Ana Maganar Makomar Kwankwaso da Ganduje yayin da Abba zai Koma APC

Ana Maganar Makomar Kwankwaso da Ganduje yayin da Abba zai Koma APC

  • Ana ci gaba da samun sababbin bayanai kan yiwuwar Gwamna Abba Kabir Yusuf ya fice daga NNPP zuwa APC, lamarin da ke tayar da kura a siyasar Kano
  • Wani makusancin marigayi shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce an ce gwamnan ya kammala shirye-shiryen shiga APC gabanin tarukan jam’iyyar da ke tafe
  • Martani daga jama’a ya nuna rabuwar kai, inda wasu ke ganin hakan zai sauya ma’aunin iko a Kano, wasu kuma na tambayar makomar manyan ‘yan siyasa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano – Rade-radin siyasa sun sake daukar sabon salo a Jihar Kano yayin da ake ta ce-ce-ku-ce kan yiwuwar Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bar jam’iyyar NNPP domin komawa jam’iyyar APC mai mulki.

Maganar ta zo ne a daidai lokacin da jam’iyyar APC ke shirin gudanar da tarukan ta na kasa da jihohi, lamarin da ya sa wasu ke danganta rade-radin da kokarin sake tsara karfin siyasa a Kano gabanin babban zaben 2027.

Kara karanta wannan

Bayan farmakin Amurka a Sokoto, mayakan ISWAP sun kai kazamin hari Yobe

Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf
Abba Kabir Yusuf da aka ce zai koma APC daga NNPP. Hoto: Sanusi Bature D-Tofa
Source: Facebook

Shirin Abba Kabir na komawa APC

A sakon da ya wallafa a X, Bashir Ahmad da ya kasance hadimi ga tsohon shugaban kasa Buhari, ya bayyana cewa an ce gwamnan Kano ya kammala shirye-shiryensa na shiga APC kafin tarukan jam’iyyar a 2026.

A cewar Bashir Ahmad, gwamna Abba Kabir Yusuf ya riga ya yanke shawarar barin NNPP da ya ci zabe a cikinta, sai ya shiga jam’iyyar APC.

Wani rahoton Daily Nigerian kuma ya nuna cewa kasancewar APC ta shirya gudanar da tarukanta a watan Fabrairu, gwamnan ya tsara yadda zai shiga cikin harkokin tarukan domin samun cikakken iko da tafiyar jam’iyyar a jihar.

Rahoton ya nuna cewa wannan mataki na daga cikin dabarun siyasa da ake ganin za su iya sauya tsarin jagoranci a APC a Kano.

Makomar Kwankwaso, Ganduje da Barau

A kafar X, wani mai amfani da suna @thekanoblog ya ce idan har gwamnan Kano ya koma APC, to burin wasu ‘yan siyasa zai cika.

Kara karanta wannan

Kano: An tabbatar da cewa Abba Kabir Yusuf zai koma APC daga jam'iyyar NNPP

Sai dai ya tambaya makomar Sanata Barau Jibrin da Abdullahi Ganduje, yana mai tambayar wanda zai zama jagoran APC a Kano idan hakan ta tabbata.

Abdullahi Umar Ganduje da Barau Jibrin
Sanata Barau Jibrin da Abdullahi Ganduje suna zaune. Hoto: Barau I Jibrin
Source: Twitter

Wani mai suna @realChrisIheme ya bayyana cewa ko da dukkan gwamnonin Najeriya sun koma APC nan da 2027, ba za su hana 'yan adawa tasiri ba.

Ya kuma yi tambaya kan makomar jagoran NNPP, Rabiu Musa Kwankwaso, wanda ake dauka a matsayin jagoran siyasar Abba Kabir Yusuf.

Bashir ya ce Abba zai koma APC

A wani labarin, kun ji cewa hadimin tsohon shugaban kasa, Bashir Ahmad ya ce wata majiya mai tushe ta sanar da shi cewa Abba Kabir Yusuf zai koma APC.

Bashir Ahmad ya bayyana cewa za su yi maraba da Abba Kabir Yusuf idan ya sauya sheka daga NNPP zuwa jam'iyyar APC mai mulki.

Jama'a da dama a Najeriya, musamman 'yan Kano na tofa albarkacin baki game da lamarin, tare da tambayoyi a kan makomar siyasar jihar.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng