Kwankwaso Ya Tara 'Yan Kwankwasiyya alhali Abba na Shirin Hada Kai da Ganduje a APC

Kwankwaso Ya Tara 'Yan Kwankwasiyya alhali Abba na Shirin Hada Kai da Ganduje a APC

  • Rabiu Musa Kwankwaso ya jagoranci taron musamman na shugabanni da dattawan jam'iyyar NNPP daga ƙananan hukumomi 44 na Jihar Kano
  • NNPP ta rusa dukkan shugabanninta na jiha, ƙananan hukumomi da mazabu a Kano gabanin sauya sheƙar gwamna Abba Yusuf zuwa APC
  • An ce rikicin siyasa tsakanin Kwankwaso da Abba Kabir ya ƙara tsananta yayin da ake ci gaba da rade-radi kan sauya jam’iyyar gwamnan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Kano – Jagoran jam’iyyar NNPP, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya jagoranci wani taron musamman na majalisar jam’iyyar a Miller Road, Jihar Kano.

Taron ya zo ne a daidai lokacin da ake rade-radin cewa Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, na shirin sauya sheƙa zuwa jam’iyyar APC.

Sanata Rabiu Musa Kwankwaso
Rabiu Kwankwaso yayin zama da 'yan NNPP a Kano. Hoto: Saifullahi Hassan
Source: Facebook

Hadimin Kwankwaso, Saifullahi Hassan ya wallafa a Facebook cewa taron ya gudana ne a ranar Juma’a, 2, Janairu, 2026, bayan sallar Juma’a.

Kara karanta wannan

A karshe, Abba zai rabu da Kwankwaso, Ganduje zai karbe shi zuwa APC

Taron Kwankwaso da 'yan Kwankwasiyya

A cewar bayanai, taron ya haɗa dattawa da masu ruwa da tsaki na NNPP daga kananan hukumomi 44 na jihar, inda aka tattauna halin da jam’iyyar ke ciki da kuma makomar siyasar Kano.

Kwankwaso, wanda shi ne jagoran NNPP na ƙasa kuma tsohon gwamnan Kano, ya yi jawabi ga mahalarta taron, inda ya jaddada muhimmancin tsayawa kan manufofi da ƙa’idojin jam’iyyar.

Taron ya gudana ne a wani yanayi da ke nuna cewa NNPP na fuskantar babbar ƙalubale a Kano, jiha da ake ɗauka a matsayin ginshiƙinta na siyasa.

Kafin taron, Kwankwaso ya fara da gudanar da sallar Juma’a a Masallacin Marigayi Alhaji Musa Saleh da ke Miller Road a Kano.

An rusa shugabancin NNPP a Kano

Kwamitin Zartarwa na Ƙasa na NNPP ya sanar da rushe shugabannin jam’iyyar a matakin jiha, ƙananan hukumomi da mazabu a Jihar Kano.

Sakataren Yaɗa Labarai na Ƙasa na NNPP, Oladipo Johnson, ya bayyana a wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma’a cewa kwamitin ya ɗauki matakin ne bayan taron gaggawa, bisa tanadin kundin tsarin mulkin jam’iyyar.

Kara karanta wannan

Ana rade radin komawa APC, mataimakin gwamnan Kano ya tura sako ga Abba da Kwankwaso

Jaridar Punch ta wallafa cewa Johnson ya ce NNPP na shirin kafa kwamitin rikon ƙwarya domin tafiyar da harkokin jam’iyyar a Kano.

Babu martanin daga bangaren Abba

A halin yanzu, babu wata sanarwa a hukumance daga gwamnatin Jihar Kano dangane da batun sauya sheƙar gwamna Abba Kabir Yusuf.

Sai dai mai magana da yawun Gwamna Abba Kabir Yusuf ya wallafa saƙo a shafinsa na Facebook da ke cewa:

“Rade-radi ko’ina…”,

Saƙon Sanusi Batire Dawakin Tofa ya janyo ce-ce-ku-ce a tsakanin jama’a da ’yan siyasa a Kano, inda mutane ke masa fassara daban-daban.

Ganduje zai karbi Abba zuwa APC

A wani labarin, kun ji cewa wasu bayanai sun nuna cewa Abba Kabir Yusuf na jihar Kano zai sauya sheka zuwa APC a mako mai zuwa.

Wani rahoto ya yi nuni da cewa tsohon shugaban APC, Abdullahi Umar Ganduje na cikin wadanda za su karbi gwamnan daga NNPP.

Ana sa ran cewa shugaban APC na jihar Kano zai dawo daga Umrah domin samun damar yankawa Abba Kabir Yusuf katin jam'iyya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng