Gwamna Abba Ya Kafe kan Komawa APC, an Ji Adadin Jiga Jigan da Za Su Tafi Tare da Shi

Gwamna Abba Ya Kafe kan Komawa APC, an Ji Adadin Jiga Jigan da Za Su Tafi Tare da Shi

  • Ana ci gaba da tattaunawa kan batun yunkurin sauya shekar da gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf yake yi daga jam'iyyar NNPP zuwa APC
  • Tun da farko an tsara gwamnan zai koma APC a ranar Litinin, 5 ga watan Janairun 2026 amma daga baya aka dage lokacin
  • Wata majiya ta ba da tabbacin cewa ba gudu ba ja da baya kan sauya shekar gwamnan duk adawar da Rabiu Musa Kwankwaso yake yi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Kano - Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, na shirin sauya sheka daga jam’iyyar NNPP zuwa APC mai mulki a Najeriya.

Wata majiya ta ba da tabbacin cewa ba gudu ba ja da baya kan shirin sauya shekar Gwamna Abba zuwa jam'iyyar APC.

Gwamna Abba Kabir Yusuf na shirin komawa APC
Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf Hoto: @KyusufAbba
Source: Facebook

Jaridar Leadership ta ce wata majiya mai karfi daga cikin gwamnatin jihar ta shaida mata hakan a ranar Lahadi, 4 ga watan Janairun 2026.

Kara karanta wannan

Gwamna Abba ya dage lokacin komawa jam'iyyar APC, an ji dalili

Rabiu Kwankwaso ya gargadi Gwamna Abba

Wannan na zuwa ne duk da gargadin da jagoran NNPP na kasa kuma shugaban tafiyar Kwankwasiyya, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ya yi cewa gwamna ya sauka daga mukaminsa idan ya bar jam’iyyar.

Kwankwaso wanda yake jagoran Kwankwasiyya, ya bukaci Abba Yusuf da ya mika kujerar gwamna idan ya sauya sheka daga NNPP, yana mai cewa kuri’un da aka kada na jam’iyyar ne.

Haka kuma, Kwankwaso ya bayyana cewa a shirye yake ya hada kai da kowace jam’iyya da za ta amince ta tsayar da shi a matsayin dan takarar shugaban kasa ko mataimakin shugaban kasa a zaben nan gaba.

Gwamna Abba ba zai fasa shiga APC ba

Sai dai wata majiya mai karfi a fadar gwamnatin Kano ta bayyana cewa ficewar Gwamna Abba Kabir Yusuf zuwa APC ta kammala kuma ba abin da za fasa ba ne.

A cewar majiyar, ana sa ran gwamnan zai tafi tare da magoya bayansa na siyasa a fadin jihar, ciki har da ‘yan majalisar wakilai tara daga cikin 13 na jihar Kano.

Kara karanta wannan

"Abin da ya fi mani ciwo game da sauya shekar Gwamna Abba zuwa APC," Kwankwaso

Sauran su ne 'yan majalisar dokokin jiha 20 daga cikin 27, ciki har da kakakin majalisa da dukkan manyan shugabannin majalisar da kuma shugabannin kananan hukumomi 42 daga cikin 44.

Majiyar ta kara da cewa kin amincewar Kwankwaso da shiga APC na da nasaba da gazawarsa ta samun damar tsayawa takarar shugaban kasa ko mataimakin shugaban kasa a jam’iyyar.

Abba ya karbe ragamar NNPP a Kano

Game da rikicin cikin gida na NNPP, majiyar ta ce Gwamna Abba Yusuf ya riga ya karbi ragamar tsarin jam’iyyar a jihar Kano.

Hakan ya biyo bayan dakatar da tsohon shugaban jam’iyyar na jiha, Hashimu Dungurawa, matakin da babbar kotun jihar Kano ta amince da shi.

Majiyar ta ce wannan lamari ya sanya kwamitin gudanarwa na kasa (NWC) na NNPP cikin raina umarnin kotu, saboda rushe shugabannin jam’iyyar daga matakin mazabu zuwa jiha duk da umarnin kotu da ke aiki.

Gwamna Abba Kabir na shirin barin NNPP zuwa APC
Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano Hoto: @KyusufAbba
Source: Facebook

Ba a ji bakin kakakin Gwamna Abba ba

Kokarin jin ta bakin kakakin gwamnan, Sanusi Bature, bai yi nasara ba, domin tun bayan barkewar rikicin ya daina tattaunawa da kafafen yada labarai.

Sai dai kuma masu bibiyar harkokin siyasa a Kano na ganin cewa matakin Gwamna Abba Yusuf ba cin amana ba ne, illa dai dabara ce ta siyasa don daidaita kansa da gwamnatin tarayya, domin kare makomar siyasarsa da kuma samun karin alfanu ga jihar Kano.

Kara karanta wannan

An 'gano' wadanda ke zuga Abba Kabir ya yi watsi da Kwankwaso, ya shiga APC

Gwamna Abba ya daga lokacin komawa APC

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya dage lokacin komawa jam'iyyar APC.

Matakin na zuwa ne bayan tun da farko Gwamna Abba ya shirya komawa APC a ranar Litinin, 5 ga watan Janairun 2026.

Majiyoyi sun bayyana cewa gwamnan ya dage lokacin ne domin ci gaba da yunkurin jawo 'yan majalisar wakilai na jihar zuwa bangarensa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng