Babban 'Dan APC, Garba Kore Ya Hango wa Abba Alheri a Rabuwa da Kwankwaso
- Jigon APC, Garba Kore, ya ce Gwamna Abba Kabir Yusuf na tafiya a kan hanya madaidaiciya a yunkurinsa na sauya sheka zuwa APC
- Ya bayyana cewa alakar siyasar Abba da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ba ta da wani alheri da ya rage da gwamnan Kano zai iya mora
- Garba Kore ya yi ikirarin cewa sauya sheƙar da ake hasashen Gwamnan Kano zai yi zai amfani jihar Kano, sannan jagorori za su numfasa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Jigo a jam’iyya mai mulkin Najeriya, APC, Garba Kore, ya bayyana cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf na kan turba ta gaskiya wajen tafiyar da harkokin siyasa da mulki a Kano.
Ya ce abubuwan da ke faruwa a yanzu sun nuna cewa Gwamnan na daukar matakai ne da za su amfani al’ummar jihar Kano baki ɗaya.

Source: Facebook
A wani sashe na hirar da Garba Kore ya yi da Dan Uwa Rano TV, wacce aka wallafa a shafin Facebook, jigon APC ya ce sauya sheƙar da ake sa ran Gwamna Abba zai yi taimako ne kai tsaye ga Kano.
Garba Kore na murnar rabuwar Abba da Kwankwaso
Garba Kore ya bayyana cewa babu wani abin alheri da ya rage a zaman siyasar Abba Kabir Yusuf da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.
Ya ce don haka ya dace a mara wa Gwamnan Kano baya domin ya ci gaba da abin da yake yi. A cewarsa, ci gaban Kano ya fi kowace alaka ta siyasa.
Garba Kore na ganin cewa a wannan lokaci babu wani alheri da ya rage da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso zai iya taimaka wa Gwamna Abba Kabir Yusuf da shi.

Source: Twitter
Ya bayyana cewa:
“Mutum yana son ya yi abin da ya kamata, ya taimaki Kano, ana son a hana shi.”
“Ni abin da nake gaya wa Abba da mutanen Abba shi ne: ku dogara ga Allah, abin da za ku yi mai kyau ne. Ko ba komai yanzu ciyamominku da ’yan majalisunku sun samu nutsuwa. Ko ba komai yanzu kai Abba ka samu nutsuwa.”
Garba Kore ya kara da cewa akwai abubuwan da Abba Kabir Yusuf ya rasa a tafiyar Kwankwasiyya, amma idan ya koma APC zai samu su.
Ya ce Kwankwaso ba zai iya yi masa wani abu ba, yana mai tambaya:
“A wace jam’iyya za su yi takara?” Sannan ya jaddada cewa “Kowane sarki zamaninsa sarki ne.”
Garba Kore ya ce za a iya daure Kwankwaso
A wani bangare na jawabin nasa, Garba Kore ya yi ikirarin cewa idan aka binciki Sanata Rabiu Musa Kwankwaso yadda ya kamata, zai iya fuskantar dauri.
Ya ce:
“Shi yanzu Kwankwaso, in ban da an kyale shi, in ban da Tinubu na sonsa, sai ka wayi gari yana kurkuku.”
Ya ci gaba da cewa:
“Ba kyale mutane ake yi ba? Shi ba mai laifi ba ne Kwankwaso? An gaya maka gaskiya ce da shi?”
Garba Kore ya ce shi shaida ne cewa Kwankwaso ba Annabi ba ne, kuma idan aka yi bincike a kansa, dole ne a dauki mataki.
Ya kara da cewa:
“A yau idan za a binciki Kwankwaso, komai da komai nasa, wallahi sai ya je kurkuku, yana da laifi.”
Hadimin Gwamna na so Abba ya koma APC
A baya, mun wallafa cewa Darakta mai kula da harkokin gidan gwamnatin Kano, Abdullahi Ibrahim Rogo, ya buƙaci Gwamna Abba Kabir Yusuf da Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso da su jagorance su zuwa APC.
Rogo ya bayyana hakan ne a yayin wani taron ƴan jam’iyya, inda ya jaddada cewa har yanzu suna tare da Kwankwaso da Gwamna Abba Kabir Yusuf a matsayin jagorori, amma APC ce mafita.
bdullahi Ibrahim Rogo ya bayyana cewa ƴan Kwankwasiyya sun miƙa wannan buƙata ne bisa ganin cewa jam’iyyar APC ce mafitar siyasarsu a wannan lokaci, kuma Kano za ta amfana.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


