Majiyoyi Sun Fadi Ranar da Gwamnan Kano, Abba Zai Sanar da Komawa APC

Majiyoyi Sun Fadi Ranar da Gwamnan Kano, Abba Zai Sanar da Komawa APC

  • Alamu sun nuna cewa jita-jitar sauya sheƙar gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, na dab da zama gaskiya bayan jawabin jam'iyyarsa ta NNPP
  • Batun sauya jam’iyya ya kara daukar hankali ne bayan an samu labarin cewa Gwamnan Kano na shirin barin Sanata Rabiu Musa Kwankwaso a NNPP
  • Majiyoyi sun sanar da Abba Gida Gida zai sanar da ranar sauya sheka zuwa jam'iyya mai mulki, duk da har yanzu bai ce komai ba game da shirinsa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – A yanzu haka, kusan babu abin da ake tattaunawa a kafafen yada labarai da majalisun siyasa a Kano face batun ko gwamnan jihar, Abba Kabir Yusuf, zai bar jam’iyyar NNPP ya koma APC.

Jita-jitar da aka dade ana ji kamar magana ce kawai, amma yanzu ta fara daukar sabon salo, inda ake ganin Gwamnan ya gama tattare kayansa daga NNPP.

Kara karanta wannan

Rabuwar Abba da Kwankwaso: Sanata Hanga ya gargadi 'maciya amana' a Kwankwasiyya

Ana sa ran Abba zai sanar da sauya sheka da bakinsa
Gwamnan Kani, Abba Kabir Yusuf Hoto: Abba Kabir Yusuf
Source: Facebook

Wata majiya ta shaidawa BBC Hausa cewa ana rade-radin gwamnan Kano na iya bayyana matsayinsa a fili a yayin taron majalisar zartarwar jihar da ake sa ran za a gudanar nan kusa.

Ana zaton Gwamna Abba zai koma APC

Duk da karfin labarin sauya shekar Gwamnan Kano, har yanzu Abba Kabir Yusuf bai ce komai ba, amma makusantansa suna maganar cewa za su iya sauya sheka.

A gefe guda kuma, hankulan jama’a sun koma kan jagoran Kwankwasiyya, Rabi’u Musa Kwankwaso, inda ake tambaya ko shi ma zai bi gwamnan idan har ya sauya sheƙa.

Wata majiya kusa da Kwankwaso ta tabbatar da cewa tsohon gwamnan Kano zai ci gaba da zama a NNPP, yayin da babban makusancinsa ke shirin komawa APC.

Martanin NNPP game da sauya shekar Abba

Shugaban jam’iyyar NNPP a Kano, Hon. Suleiman Hashim Dungurawa, ya ce jam’iyyar ba ta da hannu a duk wani shiri na sauya sheƙar gwamnan Kano zuwa APC.

Kara karanta wannan

Rade radin raba hanya da Kwankwaso ta dawo da taken 'Abba tsaya da kafarka'

Ya bayyana cewa duk wanda ya yanke shawarar barin jam’iyyar, ya yi hakan ne bisa ra’ayinsa na kansa, kuma lamarin bai yi masu dadi ba.

Ana sa ran Abba zai tafi APC ya bar Kwankwaso a NNPP
Gwamna Abba Kabir Yusuf a yayin da ya ke mika lambar yabo ga Kwankwaso Hoto: Sanusi Bature D-Tofa
Source: Facebook

A cewarsa, shugabancin jam’iyyar a matakin jiha da kasa, ciki har da Kwankwaso, sun yi iya kokarinsu wajen ganin gwamnan da magoya bayansa sun zauna a NNPP, amma duk da haka abubuwa sun gagara.

Dungurawa ya kuma roki gwamnan Kano da ya sake tunani, yana mai cewa barin jam’iyyar da jama’a suka amince da ita zuwa wata jam’iyyar da aka yi watsi da ita ba zai amfani Kano ba.

Ana shirin tarbar Abba a jam'iyyar APC

A baya, mun wallafa cewa kungiyar tsohon Minista, Abdullahi Tijjani Gwarzo (ATM Gwarzo) ta nuna goyon bayanta kan rahotannin da ke cewa gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, zai dawo APC.

A sanarwar da Babban Sakatare na Musamman ga Abdullahi Tijjani Gwarzo, Kabiru Salihu Bako, ya sanya hannu, an bayyana cewa wannan sauyi zai zo a kan lokaci mai kyau ga jihar Kano.

Sanarwar ta ce idan Kano ta yi aiki kafada da kafada da gwamnatin tarayya, hakan zai samar da damar haɗin gwiwa mai ƙarfi wanda zai taimaka wajen sauri aiwatar da ayyukan raya kasa a jihar.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng