Tirkashi: Kwankwaso Ya Bi Hanyoyi 2, Ya Yi Yunkurin Tsige Abba daga Kujerar Gwamnan Kano
- Ana zargin jagoran jam'iyyar NNPP na kasa, Dr. Rabiu Kwankwaso ya yi yunkurin tsige gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf daga kan karahar mulki
- Wata majiya ta bayyana cewa an fara samun sabani tsakanin jiga-jigan biyu daga lokacin da Kwankwaso ya fahimci Abba ya rage masa biyayya
- An ce Kwankwaso ya shirya maye gurbin Abba da mataimakinsa, Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo amma 'yan Majalisa suka juya masa baya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kano, Nigeria - Rahotanni na kara fitowa kan abin da ya jawo rigima tsakanin jagoran NNPP na kasa, Rabiu Musa Kwankwaso da Gwamna Abba Jabir Yusuf na jihar Kano.
Wasu bayanai da suka kara fitowa sun nuna cewa ana zargin Kwankwaso ya yi yunkurin sa 'yan Majalisar Dokokin Kano su tsige Gwamna Abba bayan samun labarin shirinsa na komawa APC.

Source: Facebook
Abin da ya raba Kwankwaso da Abba
Daily Trust ta ruwaito cewa lissafin Kwankwaso ya rushe ne bayan ya kira zama da mambobin majalisar, wadanda suka fada masa suna tare da Mai girma gwamna.
Wata majiya ta ce:
“Babban matsalar ita ce Kwankwaso ya fara takaici kan yadda Abba ya daina masa makauniyar biyayya kamar yadda yake masa a baya. Ya ga gwamnan ya canza ba kamar a baya ba."
Ɗaya daga cikin majiyoyin ya ce saboda haka ne Kwankwaso ya tsara zabi guda biyu da zai raba Abba da kujerar gwamnan Kano.
“Zaɓi na farko shi ne barin NNPP ta rasa mulki, wanda hakan ya sa babu wani ƙoƙari da Madugu ke yi na warware rikicin cikin gida da ya raba jam’iyyar zuwa gida biyu."
“Zaɓi na biyu kuma, mun fahimci ya yi yunkurin fara aiwatar da shi, shi ne a tsige gwamnan tare da maye gurbinsa da mataimakinsa, Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo,” in ji shi.

Kara karanta wannan
Kano ta dauki zafi, Kwankwaso ya fito ya yi magana kan komawa APC tare da Gwamna Abba
Yadda Kwankwaso ya so tsige Gwamna Abba
A cewar majiyar, Kwankwaso ya tsara sauke Abba daga mulkin Kano ta hanyoyi biyu, wadda hanya ta farko ita ce hana gwamnan tikitin neman wa'adi na biyu a zaben 2027.
Majiyar ta ce:
“Hanya ta biyu kuma ita ce idan Abba ya fice daga NNPP, Kwankwaso zai yi amfani da Majalisar Dokoki, inda ya yi imanin yana da goyon bayan mambobi 27, adadin da kundin tsarin mulki ke buƙata domin tsige gwamna."

Source: Twitter
'Yan Majalisa sun rusa lissafin Kwankwaso
Bayanai sun nuna cewa lissafin Kwankwaso ya rushe ne lokacin da ya kira 'yan Majalisa domin su fara shirin tsige Abba, amma sai suka fada masa suna tare da mai girma gwamna.
Kwankwaso ya gayyaci mambobi 27 na Majalisar Dokokin Jiha zuwa wani taro, kuma ’yan majalisa 20 ne suka halarta, ciki har da kakakin majalisa, mataimakinsa da shugaban masu rinjaye.
“Duka yan majalisa 20 sun shaida masa cewa suna tare da gwamna kuma suna shirin bin sa zuwa APC,” in ji majiyar.

Kara karanta wannan
Rigima ta kara zafi a Kano, Kwankwaso ya fara duba yiwuwar ficewa daga jam'iyyar NNPP
Kwankwaso ya yi fatali da kiran komawa APC
A wani rahoton, kun ji cewa jagoran NNPP, Rabiu Kwankwaso ya yi fatali da kiraye-kirayen ya jagoranci mabiyarsa zuwa jam'iyyar APC.
Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya tabbatar da cewa ba ya cikin tawagar da za ta koma jam'iyyar APC tare da Gwamna Abba Kabir Yusuf.
Kwankwaso ya kuma bukaci duka mabiyansa da masu masa fatan alheri da su kwantar da hankulansu, kuma su ci gaba da hada kansu.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
