Kwamanda Ya Faɗi yadda Kwankwaso da Abba Suka Kitsa Sauya Sheƙar Gwamna zuwa APC

Kwamanda Ya Faɗi yadda Kwankwaso da Abba Suka Kitsa Sauya Sheƙar Gwamna zuwa APC

  • Jigo a APC, AbdulMajeed Ɗan Bilki da ya ce babu saɓani tsakanin Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf da Rabi’u Musa Kwankwaso
  • Dan Bilki Kwamandan ya bayyana zargin cewa sauya sheƙa a matsayin dabarar siyasar Kwankwasiyya wanda Kwankwaso ya buga a Kano
  • Jigon APC ya ce shigowar Abba APC ba matsala ba ce ga jam’iyya, sai dai shiri ne na Abdullahi Umar Ganduje kan cimma manufarsa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano –Alhaji Abdulmajeed Ɗanbilki Kwamanda, Shugaban Ƙungiyar Arewa 'Media Group' kuma jigo a APC, ya ce babu wani saɓani da ya ɓarke tsakanin Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf da Rabi’u Musa Kwankwaso.

Dan Bilki ya bayyana haka ne a daidai lokacin da shugabannin ƙananan hukumomi ke neman Gwamna Abba Kabir Yusuf da Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso su koma jam’iyyar APC.

Kara karanta wannan

Yadda Abba ya lashi takobin shiga APC ko zai wargaje da Kwankwaso

Dan Bilki Kwamanda ya ce shiri ne sauya shekar Abba a Kano
Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso tare da Gwamna Abba Kabir Yusuf Hoto: Rabiu Musa Kwankwaso
Source: Facebook

A wata hira da ya yi da Express Radio, wadda aka wallafa a shafin Facebook, Kwamanda ya ce wannan batu ba sabani ba ne, illa dai wani shiri ne da ke fitowa daga siyasar Madugun Kwankwasiyya na ƙasa.

Kwamanda ya kore saɓani tsakanin Abba da Kwankwaso

Abdulmajeed Ɗanbilki Kwamanda ya bayyana cewa Kwankwaso ne da kansa ya bayar da umarnin Abba ya koma APC, yayin da mataimakinsa zai ci gaba da zama a jam’iyyar NNPP.

A cewarsa:

“Babu saɓani tsakanin Abba Gida Gida da Kwankwaso, shiri ne irin na Kwankwaso. Abba tafi jam’iyyar APC, ka je ka tsaya takarar gwamna.”
“Shi kuma mataimakinsa zai tsaya a cikin jam’iyyar NNPP, shi kuma ya tsaya takarar gwamna a NNPP. Ka ga duk wanda ya iya ta aura, Baba ne.”
“Idan Abba ya ci, nasa ne, idan kuma Kwamared AbdulSalam ya ci, nasa ne. Wannan duk dabaru ne na siyasa. Mu tsofaffin ’yan siyasa ne.”

Kara karanta wannan

Bayan tsawon lokaci, Wike ya yi magana kan sauya shekar Gwamna Fubara zuwa APC

“Bakinsu ɗaya, a duniya sai dai mutuwa ta raba Kwankwaso da Abba Gida Gida. Shiri ne irin na Rabi’u Musa Kwankwaso.”

Kwamanda ya jaddada cewa fahimtar irin wannan tsari na siyasa yana bukatar gogewa da sanin dabarun manyan ’yan siyasa.

Kwamanda ya faɗi ra’ayinsa kan sauya sheƙar Abba

Jigo a jam’iyyar APC reshen Jihar Kano, Abdulmajeed Ɗanbilki Kwamanda, ya bayyana cewa sauya sheƙar Gwamna Abba Kabir Yusuf zuwa APC bai dame su ba ko kadan.

Dan Bilki Kwamanda ya ce ana son Abba ya tsaya takara a maimakon Barau
AbdulMajeed Dan Bilki Kwamanda, Abba Kabir Yusuf Hoto: AbdulMajeed Dan Bilki Kwamanda, Sanusi Bature D-Tofa
Source: Facebook

Ya ce:

“Na daɗe ina faɗa, ina cewa akwai shiri na cewa magoya bayan Abdullahi Umar Ganduje suna ganin da Barau ya zama gwamna, gwara Abba ya shigo. Idan ya shigo jam’iyyar APC, to a ɗauki yaronsa a ba Murtala Sule Garo mataimaki.”
“Idan an ba shi mataimaki, Abba kuma idan ya gama zuwa 2031, sannan ya ba wa Murtala Sule Garo.”

Kwamanda ya kara da cewa duk waɗannan tsare-tsare na siyasa ne da ke wanda tsohon Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ke yi don cimma manufar siyasarsa.

Abba: NNPP ta kori Shugabanta a Kano

A baya, mun wallafa cewa NNPP a mazabar Gargari da ke ƙaramar hukumar Dawakin Tofa a Kano ta sanar da tsige tare da korar shugaban jam’iyya na jiha, Hashimu Dungurawa.

Kara karanta wannan

'Mun amince Abba da Kwankwaso su jagorance mu zuwa APC,' in ji ciyamomin Kano

Hukuncin korar Shugaban jam'iyyar ya zo ne makonni biyu kacal bayan da aka sake zaɓensa a matsayin shugaban jam’iyyar NNPP na jihar Kano, bayan an zarge shi da hada rikici.

An yanke wannan hukunci ne a wani taro da aka gudanar a mazabar Gargari, ƙarƙashin jagorancin shugaban mazabar, Shuaibu Hassan da sakatarensa, Yahaya Saidu Dungurawa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng