Kano: An Tabbatar da cewa Abba Kabir Yusuf zai Koma APC daga NNPP
- Ana ta tattaunawa a fagen siyasar Kano kan yiwuwar Gwamna Abba Kabir Yusuf ya fice daga jam’iyyar NNPP zuwa APC, lamarin da ya jawo ce-ce-ku-ce a kafafen sada zumunta
- Wani kusa da tsohon Shugaban kasa Muhammadu Buhari, Bashir Ahmad, ya ce yana da sahihin bayani cewa gwamnan zai koma APC nan da ‘yan makonni masu zuwa
- Bayanin ya haifar da martani iri-iri daga jama’a, inda wasu ke nuna shakku kan dalilan komawar, wasu kuma na ganin hakan cin amana ne ga masu kada kuri’a a jihar Kano
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kano – Rade-radin siyasa sun karade Jihar Kano biyo bayan jita-jitar cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf na shirin barin jam’iyyar NNPP domin komawa jam’iyyar APC.
Batun ya dauki sabon salo ne bayan wani makusancin tsohon Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya fito da magana a bainar jama’a.

Source: Facebook
Bashir Ahmad, wanda ya kasance mai taimaka wa tsohon Shugaban kasa Buhari, ya tayar da kura a shafinsa na X, inda ya bayyana cewa gwamnan Kano zai koma APC a nan gaba kadan.
Bashir ya ce Abba zai koma APC
A cewar Bashir Ahmad, yana da tabbacin cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf zai shiga jam’iyyar APC nan da ‘yan makonni masu zuwa. Wannan furuci ya sa jama’a da dama suka fara fassara al’amuran siyasa a Kano ta hanyoyi daban-daban.
Ko da yake bai yi karin bayani kan dalilan da suka sa yake da wannan tabbaci ba, kalamansa sun isa su jawo ce-ce-ku-ce, musamman daga masu bibiyar siyasar Arewa da kuma magoya bayan jam’iyyun NNPP da APC.
Martanin jama’a kan shigar Abba APC
Bayan sakon da Bashir Ahmad ya fitar, jama’a da dama sun mayar da martani wasu na goyon baya, wasu kuma na suka ga lamarin.

Kara karanta wannan
Kano: Barau ya zargi Abba da take hakkin Alfindiki, ya ba shi kudin da aka hana shi
Wani mai amfani da shafin X mai suna @thekanoblog ya ce duk da ana iya ganin alamun sauyin sheka, akwai bukatar a fahimci cewa wasu daga cikin mutanen da ke zagaye da gwamnatin Kano na ingiza gwamnan zuwa APC ne ba don son jam’iyyar ba.
A cewarsa, wasu na yin hakan ne saboda tsoron hukuma mai yaki da cin hanci da rashawa, yana mai cewa irin wadannan mutane ba su da cikakkiyar biyayya ga gwamnan, illa kawai saboda yana kan mulki.
Ya kuma yi gargadin cewa irin wadannan ‘yan siyasa ne a baya suka jefa tsohon gwamnan Kano Abdullahi Ganduje cikin yanayi mai sarkakiya.

Source: Facebook
Wani mai amfani da X, @GreatMichael1, ya ce yadda 'yan APC suka rika yabon Rabiu Musa Kwankwaso a kwanakin baya ya sa ya fahimci cewa wani abu na siyasa na faruwa a bayan fage.
A nasa bangaren, @The_Great_JiRI ya bayyana cewa idan har labarin gaskiya ne, to hakan tamkar cin fuska ne ga duk wadanda suka kada kuri’a ga NNPP a Kano.
An kira Abba Kabir ya shiga APC
A wani labarin, kun ji cewa wani jami'in gwamnatin Kano, Abdullahi Ibrahim Rogo ya yi kira ga Abba Kabir Yusuf ya shiga jam'iyyar APC.
Abdullahi Rogo ya bayyana cewa suna tare da Abba Kabir Yusuf da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso a harkokin siyasar Kano da kasa baki daya.
Duk da tabbatar da biyayya da shugabannin NNPP a Kano, Rogo ya yi kira gare su da su jagorance su zuwa jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya.
Asali: Legit.ng

