Rigima Ta Kara Zafi a Kano, Kwankwaso Ya Fara Duba Yiwuwar Ficewa daga Jam'iyyar NNPP
- Wasu rahotanni sun yi ikirarin cewa jagoran NNPP na kasa, Rabiu Musa Kwankwaso ya fara duba yiwuwar sauya sheka zuwa ADC
- Ana ganin hadewar Sanata Kwankwaso, Atiku Abubakar da Peter Obi na iya farfado da tsagin adawa gabanin zaben 2027
- Wannan na zuwa ne bayan Gwamna Abba Kabir Yusuf da 'yan Majalisar dokokin Kano sun yanke shawarar komawa APC
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kano, Nigeria - Yayin da shirye-shiryen zaɓen 2027 ke ƙara ɗaukar zafi, jagoran NNPP na kasa kuma tsohon gwamnan Kano, Dr. Rabiu Musa Kwankwaso ya fara duba yiwuwar sauya jam'iyya.
Wannan dai na zuwa ne bayan wasu rahotanni sun yi ikirarin cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf da kusan duka 'yan Majalisar dokokin jihar Kano sun yanke shawarar komawa APC.

Source: Facebook
A wani rahoton da This Day ta wallafa, an fara yada jita-jitar cewa Kwankwaso ya fara nazari tare da duba yiwuwar sauya sheka daga NNPP zuwa jam'iyyar hadaka watau ADC.
Kwankwaso na duba yiwuwar barin NNPP
An ce Kwankwaso na nazarin yiwuwar haɗa kai da tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, da kuma ɗan takarar shugaban ƙasa a 2023, Peter Obi, a ƙarƙashin inuwar ADC.
Duk da cewa ginshikan tsarin siyasar Madugu sun nuna alamun bin Abba zuwa APC, majiyoyi sun gano cewa Kwankwaso na tattaunawa da ADC kan shiga hadaka tare da 'yan Kwankwasiyya, waɗanda suke amintattun magoya bayansa.
Majiyoyi sun shaida wa Arise News cewa ana ci gaba da tattaunawa a boye, yayin da ’yan siyasar ke duba yiwuwar kafa gagarumar hadakar 'yan adawa gabanin zaɓen 2027.
Haka kuma, alamu masu ƙarfi sun nuna cewa Gwamnan Jihar Kano, Abba Yusuf, wanda shi kaɗai ne ke rike da jiha a ƙarƙashin NNPP, na shirin komawa APC a ranar Litinin.
An rawaito cewa Kwankwaso ya nuna adawa da shirin ficewar Gwamna Abba zuwa APC, lamarin da ya haifar da rikici mai tsanani a cikin darikar Kwankwasiyya.

Kara karanta wannan
Tirkashi: Kwankwaso ya bi hanyoyi 2, ya yi yunkurin tsige Abba daga kujerar gwamnan Kano
Kwankwaso zai iya karawa hadaka karfi
Idan tattaunawar da ake yi tsakanin Atiku, Obi da Kwankwaso ta yi nasara, hakan na iya sauya fasalin siyasar adawa ƙwarai tare da canza lissafin siyasar ƙasar baki ɗaya.
Atiku, Obi da Kwankwaso su ne 'yan takarar da suka zo na biyu, na uku da na huɗu a zaɓen shugaban ƙasa na 2023.

Source: Facebook
Sai dai duk da cewa APC mai mulki na nuna kwarin guiwa saboda ta kama jihohi akalla 28 a halin yanzu, adawa na ci gaba da gina kanta a hankali, tare da fatan cewa fushin jama'a kan halin da ake ciki na iya kawo sauyi a zaben 2027.
Wani mamban ADC a karamar hukumar Danja ta Katsina, Kabir Abdullahi ya shaidawa Legit Hausa cewa idan Kwankwaso ya amince ya hade da Atiku da Obi, to APC ba za ta kai labari ba.
Matashin dan siyasar ya yi ikirarin cewa da yiwuwar a maimaita abin da ya faru a zaben 2015, inda yan adawa da za su kara kifar da gwamnati mai ci.

Kara karanta wannan
Kwankwaso ya tara 'yan Kwankwasiyya a;hali Abba na shirin hada kai da Ganduje a APC
"Shigowar Kwankwaso ADC zai canza lissafin siyasar Najeriya. Ina da yakinin ba yadda Tinubu zai yi da wadannan jiga-jigan uku, sai dai a yi magudi amma matukar aka yi zabe, sai APC ta kwashi kashimta a hannu," in ji shi.
Kwankwaso ya amince Abba ya koma APC?
A wani rahoton, kun ji cewa jagoran NNPP na kasa, Dr. Rabiu Musa Kwankwaso bai amince Gwamna Abba Kabir Yusuf da mukarrabansa su sauya sheka zuwa APC ba.
'Daya daga cikin jagororin Kwankwasiyya a karamar hukumar Dala ta jihar Kano, Kabiru Adamu Kofar Ruwa ne ya tabbatar da hakan a wata hira da aka yi da shi.
Ya gargadi 'yan majalisar dokokin jihar Kano da na tarayya, kwamishinoni da ciyamomin kananan hukumomi da ke shirin bin Abba Gida-Gida.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
