PDP Ta Kausasa Harshe kan Ficewar Gwamma Mutfwang zuwa Jam'iyyar APC
- Jam'iyyar PDP reshen jihar Plateau ta nuna rashin jin dadinta bayan sauya shekar Gwamna Caleb Mutfwang zuwa APC mai-ci
- Sakataren yada labarai na PDP a Plateau, Hon. Choji Dalyop, ya bayyana cewa gwamnan bai tuntube su ba kafin ya sauya sheka
- Ya yi kira ga mutanen jihar Plateau da ka da su sake ba gwamnan kuri'unsu domin ya ci amanar yardar da suka yi masa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Plateau - Jam’iyyar PDP reshen jihar Plateau ta nuna rashin gamsuwarta kan sauya shekar Gwamna Caleb Mutfwang zuwa APC mai-ci a kasa.
PDP ta ce ta ɗauki ficewar Gwamna Caleb Mutfwang daga jam’iyyar a matsayin cin amana da kuma yaudarar al’ummar da suka yarda da shi duk da kalubalen da ya fuskanta.

Source: Facebook
Jaridar Leadership ta ce sakataren yaɗa labarai na jam’iyyar a jihar, Hon. Choji Dalyop, ne ya bayyana hakan yayin da yake ganawa da manema labarai a Jos, babban birnin jihar Plateau, a daren Juma’a, 2 ga watan Janairun 2026.
PDP ta caccaki Gwamna Caleb Mutfwang
A cewarsa, Gwamna Mutfwang ya zaɓi fifita burinsa na kashin kansa a kan muradun al’ummar Plateau, yana mai jaddada cewa jam’iyyar ba za ta ɗauki lamarin da wasa ba.
"PDP na sanar da kowa a bayyane cewa ko kaɗan gwamnan bai tuntubi jam’iyyar ba dangane da wannan batu, sabanin abin da ake yaɗawa a wasu wurare.”
- Hon. Choji Dalyop
Dalyop ya kara da cewa babu wani dalili mai karfi a kundin tsarin mulki da zai halasta wannan mataki da gwamnan ya ɗauka na barin PDP da komawa jam’iyyar APC, ba tare da sauka daga kujerar gwamna nan take ba.
"Saboda haka, wannan ficewa ana kallonta a matsayin amfani da siyasa don amfanin kashin kai, wanda ya tauye cikakken muradin masu zaɓe, tare da fifita bukatun mutum ɗaya a kan alherin al’ummar Plateau baki ɗaya.”
- Hon. Choji Dalyop
PDP ta ba mutanen Plateau shawara
Kakakin na PDP ya bukaci al’ummar jihar Plateau da su rike Gwamna Mutfwang da alhakin abin da ya aikata, tare da kin amincewa da yunkurinsa na neman sake tsayawa takara a karkashin sabuwar jam’iyyarsa.

Kara karanta wannan
Magana ta kare: Gwamna Mutfwang ya koma APC bayan ficewa daga PDP, ya fadi dalili
Hon. Choji Dalyop ya jaddada cewa jam’iyyar ba za ta bar lamarin ya wuce haka nan ba, rahoton jaridar Thisday ya tabbatar da hakan.
Ya kuma gargadi jam’iyyar APC reshen jihar Plateau da kada ta karɓi gwamnan hannu bibbiyu, yana mai cewa hakan zai sa su zama abokan tarayya a wajen cin amanar jama’a.
Dalyop ya ce PDP na Allah-wadai da matakin gwamnan, wanda ya bayyana a matsayin abin da ya saɓa wa ka’idojin amana, gaskiya da rikon amana da dimokuraɗiyya ta ginu a kansu.

Source: Twitter
Shirin jam'iyyar PDP kan zabubbukan gaba
Ya kuma yi kira ga magoya bayan jam’iyyar da jama’a gaba ɗaya da su kwantar da hankalinsu, su tsaya tsayin daka, kuma su kasance jajirtattu.
"Jam’iyyar PDP na nan daram, a haɗe, kuma tana mai da hankali wajen shiga dukkan zaɓubbukan da ke tafe a kan lokaci."
"Jam’iyyar na ci gaba da jajircewa wajen samar da kyakkyawan shugabanci da amfanin dimokuraɗiyya ga al’umma.”
- Hon. Choji Dalyop
Gwamna Mutfwang ya yi murabus daga PDP
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Plateau, Caleb Mutfwang, ya yi murabus daga jam'iyyar PDP.
Caleb Mutfwang ya sanar da murabus dinsa ne a wasikar da ya aikewa shugaban PDP na unguwar Ampang ta Yamma, a karamar hukumar Mangu.
Wasikar, wadda shugabannin mazabar suka karɓa, ta nuna godiyar gwamnan ga jam’iyyar bisa damar da ta ba shi a tsarin dimokuraɗiyya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

