Shugabar Ciyamomin Kano Ta Fadi Dalilin Kiran Abba, Kwankwaso Su Shiga APC

Shugabar Ciyamomin Kano Ta Fadi Dalilin Kiran Abba, Kwankwaso Su Shiga APC

  • Shugabannin siyasa a jihar Kano na ci gaba da bayyana mabambantan ra’ayoyi kan yuwuwar komawa APC mai mulki daga jam'iyyar NNPP
  • Shugabar Karamar Hukumar Tudun Wada, Hajiya Sa’adatu Salisu Soja Maijma'a ta bayyana dalilin da ya sa suke kira ga jagororinsu su shiga APC
  • Hakan na zuwa ne yayin da wasu manyan ’yan siyasa suka dage kan cewa za su ci gaba da zama a NNPP tare da Rabiu Musa Kwankwaso

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano – Rade-radin sauya sheƙar siyasa daga jam’iyyar NNPP zuwa APC na ci gaba da ɗaukar sabon salo a Jihar Kano, inda shugabanni da ’yan siyasa ke fito wa fili suna bayyana matsayinsu.

A halin da ake ciki, wasu shugabannin kananan hukumomi na nuna ra’ayin cewa sauya sheƙa zai iya buɗe ƙofofin cigaba, yayin da wasu ke ganin hakan barazana ce ga tafiyar Kwankwasiyya da amincin jama’ar da suka ba su ƙuri’a.

Kara karanta wannan

Shiga APC: Ciyaman ya rabu da 'yunkurin' Abba a Kano, ya tafi gidan Kwankwaso

Sa'adatu Salisu ALGON Kano
Shugabar karamar hukumar Tundunwada a Kano. Hoto: Sa’adatu Salisu Abdullahi
Source: Facebook

Dalilin neman shiga APC daga NNPP

Zababbiyar shugabar karamar hukumar Tudun Wada kuma shugabar shugabannin kananan hukumomi na Jihar Kano, Hajiya Sa’adatu Salisu Soja Maijama'a ta fadi dalilin neman sauya shekar a shafinta na Facebook.

Shugabar karamar hukumar ta bayyana cewa goyon bayan komawa jam’iyyar APC ya samo asali ne daga burin taimakon talakawa da kawo cigaba.

A cewarta, a matsayinta na shugabar ALGON a Kano, tana ganin cewa shiga APC zai bai wa shugabannin kananan hukumomi damar aiki tare da gwamnatin tarayya domin samar da ayyuka da inganta rayuwar al’umma.

Hajiya Sa’adatu ta yi kira ga Rabiu Musa Kwankwaso da kuma Gwamna Abba Kabir Yusuf da su shiga jam’iyyar APC domin, a cewarta, hakan zai amfani talakawa.

Sai dai ba kowa ne ke goyon bayan wannan ra’ayi ba, wasu ’yan siyasa irin su Sanata Rufa’i Sani Hanga da shugaban karamar hukumar Tsanyawa, Hon Abdullahi Ishaq, sun nuna cewa sun fi son zama a NNPP.

Kara karanta wannan

Yadda Abba ya lashi takobin shiga APC ko zai wargaje da Kwankwaso

Sanata Rufa'i Hanga da Rabiu Kwankwaso
Sanata Rufa'i Sani Hanga tare da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso. Hoto: Saifullahi Hassan
Source: Facebook

Kwankwaso da Abba sun fara samun sabani

Majiyoyi sun bayyana cewa alamun rashin jituwa tsakanin Kwankwaso da Abba Kabir Yusuf sun fara ne tun kafin bayyanar batun sauya sheƙa zuwa APC.

Rahoton Daily Trust ya nuna cewa cewa Kwankwaso ya taba nuna sha’awar kulla kawance da jam’iyyar APC domin samun wani matsayi a gwamnatin tarayya, tun kafin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya hau mulki.

Bayan rushewar wannan shiri, rahotanni sun ce shugabannin APC sun karkata hankalinsu zuwa ga gwamna Abba Kabir Yusuf ta hanyar dandalin gwamnonin jam’iyyar, matakin da ake cewa ya fusata Kwankwaso.

Majiyar ta ce Kwankwaso ya ji an wulakanta shi ne ganin yadda aka ci gaba da tattaunawa ba tare da shi ba, inda yake son duk wata yarjejeniya ta rika bi ta hannunsa a matsayinsa na jagora.

NNPP ta bukaci Abba kar ya shiga APC

A wani labarin, mun kawo muku cewa shugaban jam'iyyar NNPP na jihar Kano, Hashimu Dungurawa ya yi kira ga mutanensu masu son sauya sheka.

Kara karanta wannan

Bayan shirin sauya sheƙar Abba ya hargitsa Kano, NNPP ta kori shugaban jam'iyya

Dungurawa ya bayyana cewa suna kira ga Abba Kabir Yusuf da ya fasa shiga jam'iyyar APC, ya zauna su cigaba da aiki tare.

A bayanin da ya yi, ya karyata cewa wasu daga cikin 'yan NNPP kamar shi da Sanata Hanga, mataimakin gwamna na son raba Abba da Kwankwaso.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng