Bayan Shirin Sauya Sheƙar Abba Ta Hargitsa Kano, NNPP Ta Kori Shugaban Jam'iyya
- Jam'iyya mai mulki a Kano, NNPP a mazabar Gargari ta kori shugaban jam’iyya na jiha, Dr. Hashimu Suleiman Dungurawa
- Shugabannin mazabar sun ce an ɗauki matakin ne bisa zargin Shugaban da tayar da rikici da saba dokokin jam’iyya
- An tura takardun hukuncin ga matakai daban-daban na jam’iyya har da jagoran NNPP ƙasa, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano –Jam’iyyar NNPP a mazabar Gargari da ke ƙaramar hukumar Dawakin Tofa a Kano ta sanar da tsige tare da korar shugaban jam’iyyar na jihar, Hashimu Dungurawa.
Hukuncin korar Dungurawa,daga jam’iyyar na zuwa ne makonni biyu kacal bayan sake zaɓensa a matsayin shugaban NNPP na jihar.

Source: Facebook
An yi taron korar a ƙarƙashin jagorancin shugaban mazabar, Shuaibu Hassan, tare da sakatarensa, Yahaya Saidu Dungurawa kamar yadda Hon. Gashash ya wallafa ta cikin wani bidiyo a shafin X.
Dalilan tsige Shugaban NNPP a jihar Kano
Shugabannin mazabar Gargari sun ce sun ɗauki wannan mataki ne bayan dogon nazari kan abubuwan da suka zargi Hashimu Dungurawa da aikatawa da dagula NNPP.
A cewar bayaninsu, Shugabannin sun ce an dauki matsayar ne a taron zartarwa na biyu da suka yi, inda shugabannin mazabar 27 suka rattaba hannu kan kudurin korar.
Sun zarge shi da haddasa rarrabuwar kai a cikin jam’iyyar, tayar da rikice-rikicen cikin gida, da gaza biyan kuɗin da suka rataya a kansa a matsayin ɗan jam'iyya kuma Shugaba a cikinta.
An zargi Dungurawa da kausasa harshe kan Abba
Haka kuma, sun ce ana zargin Dungurawa da yin kalaman batanci da cin mutunci ga Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, lamarin da suka ce bai dace ba kuma yana cutar da martabar NNPP.
A cewarsu, irin waɗannan ayyuka na barazana ne sosai ga haɗin kai, zaman lafiya da ci gaban jam’iyyar a matakai daban-daban, kuma ba za a lamunce su ba.

Source: Facebook
Shugabannin mazabar sun jaddada cewa sun bi dukkanin tanade-tanaden kundin tsarin jam’iyyar NNPP wajen ɗaukar matakin, tare da nuna cewa babu wanda ya fi ƙarfin doka.
A cikin sanarwar, shugabannin Gargari sun bayyana cewa sun riga sun tura kwafen kudurin korar zuwa ga shugabannin jam’iyyar a matakin ƙaramar hukuma, jiha da ƙasa. Sun kuma isar da sanarwar ga jagoran jam’iyyar na ƙasa, Rabiu Musa Kwankwaso, da kuma Gwamna Abba Kabir Yusuf, domin su sani tare da bayar da umarnin da ya dace.
Shugabannin mazabar sun ce wannan hukunci zai zama darasi ga duk wanda ke amfani da mukaminsa ba daidai ba ko kuma ke ganin ya fi dokokin jam’iyya ƙarfi.
Sun ƙara da jaddada cikakken biyayyarsu ga shugabancin jam’iyyar NNPP a ƙarƙashin Sanata Kwankwaso, tare da tabbatar da goyon bayansu ga gwamnatin Abba Kabir Yusuf.
Shugabannin sun ce za su ci gaba da aiki don tabbatar da zaman lafiya, haɗin kai da cigaban NNPP a Kano da ma ƙasa baki ɗaya.
Dungurawa ya zargi wasu da raba NNPP
A baya, kun ji cewa Shugaban NNPP na jihar Kano, Hashimu Sulaiman Dungurawa, ya musanta rade-radin cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf na shirin ficewa daga jam’iyyar zuwa APC.
Dungurawa ya ce jam’iyyar ta lura da yadda ake ta yaɗa jita-jita da ke cewa akwai sabani ko baraka tsakanin Gwamna Abba Kabir Yusuf da Rabiu Musa Kwankwaso.
Shugaban na NNPP ya ce dangantakar dake tsakanin Gwamna Abba Kabir Yusuf da Sanata Kwankwaso tana nan daram, kuma babu wata alamar rashin jituwa a tsakaninsu.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


