Kano Ta Dauki Zafi, Kwankwaso Ya Fito Ya Yi Magana kan Komawa APC tare da Gwamna Abba
- Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya tabbatar da cewa ba ya cikin tawagar da za ta koma jam'iyyar AapC tare da Gwamna Abba Kabir Yusuf
- Jagoran NNPP na kasa ya bukaci magoya bayansa da ka da su tayar da hankulansu kan abubuwan da ke faruwa a jihar Kano
- Tsohon gwamnan ya fadi haka ne a cikin wata sanarwa da aka fitar jim kadan bayan ganawarsa da masu ruwa da tsaki na Kwankwasiyya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kano, Nigeria - Jagoran jam'iyyar NNPP na kasa kuma tsohon gwamnan Kano, Dr. Rabiu Musa Kwankwaso ya bayyana matsayarsa kan shirin Gwamna Abba Kabir Yusuf na komawa APC.
Rahotanni sun tabbatar da cewa gwamnan Kano ya gama duk wani shiri na ficewa daga tafiyar Kwankwasiyya a NNPP, tare da komawa APC mai mulkin Najeriya.

Source: Facebook
A wani rahoto da BBC Hausa ta tattaro yau Asabar, 3 ga watan Janairu 2026, Kwankwaso ya tabbatar da cewa ba zai bi Gwamna Abba zuwa jam'iyyar APC.
Kwankwaso zai koma APC tare da Abba?
Madugun Kwankwasiyyar ya kuma tsame kansa daga duk wani shiri da Abba ke yi tare da mukarrabansa, tare da tabbatar da cewa yana nan daram a NNPP a halin da ake ciki.
Tsohon gwamnan jihar Kano ya bayyana wannan matasaya ne jim kadan bayan ganawa da masu ruwa da tsaki na Kwankwasiyya jiya Jumma'a, 2 ga Janairu, 2025 a Kano.
Taron ya samu halartar manyan kusoshi da masu fada a ji na tafiyar Kwankwasiyya daga kananan hukumomi 44 da ke fadin jihar Kano.
Sanata Kwankwaso ya shirya barin NNPP?
Da yake bayyana matsayarsa a taron, Kwankwaso ya nesanta kansa daga bin tawagar gwamnan Kano zuwa jam'iyyar APC.

Kara karanta wannan
Tirkashi: Kwankwaso ya bi hanyoyi 2, ya yi yunkurin tsige Abba daga kujerar gwamnan Kano
Wata sanarwar da aka fitar bayan taron, ta ce Kwankwaso zai ci gaba da zama a jam'iyyar NNPP, yana mai cewa zai sanar da matakinsa na gaba a lokacin da ya dace.
Jagoran Kwankwasiyya ya kuma musanta duk wata jita-jita da ake yadawa kan sauya shekarsa zuwa wata jam'iyya, tare da kira ga mabiyansa da su yi watsi da rade-radin.

Source: Facebook
Sakon Kwankwaso zuwa ga mabiyansa
Kwankwaso ya kuma bukaci duka mabiyansa da masu masa fatan alheri da su kwantar da hankulansu, kuma su ci gaba da hada kansu a halin da ake ciki yanzu.
Wannan kalamai na Kwankwaso na zuwa ne a daidai lokacin da dakon sanarwar sauya sheka daga Gwamma Abba, wanda rahotanni suka tabbatar da zai koma APC, in ji rahoton This Day.
Kwankwaso ya fara tattaunawa da ADC
A baya, an ji cewa wasu rahotanni sun yi ikirarin cewa jagoran NNPP na kasa, Rabiu Musa Kwankwaso ya fara duba yiwuwar sauya sheka zuwa jam'iyyar ADC.
An ce Kwankwaso na nazarin yiwuwar haɗa kai da tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, da kuma ɗan takarar shugaban ƙasa a 2023, Peter Obi a ADC.
Idan tattaunawar da ake yi tsakanin Atiku, Obi da Kwankwaso ta yi nasara, hakan na iya sauya fasalin siyasar adawa tare da canza lissafin siyasar ƙasar baki ɗaya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
