A Karshe, Abba zai Rabu da Kwankwaso, Ganduje zai Karbe Shi zuwa APC
- Ana rade-radin cewa Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, zai sanar da ficewarsa daga jam'iyyar NNPP zuwa APC a ranar Litinin bayan kammala shiri a Abuja
- Rahotanni sun nuna manyan jiga-jigan APC ciki har da Mataimakin Shugaban Kasa Kashim Shettima za su karɓi gwamnan domin tabbatar da sauyin siyasar Kano
- Matakin gwamnan ya haifar da rikici a sansanin mabiya tafiyar Kwankwasiyya, inda wasu magoya baya ke nuna biyayya ga Sanata Rabiu Musa Kwankwaso
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, na dab da komawa jam’iyyar APC mai mulki a wani mataki da ke nuna gagarumin sauyi a siyasar Kano da Arewa baki ɗaya.
Rahotanni sun tabbatar da cewa Abba Kabir Yusuf da shi kaɗai ne gwamnan NNPP a ƙasar, ya isa Abuja domin kammala shirye-shiryen ficewarsa.

Kara karanta wannan
Ana rade radin komawa APC, mataimakin gwamnan Kano ya tura sako ga Abba da Kwankwaso

Source: Facebook
Rahoton Daily Nigerian ya bayyana cewa an tsara karɓar gwamnan ne a hukumance a ranar Litinin, 5 ga Janairun 2026 inda manyan shugabannin APC za su hallara.
Ana shirin karɓar Gwamna Abba a APC
Majiyoyi da ke da masaniya kan lamarin sun shaida cewa Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima, tare da Shugaban APC na ƙasa, Yitwalda Nentawe, ne za su jagoranci karɓar Gwamna Abba Yusuf a Abuja.
A Kano kuma, an ruwaito cewa jagoran APC a jihar, Abdullahi Ganduje, an nemi ya dawo daga tafiyar da ya yi zuwa Dubai domin halartar muhimman taruka.
Aminiya ta wallafa cewa an nemi Shugaban APC na Kano, Abdullahi Abbas, ya katse tafiyar Umrah da yake yi domin shirya batun ba gwamnan katin zama mamba a mazabarsa ta Diso da ke Karamar Hukumar Gwale.
Abba zai zauna da Abdullahi Ganduje
Rahotanni sun nuna cewa gwamnan na sa ran yin wata ganawa ta musamman da Abdullahi Ganduje cikin makon, domin tsara sabuwar tafiyar jam’iyyar APC a Kano.
Majiyoyi sun ce Shugaba Bola Ahmed Tinubu da farko bai nuna cikakken amincewa da karɓar gwamnan ba, matuƙar dai ba tare da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ba.

Source: Twitter
Shugaban kasar ya yi imanin cewa Kwankwaso na da tasiri mai ƙarfi a Kano da wasu sassan Arewa. Sai dai bayan ƙoƙarin shawo kan Kwankwaso ya ci tura, Gwamnan Imo, Hope Uzodinma, ya shawo kan Tinubu ya amince da karɓar Abba Yusuf shi kaɗai.
Bashir ya yi maraba da Abba a APC
Hadimin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, Bashir Ahmad, ya tabbatar da cewa Abba Kabir zai koma APC a ranar Litinin a wani sako da ya wallafa a X.
Ya tabbatar da labarin cewa babu wata matsala da za ta hana gwamnan shiga APC. Ya ce wannan sauyi zai ƙara ƙarfafa APC a Kano, tare da haifar da sabon yanayi a siyasar jihar.
Gwamnan Filato ya koma jam'iyyar APC
A wani labarin, kun ji cewa gwamnan jihar Filato, Caleb Mutfwang ya koma jam'iyyar APC mai mulki bayan sanar da ficewa daga PDP.
Gwamna Mutfwang ya bayyana cewa ya koma APC ne domin cigaba da gudanar da ayyukan raya kasa ga 'yan jihar Filato da ya ke mulka.
Sauya shekar gwamnan na zuwa a lokacin da PDP ke rasa gwamnoni, 'yan majalisun jihohi da na tarayya a fadin Najeriya zuwa APC mai mulki.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
