Shugaban NNPP Ya Fadi Wadanda ake Zargi da Son Raba Abba da Kwankwaso
- Shugaban jam’iyyar NNPP na jihar Kano, Hashimu Sulaiman Dungurawa, ya magantu kan rade-radin cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf na shirin komawa APC
- Dungurawa ya ce jita-jitar da ake yadawa na cewa wasu manyan ’yan NNPP na ƙoƙarin raba Rabiu Musa Kwankwaso da Abba Kabir Yusuf ba ta da tushe
- NNPP ta yi kira ga mambobinta a Kano da matakin ƙasa da su tsaya daram cikin jam’iyyar tare da ci gaba da goyon bayan Kwankwaso da gwamnatin jihar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kano – Shugaban jam’iyyar NNPP na jihar Kano, Hashimu Sulaiman Dungurawa, ya fito ya yi bayani kan rade-radin da ke yawo cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf na shirin ficewa daga NNPP zuwa jam’iyyar APC.
Dungurawa ya ce jam’iyyar ta lura da yadda ake ta yada jita-jita da zarge-zarge a kafafen sada zumunta da wasu wurare, inda ake ƙoƙarin nuna cewa akwai baraka tsakanin Abba Kabir Yusuf da jagoran NNPP na ƙasa, Rabiu Musa Kwankwaso.

Source: Facebook
A bayanin da ya yi a wani bidiyo da Abba Gwale ya wallafa a Facebook ya ce wasu abubuwan da ake fada basu da tushe balle makama duk da sun san akwai wasu masu shirin fita daga NNPP.
Wane ne masu son raba Abba da Kwankwaso?
Dungurawa ya ce zargin da ake yi na cewa shi da wasu manyan ’yan NNPP, ciki har da Mataimakin gwamnan Kano, Sanata Rufa’i Sani Hanga da Sanusi Sirajo Kwankwaso, suna ƙoƙarin raba Rabiu Musa Kwankwaso da Abba Kabir Yusuf, ƙarya ce tsagwaronta.
A cewarsa, ana yada wannan zargi ne kawai saboda kusancin da suke da shi da Gwamna Abba Kabir Yusuf, wanda hakan ya sa wasu ke ƙoƙarin fassara al’amura ba daidai ba.
Matsayar NNPP kan komawa jam'iyyar APC
Shugaban NNPP na Kano ya ce jam’iyyar ta san da rade-radin da ake yi cewa Abba Kabir Yusuf zai koma APC, amma ya jaddada cewa babu wata niyya daga bangaren jam’iyyar ko shugabanninta na komawa APC.
Ya ce a matsayinsa na shugaban jam’iyyar a Kano, kuma yana magana a madadin shugabannin NNPP na jiha da na ƙasa, yana tabbatar wa jama’a cewa NNPP ta tsaya tsayin daka kan matsayar.

Source: Facebook
BBC Hausa ta wallafa a X cewa shugaban jam'iyyar ya yi kira ga Abba Kabir Yusuf da ya cigaba da zama a NNPP ba tare da sauya sheka zuwa APC ba.
Dungurawa ya yi kira ga al’ummar jihar Kano da na ƙasa baki ɗaya da su ci gaba da goyon bayan jam’iyyar NNPP da jagoranta, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.
Muaz Magaji ya goyi bayan Abba Kabir
A wani labarin, mun kawo muku cewa tsohon kwamishinan Kano a lokacin Abdullahi Umar Ganduje ya yi magana kan rade-radin sauya shekar Abba Kabir Yusuf.
Injiniya Muaz Magaji ya bayyana cewa a yanzu haka Abba Kabir Yusuf ya nuna cewa zai tsaya da kafarsa, kuma za su goyi bayansa dari bisa dari.
Sai dai wasu jama'a sun yi martani da cewa tsohon kwamishinan bai fahimci yadda lamarin ya ke ba, kuma ba lallai abin da ya ke zato ya faru ba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

