APC ko ADC: Kwankwaso Ya Yi Magana kan Ficewa daga NNPP zuwa Wata Jam'iyya
- An fara hasashen cewa tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso na shirin sauya sheka zuwa wata jam'iyya
- Jagoran tafiyar Kwankwasiyya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya tabo batun sauya sheka daga jam'iyyar NNPP zuwa wata jam'iyya
- Sanata Kwankwaso ya bayyana cewa zai ci gaba da zama a jam'iyyar NNPP tare da 'yan tawagarsa ta Kwankwasiyya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Kano - Jagoran tafiyar Kwankwasiyya, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, tare da jiga-jigan Kwankwasiyya na Kano, sun yi magana kan sauya sheka zuwa wata jam'iyya.
Kwankwaso da jiga-jigan na Kwankwasiyya sun nesanta kansu daga rahotanni da kiraye-kirayen jama’a da ke cewa ana shirin sauya sheka zuwa wata jam’iyya daga bangaren jagoran tafiyar ko wasu mambobinta.

Source: Facebook
Jaridar Daily Trust ta ce an bayyana hakan ne a cikin sanarwar da aka fitar bayan wani dogon taro da aka gudanar ranar Juma’a, 2 ga Janairu, 2026, a dakin taro na Amana, Kwankwasiyya House, da ke Miller Road, Kano.

Kara karanta wannan
Kano ta dauki zafi, Kwankwaso ya fito ya yi magana kan komawa APC tare da Gwamna Abba
Kwankwasiyya ta fitar da sanarwa
Sanarwar ta samu sa hannun Magaji Mato Ibrahim, SAN, wanda shi ne shugaban jiga-jigan Kwankwasiyya na Rano kuma mai ba jam’iyyar NNPP shawara kan harkokin shari’a na kasa.
Dangane da kudurorin da aka cimma a taron, jiga-jigan sun yi watsi gaba ɗaya da abin da aka kira “labaran sauya sheka da ba a amince da su ba", yana mai jaddada cewa irin wadannan kiraye-kirayen ba su dace da akidar Kwankwasiyya ko tsarin tafiyarta ba.
Wani bangare na sanarwar na cewa:
“Tafiyar Kwankwasiyya ta nesanta kanta sarai kuma ba tare da shakka ba daga duk wani kira, bayani ko rahoton kafafen yada labarai da ke neman Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ko mambobin tafiyar su sauya sheka zuwa wata jam’iyya."
Jiga-jigan sun kuma fayyace wa mambobi, magoya baya da al’umma cewa wadannan kiraye-kirayen karya ne, masu ruɗani, ba tare da izini ba, kuma ya dace a yi watsi da su gaba ɗaya.

Kara karanta wannan
Rigima ta kara zafi a Kano, Kwankwaso ya fara duba yiwuwar ficewa daga jam'iyyar NNPP
Kwankwaso ba zai sauya sheka ba
Sun amince cewa wasu daga cikin mutanen da suka yi irin wadannan kalamai na iya yin hakan ne saboda rashin cikakken bayani ko matsin lamba daga waje.
Haka kuma sun gargadi mambobi da su guji yin kalamai ba tare da izini ba, tare da yin yaki da jita-jita da bayanan karya bisa tsarin ladabi da horon tafiyar.
Da suke sake jaddada matsayarsa ta siyasa, jiga-jigan sun ce Sanata Kwankwaso da daukacin Tafiyar Kwankwasiyya suna nan daram a cikin jam’iyyar NNPP.

Source: Twitter
Sun kara da cewa ba a bai wa wani mutum ko kungiya umarni, amincewa ko kwarin gwiwar tayar da batun sauya sheka ba.
Hakazalika sun bayyana cewa duk wani mataki na siyasa za a sanar da shi ne kawai ta hanyoyin shugabanci da aka amince da su, kuma daga bakin jagoran tafiyar.
Batun shugabancin jam'iyyar NNPP a Kano
Game da rikicin shugabanci da ke ci gaba da addabar NNPP a Kano, jiga-jigan sun amince da rushewar shugabannin jam’iyyar na jiha, kananan hukumomi da mazabu da kwamitin gudanarwa na kasa (NWC) ya yi.

Kara karanta wannan
Kwankwaso ya tara 'yan Kwankwasiyya a;hali Abba na shirin hada kai da Ganduje a APC
Saboda haka, sun yanke hukuncin cewa a halin yanzu babu wata sahihin shugabancin NNPP a kowane mataki a jihar Kano.
Hakazalila sun jaddada cewa babu wani mutum ko kungiya da ke da izinin yin magana ko daukar mataki a madadin jam’iyyar, har sai an fitar da sabon umarni daga hukumomin jam’iyyar na kasa da kuma shugabancin Kwankwasiyya.
A karshe, sun bukaci mambobin tafiyar da su ci gaba da kasancewa cikin natsuwa, ladabi tare da gujewa jita-jita, hasashe da hira da kafafen yada labarai ba tare da izini ba, domin kare hadin kai da dunkulewar tafiyar.
Kwankwaso ya yi yunkurin tsige Gwamna Abba
A wani labarin kuma, kun ji cewa an samu bayanai kan dambarwar siyasar da ta auku tsakanin Gwamna Abba Kabir Yusuf da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.
Wasu bayanai sun nuna cewa Kwankwaso ya yi yunkurin sa 'yan Majalisar Dokokin Kano su tsige Gwamna Abba bayan samun labarin shirinsa na komawa APC.
Sai dai, shirin Kwankwaso ya rushe ne bayan ya kira zama da mambobin majalisar, wadanda suka fada masa suna tare da Gwamna Abba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng