Shiga APC: Yadda Kwankwaso Ya Gargadi Masu Shirin Masa Butulci a Bidiyo
- A kwanakin baya, Rabiu Musa Kwankwaso ya yi gargaɗi ga mambobin NNPP kan abin da ya kira cin amana a siyasa, yana cewa ba lallai su yi nasara ba
- Jagoran Kwankwasiyya ya yi wannan jawabi ne a Kano a wani taro, a daidai lokacin da ya ji labarin rade-radin sauya sheƙa a tsakanin wasu mambobin tafiyar
- A yanzu haka, wasu 'yan Kwankwasiyya sun bayyana ra’ayin komawa APC, lamarin da ya haifar da martani kai tsaye daga 'yan siyasa a Kano da fadin Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kano – Wani tsohon bidiyo ya nuna tsohon gwamnan jihar Kano kuma jagoran jam’iyyar NNPP na ƙasa, Rabiu Musa Kwankwaso, yana gargadi ga magoya bayansa da mambobin jam’iyyar kan abin da ya kira butulci.
Kwankwaso ya yi wannan gargadi ne yayin da yake jawabi ga dimbin magoya bayansa a Kano, a lokacin da ake ci gaba da samun rade-radin cewa wasu mambobin jam’iyyar na shirin sauya sheƙa.

Source: Twitter
Legit Hausa ta tattaro bayanan da Rabiu Kwankwaso ya yi ne a wani bidiyo da hadiminsa, Saifullahi Hassan ya wallafa a shafinsa na X.
Gargadin Kwankwaso ga masu butulci
Kwankwaso ya ce jama'ar da ya gani a wajen taron ya wuce tsammaninsa, yana mai cewa yawancin magoya bayan tafiyar na nan daram a kan tafiyar da aka gina tun shekaru da dama.
Ya ce:
“Na sani cewa kaɗan daga cikinku sun yanke shawarar tsallakawa zuwa wani ɓangare. Duk wanda ya san su, ya ba su shawara.”
Jagoran NNPP ya jaddada cewa babu wani mutum da ya taɓa samun nasara ta hakika ta hanyar cin amana ko butulci, yana mai kira ga magoya baya da su duba tarihi tun daga shekarar 1999 zuwa yau.
Ya ce duk waɗanda suka bar tafiyar Kwankwasiyya a baya ba su kai ga inda suka nufa ba, ko da kuwa sun yi kama da suna samun nasara na ɗan lokaci.
Rahoton The Cable ya nuna cewa Kwankwaso ya ce wasu sun nuna alamun cewa sun ci nasara a tsawon shekaru, amma daga bisani sun faɗi ƙasa warwas.
Kwankwaso ya bukaci a hada kai
Kwankwaso ya yi kira ga magoya bayansa da su koyi darasi daga abubuwan da suka faru a baya, yana mai cewa koyon darasi daga kuskuren wasu ya fi sauki fiye da mutum ya koyi darasi daga kuskurensa.

Source: Facebook
Ya bukaci mambobin tafiyar da su zauna lafiya kamar 'yan uwan juna, su goyi bayan juna tare da kare akidar Kwankwasiyya, yana mai jaddada cewa haɗin kai ne kaɗai zai tabbatar da dorewar tafiyar a siyasar Kano da ma Najeriya baki ɗaya.
Abba Kabir Yusuf ya gana da 'yan APC
A wani labarin, mun kawo muku cewa gwamna Abba Kabir Yusuf ya gana da wasu 'yan jam'iyyar APC yayin da ake maganar sauya shekarsa.
'Dan majalisar wakilai, Hon. Kabiru Alhassan Rurum da ya koma APC daga NNPP ya tabbatar da tattaunawar da suka yi da gwamnan.
A bayanin da ya yi, Hon. Rurum ya bayyana cewa sun tattauna batun sauya shekar Abba Kabir ba tare da magana kan Rabiu Kwankwaso ba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

