Rade Radin Raba Hanya da Kwankwaso Ya Dawo da Taken 'Abba Tsaya da Kafarka'
- Ana ci gaba da rade-radin cewa gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, na shirin barin NNPP zuwa APC, duk da rashin sanarwa a hukumance
- Tsohon kwamishinan Kano a lokacin Abdullahi Ganduje, Mu’az Magaji, ya bayyana shirinsa na goyon bayan gwamnan idan ya shiga APC
- Kalaman Mu’az sun sake tayar da muhawara kan tsohon taken “Abba tsaya da kafarka” da aka taba alakantawa da batun tasirin Rabiu Kwankwaso
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kano – Duk da cewa har yanzu babu wata sanarwa a hukumance kan fitan gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, daga jam’iyyar NNPP, ana ci gaba da samun rade-radi da muhawara kan lamarin.
Batun ya kara daukar sabon salo bayan tsohon kwamishinan Kano, Mu’az Magaji, ya fito ya bayyana cewa yana goyon bayan sauyin da ake shirin samu.

Source: Facebook
Muaz Magaji zai tallafa wa Abba Kabir
Mu’az Magaji, wanda ya taba aiki a gwamnatin tsohon gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya wallafa a Facebook cewa a shirye yake ya mara wa Abba Kabir Yusuf baya idan gwamnan ya yanke shawarar shiga jam’iyyar APC.
A cewarsa:
“Abba zai tsaya da kafarsa, mu kuma za mu tallafa masa in sha Allah.”
Wannan furuci ya sake tayar da tsohon taken “Abba tsaya da kafarka,” wanda a baya aka rika amfani da shi wajen kira ga gwamnan da ya nisanta kansa daga tasirin jagoran NNPP, Rabiu Musa Kwankwaso.
Asalin taken 'Abba tsaya da kafarka'
Rahotanni sun nuna cewa wannan taken ya fara fitowa ne kafin gwamnan ya yi sauye-sauye a majalisar zartarwarsa, inda daga bisani aka sauke manyan jami’ai, ciki har da sakataren gwamnatin jihar Kano.
Bayan wadannan matakai, taken “Abba tsaya da kafarka” ya ja baya, lamarin da ya sanya wasu suka yi imanin cewa matsalar ta wuce.

Source: Facebook
Sai dai, bayan bullar labaran da ba a tabbatar ba na cewa Abba Kabir Yusuf na duba yiwuwar shiga APC, Mu’az Magaji ya sake farfado da taken, yana mai alakanta shi da sabon yanayin siyasa da ke tasowa a Kano.
Martanin jama'a ga Mu'az Magaji
Kalaman Mu’az Magaji sun jawo martani mabambanta daga ‘yan Najeriya. Aliyu Muhd Gadanya ya ce masu yada irin wadannan sakonni na yaudarar kansu ne, yana mai cewa har yanzu ba su fahimci “salon wasan siyasa” ba.
A nasa bangaren, Musa Fagge ya bayyana cewa wasu ‘yan siyasa na murnar labarin sauyin sheka, amma ya ce ko Abba Kabir Yusuf shi kadai ya shiga APC, hakan zai iya sauya siyasar Kano.
Mustafa Mujitaba Tahir ya yi nuni da cewa ana gudanar da manyan shirye-shiryen siyasa a bayan fage, yana mai gargadin cewa wasu za su iya tsintar kansu cikin rudani.
Sai dai Abba N. Abubakar ya kare Rabiu Musa Kwankwaso, yana mai cewa har yanzu jagora ne abin koyi, duk da cewa ba lallai ne ya bi tafiyarsa ba.
An ce Abba zai koma APC daga NNPP
A wani labarin, kun ji cewa hadimin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, Bashir Ahmad ya ce ya samu labarin sauya shekar Abba Kabir Yusuf.
Bashir Ahmad ya sanar da cewa wata majiya mai tushe ce daga jam'iyyar APC ta tabbatar masa da cewa gwamnan zai sauya sheka.
Jama'a da dama sun yi martani game da rade-radin tare da tambayoyi kan yadda makomar manyan 'yan siyasa za ta kasance a jihar.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


