Wike Ya Yi Magana kan Shiga APC, Ya Fadi Abin da Zai Faru idan Ya Fice daga PDP
- Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya yi tsokaci kan yiwuwar ya sauya sheka daga jam'iyyar PDP zuwa APC mai mulki
- Nyesom Wike ya bayyana cewa ficewar da wasu ke yi zuwa APC, ba za ta sanya ya raba gari da jam'iyyar PDP ba
- Ministan na Abuja ya nuna cewa jam'iyyar PDP za ta shiga tsaka mai wuya duk lokacin da ya yanke shawarar barinta
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya yi magana kan sauya sheka zuwa jam'iyyar APC daga PDP.
Nyesom Wike ya ce jam’iyyar PDP za ta ruguje idan har ya sauya sheka zuwa APC mai mulki.

Source: Facebook
Jaridar The Punch ta ce Wike ya bayyana hakan ne yayin tattaunawarsa da manema labarai ta karshen shekara da aka gudanar a birnin Port Harcourt na jihar Rivers ranar Litinin, 29 ga watan Disamban 2025.
Wike ya amsa tambaya kan barin PDP
A yayin tattaunawar, Ministan na Abuja ya amsa tambayoyi kan ko yana shirin sauya sheka zuwa jam’iyyar APC mai mulki.
Magoya bayan Wike a majalisar dokokin jihar Rivers, ciki har da Gwamna Siminalayi Fubara, sun sauya sheka daga PDP zuwa APC kwanan nan.
Sai dai Wike ya jaddada cewa har yanzu shi mamba ne a jam’iyyar PDP kuma ba ya da niyyar barinta, tashar Channels tv ta kawo labarin.
“Idan a yau na ce zan sauya sheka zuwa APC, wannan shi ne karshen PDP. Za ku ga shugabannin jam’iyyar a wasu jihohi da za su biyo ni."
“Idan a yau na ce, ‘ya ku jama’a, mun gaji da PDP,’ za ku kalli wadanda za su sauya sheka a Benue; za ku kalli wadanda za su sauya sheka a Plateau, a Abia, a Edo."
“Amma kasancewar wasu sun bar PDP zuwa APC ba yana nufin dole ne ni ma na bar jam’iyyar ba. A’a, hakan ba daidai ba ne. Har yanzu ni mamba ne a PDP."
- Nyesom Wike
Me Wike ya ce kan sauya shekar Fubara zuwa APC?
Dangane da yiwuwar Gwamna Fubara ya karbe tsarin siyasar da Wike ke da shi a jihar Rivers, Ministan ya tabbatar wa magoya bayansa cewa tasirinsa a fagen siyasar jihar bai gushe ba.

Source: Facebook
Ya ce sauya shekar Fubara zuwa APC ba shi da wani tasiri sosai, yana mai cewa gwamnan ya shiga jam’iyyar ne shi kadai.
“Idan gwamna zai koma wata jam’iyya, yana tafiya ne tare da shugabannin kananan hukumomi, shugabannin jam’iyya da mambobin majalisar dokokin jiha."
“A wannan yanayin kuwa, mutanen sun riga sun bar PDP sun shiga APC da kansu. Don haka sauya shekar sa zuwa APC ba ya ba shi tabbacin samun tikitin tazarce kai tsaye."
- Nyesom Wike
Wike ya magantu kan rikicinsa da Makinde
A wani labarin kuma, kun ji cewa Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya warware zare da abawa kan rikicinsa da gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde.
Wike ya bayyana cewa rikicin ya samo asali ne bayan Gwamna Makinde ya kasa samun damar zabar Minista daga jihar Oyo.
Ministan ya nuna cewa sun yi kokarin kwantar da hankalin Makinde amma sai gwamnan ya ki ba su dama.
Asali: Legit.ng


