Zulum Ya Nemi Gafarar ’Yan Borno, Ya Ja Kunnen Masu Neman Kujerarsa

Zulum Ya Nemi Gafarar ’Yan Borno, Ya Ja Kunnen Masu Neman Kujerarsa

  • Gwamna Babagana Umara Zulum na jihar Borno ya roƙi al’ummar jihar su yafe masa duk wanda ya ɓata masa rai
  • Farfesa Babagana Zulum ya ce duk da roƙon yafiya, zai ci gaba da taka wasu mutane yayin shirye-shiryen zaɓen 2027
  • Ya yi alƙawarin barin kuɗi a baitul-mali da kuma biyan dukkan basukan giratuti na ma’aikatan da suka yi ritaya kafin 2027

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Maiduguri, Borno - Gwamnan Borno, Babagana Umara Zulum, ya yi kira ga al’ummar jihar da su yafe masa.

Zulum ya yi kiran ne musamman wadanda ya taɓa cutar da su ko ya take su da gangan ko a rashin sani a tsawon shekaru bakwai da ya shafe yana mulki.

Zulum ya nemi gafarar 'yan Borno
Gwamna Babagana Umara Zulum na jihar Borno. Hoto: Prof. Babagana Umara Zulum.
Source: Twitter

Zulum ya roki yafiya daga al'ummar Borno

Zulum ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi a zauren Majalisar Dokokin Jihar Borno bayan gabatar da kasafin kuɗin shekarar 2026, cewar Vanguard.

Kara karanta wannan

Shiga APC: Kwankwaso ya gargadi masu shirin masa butulci a bidiyo

Sai dai gwamnan ya bayyana cewa, duk da roƙon yafiyar da ya yi, zai ci gaba da taka wasu musamman yayin da wa’adin mulkinsa na biyu ke gab da ƙarewa a 2027.

Ya ce:

“Ina so in yi amfani da wannan dama in gode muku bisa goyon baya da haɗin kai, Amma mafi muhimmanci, ina roƙon al’ummar Borno su yafe mini duk wanda na taɓa takawa a cikin mulkina a shekaru bakwai da suka gabata.”

Gwamnan ya ce ɗaya daga cikin burikansa shi ne ya bar mulki cikin mutunci tare da tabbatar da cewa ya bar isassun kuɗi a baitul-malin jihar.

Ya ce zai yi haka ne domin magajinsa ya samu damar fara aiki cikin sauƙi, ya kuma gina kan nasarorin da gwamnatinsa ta cimma.

Amma ya dage cewa duk wanda zai zama magaji dole ne ya kasance da kyawawan halayen shugabanci da cancanta, domin ci gaba daga inda shi ya tsaya.

Zulum ya sha alwashin kyautatawa yan fansho
Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum. Hoto: Prof. Babagana Umara Zulum.
Source: Twitter

Alkawarin Gwamna Zulum ga tsofaffin ma’aikata

Dangane da bashin giratuti na tsofaffin ma’aikatan gwamnati da suka yi ritaya, wanda ya kai biliyoyin Naira, Zulum ya kwantar da hankulan jama'a.

Kara karanta wannan

Malami: Kotu ta iza ƙeyar surukin Buhari da ɗansa zuwa gidan yarin Kuje

Gwamna Zulum ya ba da tabbacin cewa zai yi duk mai yiwuwa cikin gaskiya da adalci, domin tabbatar da cewa an warware dukkan batutuwan biyan haƙƙoƙin ma’aikata.

Zulum ya ƙara da cewa kafin zaɓen 2027, zai ci gaba da ɗaukar matakai masu tsauri, musamman kan masu son gadon kujerarsa.

Amma ya jaddada cewa burinsa shi ne ganin Borno ta samu shugaba nagari da zai ci gaba da tafiyar da jihar yadda ya kamata, cewar Daily Post.

Kirsimeti: Zulum ya kyautata wa Kiristocin Borno

An ji cewa al'ummar Kiristoci sun gudanar da bukukuwan Kirsimeti na shekarar 2025 wadda ta zo karshe.

Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya ba da kayan tallafi ga zawarawa da marasa galihu cikin al'ummar Kiristoci.

Hakazalika ya kuma amince da tsarin kai Kiristoci wadanda ba 'yan asalin jihar Borno ba zuwa garuruwansu kyauta a mota.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.