2027: Shugaban Hukuma a Kano Ya 'Gano' Makomar Abba ana batun zai Rabu da Kwankwaso

2027: Shugaban Hukuma a Kano Ya 'Gano' Makomar Abba ana batun zai Rabu da Kwankwaso

  • Darektan a hukumar KASA a Jihar Kano ya gargadi Sanata Barau I Jibrin kan sukar gwamnatin Kano
  • Ya ce sukar ta samo asali ne daga burin siyasar Barau na samun kujerar Gwamna Abba Kabir Yusuf a 2027
  • Dakata ya bukaci Sanatan ya mayar da hankali kan ayyukan talakawa duba da cewa ba shi da rabo a zama Gwamna a zabe.mai zuwa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – Darekta a Hukumar kula da allunan tallace-tallace ta Kano (KASA), Kabiru Sa’id Dakata, ya gargadi Sanata Barau Jibrin da ya daina kushe ayyukan gwamnatin Abba Kabir Yusuf

Ya bayyana haka ne a matsayin martani ga yadda Sanata Barau ke yawan sukar ayyuka da manufofin gwamnatin Abba Kabir Yusuf a Kano.

Kara karanta wannan

Kano: An tabbatar da cewa Abba Kabir Yusuf zai koma APC daga NNPP

Dakata ya ja kunnen Barau kan neman kujerar Abba
Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf, Sanata Barau I Jibrin Hoto: Sanusi Bature D-Tofa/Barau I Jibrin
Source: Facebook

Dakata ya yi wannan bayani ne a wata hira da ya yi da Freedom Radio, wacce aka wallafa a shafin Facebook na kafar watsa labaran.

Shugaban hukuma a Kano ya dura kan Barau

Kwamred Kabiru Sa’id Dakata ya bayyana cewa adawar da Sanata Barau ke yi wa gwamnatin Abba Kabir Yusuf ba ta rasa nasaba da burinsa na siyasa, musamman maye gurbin gwamna a zaben 2027.

A cewarsa, Sanata Barau na nuna rashin jin dadi ne saboda ya fahimci cewa Abba Kabir Yusuf na da karbuwa a wurin al’ummar Kano, kuma hakan na iya hana shi cimma burinsa na siyasa.

Dakata ya ce:

“Mai girma gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, za a sake zabensa a shekarar 2027, zai kammala wa’adinsa na shekaru hudu, sannan ya sauka a shekarar 2031."
"Idan Allah ya so, zai iya zuwa matakin tarayya, ko a matsayin Sanata, ko Shugaban Kasa, ko Minista. Allah ne kaɗai ya san abin da Ya tanadar masa bayan shekarar 2031.”

Kara karanta wannan

Manyan jam'iyya sun fara shirin tarbar Gwamnan Kano Abba zuwa APC

Ya kara da cewa Sanata Barau na ganin burinsa na takara ba zai cika ba, shi ya sa yake nuna fushi da jin haushi ta hanyar sukar ayyukan gwamnan Kano.

Tuni mu ke yi wa Barau – shugaban hukuma

Kwamred Dakata ya ce su kan yi wa Sanata Barau I. Jibrin tuni a kan abubuwan da suka shafi nauyin da ke kansa na wakiltar jama’a a Majalisar Dattawa, musamman wajen kare muradun talakawan Najeriya.

Dakata ya ce Kanawa za su sake zaben Abba a 2027
Kabiru Sa'id Dakata, Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf Hoto: Kabiru Dakata
Source: Facebook

Ya ce:

“Mun ce masa maimakon ya rika nuna haushi da ci gaban da ake samu a Jihar Kano, ya fi dacewa ya mayar da hankali kan abin da ya dace a lokacin da aka kawo dokar haraji a gabansu.”

Ya kara da cewa da Sanatan ya yi la’akari da irin matsin da dokar harajin za ta jefa talakawa a ciki, da ba a kai ga wannan matsaya ba.

Dakata ya ce:

“Yanzu ana fargabar cewa duk lokacin da aka fara aiwatar da dokar, Allah kaɗai ya san irin halin da al’ummar Najeriya za su shiga."

Kwamred Kabiru Sa’id Dakata ya jaddada cewa idan maganar zaben gwamnan Kano ta taso, al’ummar jihar sun riga sun yarda da Abba Kabir Yusuf, kuma za su kuma zabensa.

Kara karanta wannan

Harin Amurka: Ndume ya roƙi Tinubu da Donald Trump game da yaƙi da ta'addanci

Tsohon Minista na son Abba ya koma APC

A baya, kun samu labarin cewa kungiyar tsohon Ministan Sadarwa, Abdullahi Tijjani Gwarzo, wato ATM Gwarzo Organization, ta bayyana farin cikinta kan rahotannin sauya shekar Gwamna.

Kungiyar ta bayyana cewa sauyin jam’iyyar da ake hasashe zai iya taimaka wa Kano wajen samun kusanci da gwamnatin tarayya, lamarin da zai buɗe ƙofofi da dama na ci gaba

Wannan bayani na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Kabiru Salihu Bako, Babban Sakatare na Musamman ga Abdullahi Tijjani Gwarzo, ya sanya wa hannu a ranar Lahadi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng