Hadimin Abba Ya Hada Gangami, Yana Roƙon Gwamna da Kwankwaso Su Ja Su zuwa APC

Hadimin Abba Ya Hada Gangami, Yana Roƙon Gwamna da Kwankwaso Su Ja Su zuwa APC

  • Daraktan gidan gwamnatin Kano, Abdullahi Ibrahim Rogo, ya roki Gwamna Abba Kabir Yusuf da Rabi'u Musa Kwankwaso su ja su zuwa APC
  • Rogo ya ce har yanzu suna tare da Kwankwaso da Abba, amma suna ganin APC ce mafitar siyasar su a yanzu saboda wadansu dalilai
  • Ya ce burin sauya sheka shi ne ci gaban Kano da kuma makomar siyasar Kwankwaso matukar yana son ya zama Shugaban Kasar nan a nan gaba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – Darekta mai kula da harkokin gidan gwamnatin Kano, Abdullahi Ibrahim Rogo, ya roki Gwamna Abba Kabir Yusuf da Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso da su jagoranci mabiyansu zuwa APC.

Rogo ya mika wannan buƙata ne a yayin wani taron ƴan jam’iyya, inda ya jaddada cewa har yanzu suna tare da Kwankwaso da Gwamna Abba Kabir Yusuf.

Kara karanta wannan

Manyan jam'iyya sun fara shirin tarbar Gwamnan Kano Abba zuwa APC

Ana so Kwankwaso da Abba su bar APC
Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso da Gwamna Abba Kabir Yusuf Hoto: Rabiu Musa Kwankwaso
Source: Facebook

A wani bidiyo da Premier Radio ta wallafa a shafinta na Facebook, Abdullahi Ibrahim Rogo ya bayyana cewa ƴan Kwankwasiyya sun mika wannan buƙata ne bisa ganin APC ce mafitar siyasarsu.

Ƴan Kwankwasiyya na son komawa jam'iyyar APC

A jawabin da ya gabatar, Abdullahi Ibrahim Rogo ya ce 'yan jam'iyyar gudanar da zama na musamman domin tattauna batun kafin fito da matsayar su a bainar jama’a.

Ya ce:

"Da farko dai, mun amince cewa mai girma jagora, Injiniya Dr. Rabi’u Musa Kwankwaso, shi ne jagoran wannan tafiya, kuma shi ne abin koyi a gare mu a harkokin siyasa.”

Ya kara da cewa:

“Haka kuma, wannan zama ya amince cewa mai girma jagora da kuma mai girma Gwamna, mun yarda kuma mun amince da su tafi jam’iyyar APC gaba ɗaya.”

Dalilin ƴan Kwankwasiyya na harin APC

Abdullahi Ibrahim Rogo ya bayyana cewa ba wani abu ne ya sa suke neman sauya sheka zuwa jam’iyya mai mulki ba face burin ganin an samu ci gaban Kano da al’ummarta.

Kara karanta wannan

Kwankwaso ya gabatar da sama da masu digirin PhD 300 da Kwankwasiyya ta horar

Rogo na ganin sauya shekar Kwankwaso da Abba ce mafitarsu
Jagoran Kwankwasiyya Rabi'u Musa Kwankwaso da Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf Hoto: Sanusi Bature D-Tofa
Source: Facebook

A cewarsa:

“Saboda ci gaban al’ummarmu, da kuma ci gaban Injiniya Dr. Rabi’u Musa Kwankwaso kansa, muna hangen cewa, in Allah Ya yarda, nasararsa da burinsa na zama Shugaban Najeriya za su fi yiwuwa idan yana cikin jam’iyyar APC a nan gaba."

Rogo ya kara da cewa dukkanin masu ruwa da tsaki a NNPP da kuma Kwankwasiyya a karamar hukumar Rogo sun amince da wannan matsaya domin cimma burinsu na siyasa.

Ya yi kira ga dukkannin ƴaƴan NNPP da su guji cin mutuncin juna, tare da kaucewa fadin kalaman da za su haddasa rarrabuwar kai ko bata sunan jagororinsu.

Gargaɗin Kwankwaso game da tsaro

A baya, kun ji cewa tsohon Gwamnan Kano kuma dan takarar shugaban kasa na NNPP a zaben 2023, Rabi’u Musa Kwankwaso, ya bayyana damuwa kan tabarbarewar tsaro. Kwankwaso, wanda ya taba rike mukamin Ministan Tsaro, ya ce matsalolin ‘yan daba, ta’addanci da rigingimun kabilanci na ci gaba da zama babbar barazana ga kasa. Kwankwaso ya ce daya daga cikin manyan alamomin gazawar gwamnati shi ne yadda ake barin jihohi su kafa kungiyoyin tsaro na sa-kai ba tare da isasshen horo da tsari ba.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng