Rabuwar Abba da Kwankwaso: Sanata Hanga Ya Gargadi 'Maciya Amana a Kwankwasiyya

Rabuwar Abba da Kwankwaso: Sanata Hanga Ya Gargadi 'Maciya Amana a Kwankwasiyya

  • Sanata Rufa’i Sani Hanga ya ce masu kiran Gwamna Abba Kabir Yusuf ya koma APC ba masoyinsa ba ne, illa masu son ya juya wa talakawan da suka zaɓe shi baya
  • Dattijon ya jaddada cewa bai dace Abba Kabir ya butulce wa Rabiu Musa Kwankwaso ba, duba da irin gudunmawar da Kwankwaso ya bayar a rayuwarsa ta siyasa
  • Hanga ya sake tabbatar da tsayuwarsa a jam'iyyar NNPP, yana mai kira ga ’yan Kwankwasiyya da su guji rade-radi da masu zuga jama'a su sauya sheƙa zuwa APC

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano – Sanata Rufa’i Sani Hanga ya yi magana kan rade-radin da ke yawo na kira ga Gwamna Abba Kabir Yusuf da ya sauya sheƙa daga NNPP zuwa APC.

Kara karanta wannan

Shugaban NNPP ya fadi wadanda ake zargi da son raba Abba da Kwankwaso

Sanatan ya bayyana hakan ne yayin da ake ci gaba da muhawara a tsakanin jama’a da ’yan siyasa game da makomar siyasar Kano, musamman dangane da dangantakar Abba Kabir Yusuf da jagoran NNPP na ƙasa, Rabiu Musa Kwankwaso.

Sanata Rufa'i Hanga
Sanata Rufa'i Hanga tare da Kwankwaso. Hoto: Nigerian Senate
Source: Facebook

A wani bidiyo da shafin Kano Online News ya wallafa a Facebook, Hanga ya ce wannan kira ba alheri ba ne ga Abba Kabir Yusuf, kuma bai nuna kauna ko kishin talakawan da suka ba shi kuri’unsu ba.

Maganar Hanga kan sauya shekar Abba

Sanata Rufa’i Hanga ya ce a bayyane yake cewa duk masu kiran Abba Kabir Yusuf ya koma APC ba masoyinsa ba ne na gaskiya.

Ya ce bai kamata a zuga Abba Kabir ya juya wa talakawan Kano da suka tsaya tsayin daka suka zaɓe shi a karkashin jam’iyyar NNPP ba.

A cewarsa, duk wanda ke kiran Abba ya koma APC yana so ne ya jefa shi cikin rikici da rashin amincewar jama’a saboda ba a goyon bayan butulci a Kano.

Ko Abba Kabir zai butulcewa Kwankwaso?

Sanatan ya jaddada cewa bai dace Abba Kabir Yusuf ya butulce wa Rabiu Musa Kwankwaso ba, ganin irin rawar da Kwankwaso ya taka wajen gina siyasarsa da rayuwarsa a shekarun baya.

Kara karanta wannan

Rade radin raba hanya da Kwankwaso ta dawo da taken 'Abba tsaya da kafarka'

Aminiya ta rahoto ya ce ra’ayin cewa Kwankwaso ya tsaya a NNPP, Abba kuma ya koma APC rainin hankali ne lura da gogewar da jagoran NNPP ke da shi a babin siyasa.

A cewarsa, Kwankwaso ya wuce wannan mataki na a raba kafa, domin tafiyar Kwankwasiyya tafiya ce ta tsari da akida, ba ta amfani ta mutum ɗaya ba.

Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf
Abba Kabir Yusuf yana bayani a wani taro. Hoto: Sanusi Bature D-Tofa
Source: Facebook

Hanga ya ƙara da cewa ba za su goyi bayan wanda zai goyi bayan butulci ga jagora ba, yana mai cewa ya kamata Abba Kabir Yusuf ya hukunta masu zuga shi.

Sanatan na NNPP bai ma yarda cewa Abba yana da wannan tunani ba, amma ya tuna wa jama'a cewa mutanen Kano ba su wasa da cin amana a siyasa.

Makomar alakar Hanga da Kwankwaso

Sanata Rufa’i Hanga ya bayyana cewa duk da yadda ake bi ana ba Sanatoci kuɗi masu nauyi domin su sauya sheƙa, shi bai bar NNPP ba.

Ya ce tsayuwarsa da Rabiu Musa Kwankwaso dari bisa dari ce, domin ya fahimci Kwankwaso yana abubuwa ne domin neman kawo cigaba.

Da aka tambaye shi idan gwamna ya koma APC da Abba zai tafi ko Kwankwaso, Hanga ya ce babu shakka yana tare da Kwankwaso.

Kara karanta wannan

Ana maganar makomar Kwankwaso da Ganduje yayin da Abba zai koma APC

Sanata Hanga ya yi kira ga ’yan Kwankwasiyya da su fahimci cewa hanya ɗaya ce a tafiyar su, kuma babu wani tunani na rarrabuwar kai.

NNPP ta magantu kan siyasar Kano

A wani labarin, kun ji cewa shugaban jam'iyyar NNPP na jihar Kano, Hashim Sulaiman Dungurawa ya yi magana kan rade-radin sauya shekar Abba Kabir Yusuf.

Shugaban ya bayyana cewa suna sane da labarin da ake yadawa a kafafen sada zumunta amma suna kira ga 'yan jam'iyyar da kada su koma APC.

Ya kuma bukaci dukkan 'yan NNPP a Kano da Najeriya baki daya su cigaba da goyon bayan madugun jam'iyyar na kasa, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng