Rikicin Ribas: An Gano Yadda Gwamna Ya Yaudari Jama'a kafin Sauya Sheka zuwa APC

Rikicin Ribas: An Gano Yadda Gwamna Ya Yaudari Jama'a kafin Sauya Sheka zuwa APC

  • Jam'iyyar PDP a jihar Ribas ta soki matakin da Gwamna Siminalayi Fubara ya dauka na sauya sheka zuwa APC mai mulkin Najeriya
  • PDP ta bayyana hakan a matsayin cin amanar al'ummar jihar Ribas, tana mai cewa Gwamna Fubara ya yaudari mutane
  • Ta kuma bukaci mai girma gwamnan ya fito ya gaya wa al'ummar Ribas yarjejeniyar sulhun da ya kulla da Shugaba Bola Tinubu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Rivers, Nigeria - Jam'iyyar PDP reshen jihar Ribas ta yi ikirarin cewa Gwamna Siminalayi Fubara ya ci amanarta da ya sauya sheka zuwa APC.

PDP ta zargi Gwamna Fubara da yaudara da cin amanar al'ummar jihar Ribas sakamakon shiga APC ana tsakiyar rikicin siyasar jihar.

Gwamna Siminalayi Fubara.
Gwamnan jihar Ribas, Sir Siminalayi Fubara Hoto: Sir Siminalayi Fubara
Source: Twitter

Shugaban tsagin PDP na Ribas, Dr. Nname Ewor, ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai da ya gudanar a ranar Alhamis a Fatakwal, kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Ana rade radin komawa APC, mataimakin gwamnan Kano ya tura sako ga Abba da Kwankwaso

Wasu sharuddan yarjejeniyar sulhun Ribas

Ewor ya tuna yadda Shugaban kasa Bola Tinubu ya shiga tsakani tare da samar da masalaha a rikicin siyasar Ribas tsakanin Fubara da yan majalisar dokoki masu goyon bayan Wike.

Ya kara da cewa daya daga cikin sharudan sulhun da aka cimma shi ne cewa Fubara ba zai nemi tsayawa takarar wa’adi na biyu ba.

Ya ce bayan haka kuma, an bukaci Fubara da ya maido da Cif Ohna Awuse a matsayin Shugaban Majalisar Sarakunan Gargajiya ta Jihar Ribas.

Ewor ya ce daga cikin sauran yarjejeniyoyin da aka cimma akwai bukatar gwamnan ya cire Tammy Danagogo daga mukamin Sakataren Gwamnatin Jihar da kuma Edison Ehie daga mukamin Shugaban Ma’aikatan Gwamna.

Ana zargin Gwamna Fubara ya yaudari PDP

Ya zargi Fubara da kin bin dukkan sharudan yarjejeniyar da aka cimma, wanda hakan ya kai ga rushewar sulhun da aka yi da kuma ayyana dokar ta-baci a Ribas.

Kara karanta wannan

Sanatan APC ya sha alwashin korar gwamna daga mulki, zai iya yin komai a 2027

Shugaban PDP ya kara da cewa daga baya Fubara ya lallaba ya sake kulla wata yarjejeniya da Tinubu jim kadan kafin a dage dokar ta-bacin, lamarin da daga bisani ya kai ga ficewarsa daga PDP zuwa APC.

Ya bayyana cewa bayan sanar da ficewarsa daga PDP, Fubara ya fara ikirarin cewa Tinubu zai tilasta wa ‘yan Majalisar Dokokin Jihar su amince da kasafin kudin shekarar 2026.

PDP ta aika sako ga Gwamna Fubara

Ya kuma ce gwamnan ya yi ikirarin cewa Tinubu zai tilasta wa Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT), Nyesom Wike, ya mara masa baya a yunkurinsa na sake tsayawa takarar wa’adi na biyu.

Gwamna Fubara da Wike.
Gwamna Siminalayi Fubara na jihar Ribas da ministan harkokin Abuja, Nyesom Wike Hoto: Sir Siminalayi Fubara
Source: Facebook

Ewor ya bukaci Fubara da ya fito ya fadawa al’ummar Ribas sharudan yarjejeniyar da ya cimma da Tinubu kafin a dage dokar ta-bacin a jihar, in ji Vanguard.

"Ya zama wajibi a wannan lokaci mai muhimmanci ya bayyana wa 'yan Ribas sharudan yarjejeniyar sulhun da ya kulla da Tinubu kafin a dage dokar ta-baci. Hakan zai bai wa al’umma damar yanke shawara bisa fahimta,” in ji shi.

Wike na shirin fallasa yarjejeniyar sulhu

A wani labarin, kun ji cewa Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, ya zargi Gwamna Fubara, da karya yarjejeniyar da Bola Tinubu ya shimfida a tsakaninsu.

Kara karanta wannan

Wike ya yi barazanar bude asiri kan sulhunsa da Fubara da Tinubu ya umarta

Wike ya bayyana cewa ba da jimawa ba zai fito ya bayyana wa al’ummar Ribas cikakkun bayanan yarjejeniyar da aka cimma a gaban shugaban kasa.

An cimma yarjejeniyar ne bayan wani taro na sirri da Shugaba Tinubu ya kira a Fadar Shugaban kasa da ke Abuja a watan Yunin 2025.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262