PDP na Tsaka Mai Wuya da INEC Ta Fitar da Sunayen 'Yan Takarar Gwamna a Zaben Ekiti

PDP na Tsaka Mai Wuya da INEC Ta Fitar da Sunayen 'Yan Takarar Gwamna a Zaben Ekiti

  • Hukumar INEC da jam'iyyun siyasa na ci gaba da shirye-shiryen zaben gwamnan jihar Ekiti, wanda za a gudanar a watan Yuni na shekarar 2026
  • Rahoto ya tabbatar da cewa INEC ta fitar da jerin sunayen 'yan takara 12 da mataimakansu, wadanda za su fafata a zaben gwamnan Ekiti
  • Sai dai abin da ya ja hankali shi ne rashin ganin sunan dan takarar gwamnan PDP da mataimakinsa, wanda ake ganin yana da alaka da rikicin jam'iyyar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Ekiti, Nigeria - Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta fitar da jerin sunayen ’yan takarar gwamna da mataimakansu a zaɓen gwamnan Jihar Ekiti da aka shirya yi a 2026.

Abin da ya fi daukar hankali a sunayen da INEC ta fitar shi ne rashin ganin sunan dan takarar gwamna na jam'iyyar PDP a zaben Ekiti da za a gudanar a ranar 20 ga Yuni, 2026.

Kara karanta wannan

Garkuwa da mutane: Sojojin Najeriya sun gwabza kazamin fada 'yan bindiga a Kano

Hukumar INEC.
Tambarin hukumar zabe mai zaman kanta ta Najeriya (INEC) Hoto: @INECNigeria
Source: Twitter

Vanguard ta rahoto cewa an liƙa jerin sunayen a ranar Litinin a ofishin INEC da ke kan titin New Iyin Road a Ado-Ekiti, babban birnin Jihar Ekiti.

Sunayen 'yan takarar gwamnan Ekiti 12

Jerin sunayen ya ƙunshi ’yan takara daga jam’iyyun siyasa 12 da ke shirin gwabza wa domin neman kujerar gwamna da mataimakinsa a jihar Ekiti.

Legit Hausa ta tattaro muku sunayen yan takarar 12 da mataimakansu kamar yadda INEC ta fitar, ga su kamar haka:

1. Gwamna mai ci, Biodun Oyebanji/Monisade Afuye (APC)

2. Opeyemi Falegan/Omoyemi Olaleye (Jam'iyyar Accord)

3. Akande Oluwasegun/Oluwasanmi Fajuyigbe (AAC)

4. Ayodeji Ojo/Itunu Ibitoye (ADP)

5. Oluwadare Bejide/Paul Olowoyeye (ADC)

6. Bidemi Awogbemi/Akinyemi Adewumi (APP)

7. Joseph Anifowose/Margaret Ilesanmi (APM)

8. Oyebanji Olajuyin/Ayokunle Okumade (jam'iyyar LP)

9. Blessing Abegunde/Francis Ajayi (NNPP)

10. Olaniyi Ayodele/Modupe Adebiyi (PRP)

11. Owoola Daramola/Opeyemi Adeyemo (YPP)

12. Victor Adetunji/Adesina Oyeniyi (ZLP)

Me yasa INEC ta cire 'dan takarar PDP?

Kara karanta wannan

Barau ya sake yi wa NNPP lahani, hadimin Abba da jigon Kwankwasiyya sun koma APC

Sai dai abin lura shi ne sunayen ’dan takarar jam’iyyar adawa ta PDP, Dr. Wole Oluyede, da mataimakinsa ba su bayyana a jerin sunayen 'yan takarar da INEC ta fitar yau Litinin ba, cewar rahoton Leadership.

Wata sahihiyar majiya a ofishin INEC ta bayyana cewa ba a saka ’dan takarar PDP ba ne saboda shari’o’in da ke gaban kotu kan rikicin shugabancin jam’iyyar, waɗanda har yanzu ba a warware su ba.

Shugaban INEC, Farfesa Amupitan.
Shugaban hukumar INEC na kasa, Farfesa Joash Amupitan Hoto: INEC Nigeria
Source: Twitter

A kwanakin baya, hukumar INEC ta gana da bangarorin PDP guda biyu kan rikicin shugabamci, inda ta yanke shawarar cewa za ta jira hukuncin kotu game da lamarin.

INEC za ta yi wa sababbin jam'iyyu rijista

A wani rahoton, kun ji cewa hukumar INEC ta sake soke bukatar kungiyoyi shida da suka nemi yin rijistar zama jam'iyyun siyasa a Najeriya.

Majiyoyi masu karfi sun nuna cewata INEC ta amince da ƙungiyoyin siyasa biyu kacal, AAP da DLA, su wuce zuwa matakin ƙarshe na rajistar zama jam’iyyun siyasa.

A watan Yunin 2025, INEC ta bayyana cewa ta karɓi buƙatu daga ƙungiyoyi 110 da ke son yin rajista a matsayin jam’iyyun siyasa a Najeriya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262