Manyan Jam'iyya Sun Fara Shirin Tarbar Gwamnan Kano Abba zuwa APC

Manyan Jam'iyya Sun Fara Shirin Tarbar Gwamnan Kano Abba zuwa APC

  • Kungiyar tsohon Minista ta ATM Gwarzo ta nuna goyon baya ga yiwuwar sauya sheƙar Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf
  • Kungiyar ta bayyana cewa sauya shekar Gwamnan za ta jawo kusanci tsakanin Kano da gwamnatin tarayya, kuma za a samu tagomashi
  • Ta tabbatar wa gwamnan cikakken goyon baya domin haɗin kai da cigaban jihar, inda ta fara yi masa maraba da shirin shiga APC

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – Kungiyar tsohon Minista Abdullahi Tijjani Gwarzo ta ATM Gwarzo ta bayyana farin cikinta kan rahotannin da ke cewa Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, na iya ficewa daga NNPP zuwa APC.

A cewar kungiyar, wannan mataki zai zo a kan lokaci mai kyau kuma zai amfani Kano ta fannoni da dama da jawo ci gaba mai dorewa.

Kara karanta wannan

Hadimin Abba ya hada gangami, yana roƙon Gwamna da Kwankwaso su ja su zuwa APC

ATM Gwarzo na son Abba ya koma APC
Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf Hoto: Sanusi Bature D-Tofa
Source: Facebook

Wannan na kunshe a cikin wata sanarwar, da Kabiru Salihu Bako, Babban Sakatare na Musamman ga Abdullahi Tijjani Gwarzo ya sanya wa hannu kuma aka wallafa ta a shafin Facebook na kungiyar.

Kano: Jigo a APC na maraba da Abba

Kungiyar ta ce idan Kano ta yi aiki kafaɗa da kafaɗa da gwamnatin tarayya, hakan zai buɗe ƙofofin haɗin gwiwa mai ƙarfi, da kuma hanzarta aiwatar da ayyukan raya ƙasa a jihar.

ATM Gwarzo ta jaddada cewa haɗin kai tsakanin jiha da tarayya na da matuƙar muhimmanci wajen cimma muradun jama’a da ci gabansu.

Bayan haka, ta ce manufofi da sauye-sauyen da ake aiwatarwa a matakin tarayya sun samar da ingantaccen tubali da Kano za ta iya amfani da shi domin bunƙasa tattalin arziƙi.

Abdullahi Gwarzo na maraba da Abba a APC ta Kano
Tsohon Minista a Najeriya, Abdullahi T Gwarzo Hoto: Abdullahi T Gwarzo
Source: Facebook

Haka kuma kungiyar na ganin hakan zai kara inganta shugabanci, da kuma bunƙasa ababen more rayuwa a sassa daban-daban na jihar Kano.

A cewar sanarwar:

Kara karanta wannan

Gwamnatin Sokoto ta fito da bayanai kan harin da Amurka ta kai jihar

"Muna ganin wannan mataki ba kawai ya zo a kan lokaci ba ne, abu ne da ya dace, musamman idan aka yi la’akari da irin gagarumin ci gaban da ake samu a halin yanzu."
"Manufofi da tsare-tsaren da ake aiwatarwa sun samar da ingantaccen tsari na cigaba mai ɗorewa, farfaɗo da tattalin arziƙi, da gina manyan ababen more rayuwa, wanda hakan zai amfani Kano matuƙa.”

Gwamnatin tarayya za ta taimaki Kano - ATM Gwarzo

Kungiyar ta kara da cewa kusantar gwamnatin tarayya za ta taimaka wa Kano wajen samun kyakkyawan sauƙin aiwatar da ayyuka a bangaren lafiya da sauransu.

Ta bayyana cewa idan aka samu cikakken fahimta da haɗin kai, jama’ar Kano za su fi cin gajiyar shirye-shirye da tallafin da ke fitowa daga matakin tarayya.

Sanarwar ta kuma tabbatar wa Gwamna Abba Kabir Yusuf cikakken goyon baya daga kungiyar, tare da alkawarin yin aiki tare da duk wani shiri da zai kawo ci gaban Kano.

Sanarwar ta ce:

“Muna tabbatar wa Mai Girma Gwamna Abba Kabir Yusuf cikakken goyon baya da haɗin kai a wannan al’amari, tare da jaddada jajircewarmu wajen duk wani yunƙuri da zai ƙarfafa haɗin kai, cigaba, da amfanin bai ɗaya ga Jihar Kano da ƙasar Najeriya baki ɗaya."

Kara karanta wannan

Sheikh Gumi ya aika sako ga Tinubu bayan harin Amurka a Sakkwato

Kungiyar ta kara da cewa duk wani mataki da zai kawo ci gaba, rage matsalolin jama’a, da ɗora Kano a sahun gaba na jihohin da ke cin moriyar hadin gwiwar tarayya, abu ne da ya dace a yi maraba da shi.

Ana so Abba, Kwankwaso su koma APC

A baya, mun wallafa cewa Darekta mai kula da harkokin gidan gwamnatin Kano, Abdullahi Ibrahim Rogo, ya buƙaci Rabi’u Musa Kwankwaso da Abba Kabir Yusuf su koma APC.

Abdullahi Ibrahim Rogo ya bayyana wannan roƙo ne a yayin wani taron ƴan jam’iyya, inda ya ce wannan buƙata ta fito ne daga ra’ayin mabiyan Kwankwasiyya baki ɗaya.

A cewarsa, duk da wannan buƙata, ƴan Kwankwasiyya har yanzu suna mutunta jagorancin Kwankwaso da Gwamna Abba Kabir Yusuf, kuma suna tare da su a harkokin siyasa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng