Sanatoci 3 da 'Dan Majalisar Wakilai Sun Bi Atiku da Peter Obi, Sun Sauya Sheka zuwa ADC
- Jam'iyyar ADC ta kara samun mambobi a Majalisar Tarayya ta 10 bayan Sanata Enyinnaya Abaribe ya fice daga jam'iyyar APGA
- Abaribe tare da wasu sanatoci biyu daga jihar Anambra sun bi sahun tsohon dan takarar shugaban kasa, Peter Obi zuwa ADC
- ADC ta kasance jam'iyyar adawa da manyan jagororin jam'iyyun hamayya suka zabi yin hadin gwiwa a cikinta domin kifar da Bola Tinubu da APC a 2027
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Enugu, Nigeria - Jam'iyyar hadakar 'yan adawa, ADC ta fara samun manyan jagororin siyasa masu rike da kujerun shugabanci a Najeriya.
Sanata Enyinnaya Harcourt Abaribe, wanda ke wakiltar mazabar jihar Abia ta Kudu a Majalisar Dattawa ta 10, ya sauya sheka daga jam'iyyar APGA zuwa ADC.

Source: Twitter
Sanatoci 3 da dan Majalisa sun koma ADC
Tashar TVC News ta tattaro cewa Sanata Abaribe ya tabbatar da ficewa daga APGA zuwa ADC a hukumance yau Laraba, 31 ga watan Disambar 2025.
Haka zalika sanata mai wakiltar Anambra ta Tsakiya, Victor Umeh ta takwaransa na mazabar Anambra ta Arewa, Tony Nwoye, sun bi sahun Abaribe zuwa jam'iyyar ADC.
'Dan majalisa mai wakiltar mazabar tarayya ta Ogbaru a majalisar wakilai, Hon. Afam Ogene, ya bi sahu zuwa ADC.
Sauran wadanda suka sauya shekar sun hada da tsohon gwamnan jihar Imo, Achike Udenwa, da wasu manyan 'yan siyasa a yankin Kudu maso Gabas.
Peter Obi ya ja zuga zuwa jam'iyyar ADC
Wadannan manyan jiga-jigai sun tabbatar da komawa ADC ne a taron da tsohon dan takarar shugaban kasa, Peter Obi ya sanar da ficewarsa daga LP zuwa jam'iyyar hadaka.
Idan za ku iya tunawa, manyan jagororin adawar kasar nan sun amince su rungumi ADC a matsayin dandalin da za su kalubalanci Shugaba Bola Tinubu da APC a zaben 2025.
Peter Obi da tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar na cikin wadanda ke jagorantar hadakar 'yan adawar Najeriya.
Sauran wadanda ke sahun gaba a hadakar sun hada da tsohon gwamnan Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, tsohon shugaban majalisar dattawa, David Mark, tsohon ministan cikin gida, Rauf Aregbesola da sauran jiga-jigai.

Kara karanta wannan
Kalu: Mataimakin shugaban majalisa ya fara zawarcin gwamna 1 na jam'iyyar LP zuwa APC
Jam'iyyar ADC ta fara shirya wa zaben 2027
A makonnin da suka shige, Atiku Abubakar ya bar PDP tare da komawa ADC, kuma ya garzaya mahaifarsa ya yanki katin zama cikakken mamba a jihar Adamawa.
A halin yanzu, Peter Obi, wanda ake ganin yana da dumbin magoya baya a Kudancin Najeriya ya sauya sheka zuwa ADC domin fara shirye-shiryen 2027, kamar yadda The Nation ta kawo.

Source: Facebook
Obi tare da Sanata Abaribe da wasu 'yan majalisa, tsofaffin gwamnoni da manyan jiga-jigai a Kudu maso Gabashin Najeriya sun tabbatar da shiga ADC a wani taro da aka shirya a jihar Enugu.
Peter Obi ya cika baki kan mulkin Najeriya
A wani rahoton, kun ji cewa Peter Obi ya bayyana cewa ya cancanta kuma ya shirya tunkarar kowane irin kalubale da ya addabi Najeriya idan ya zama shugaban kasa.
Peter Obi ya ce babu wani daga cikin wadanda ke shirin tsayawa takarar shugaban kasa a zaben 2027 da ya taba rainon kasuwanci tun daga tushe har ta girma kuma ta bunkasa.
Tsohon dan takarar LP ya kuma musanta rade-radin cewa ya amince zai nemi takarar mataimkin shugaban kasa a ADC, yana mai kira magoya bayansa su yi watsi da labarin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
