sun taka muhimmiyar rawa wajen yanke wannan shawara.

“Wadannan dalilai ne suka sa gwamnan ya ɗauki wannan mataki, kuma shawarar ta zama tabbatacciya, ba tare da la’akari da matsin lamba daga tsohon ubangidansa na siyasa, Kwankwaso ba, wanda mun san har ya yanke shawarar hana gwamnan samun wa’adi na biyu."

- Hadimin gwamna

Tinubu ya taya Gwamna Abba murna

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, ya aika da sakon taya murna ga gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf.

Shugaba Tinubu ya taya Gwamna Abba murnar zagayowar lokacin haihuwarsa wadda ta kama ranar Litinin, 5 ga watan Janairun 2026.

Mai girma Tinubu ya bayyana Gwamna Yusuf a matsayin shugaba mai mutunci, kan-kan da kai, saukin kai da jajircewa wajen aikin gwamnati.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng