Sanata Barau Ya Sake Yi Wa NNPP Lahani, Hadimin Abba da Jigon Kwankwasiyya Sun Koma APC

Sanata Barau Ya Sake Yi Wa NNPP Lahani, Hadimin Abba da Jigon Kwankwasiyya Sun Koma APC

  • APC mai hamayya a jihar Kano ta sake samun karuwa bayan wasu jiga-jigai a NNPP sun sauya sheka daga jam'iyya mai mulki
  • Mataimakinn shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin ya tarbi masu sauya shekar da suka hada har da hadimin Gwamna
  • Sanata Barau ya taya su murnar sauya sheka zuwa APC tare da cika baki kan makomar jam'iyyar NNPP idan an buga gangar zabe

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Mataimakin shugaban majalisar Dattawan Najeriya, Sanata Barau Jibrin, ya karbi manyan ’ya’yan jam’iyyar NNPP/Kwankwasiyya guda biyu da suka sauya sheka zuwa jam’iyyar APC.

Masu sauya shekar sun hada da Hon. Umar Bala Haruna, mataimaki na musamman ga gwamnan jihar Kano a ofishin shugaban ma’aikatan na jiha, da kuma Hon. Muhammad Hussaini, sakataren tsare-tsare na NNPP a mazabar Bichi.

Kara karanta wannan

'Yan majalisa 6 da aka dakatar da su a Zamfara sun fice daga PDP, sun koma APC

Sanata Barau ya tarbi mambobin NNPP zuwa APC
Sanata Barau Jibrin a zauren majalisar dattawa Hoto: @barauijibrin
Source: Facebook

Jaridar The Nation ta ce hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai ba Sanata Barau shawara ta musamman kan harkokin yada labarai, Malam Ismail Mudashir, ya fitar.

'Yan NNPP sun koma jam'iyyar APC a Kano

Sanarwar ta ce manyan ’ya’yan NNPP/Kwankwasiyya din sun sanar da sauya shekar su zuwa APC ne yayin wata ziyara ta girmamawa da suka kai wa Sanata Barau a Abuja a kwanakin baya.

Hakazalika, sanarwar ta ce masu sauya shekar sun bayyana gamsuwarsu da nagartaccen jagoranci da manufofin da suka shafi jama’a kai tsaye na Sanata Barau, inda suka bayyana shi a matsayin abin koyi.

Barau Jibrin ya yi masu maraba a APC

Da yake mayar da martani, Sanata Barau ya yi maraba da su, yana mai cewa matakin da suka dauka alama ce ta karuwar amincewar ’yan Najeriya da gwamnatin APC karkashin Shugaba Bola Ahmed Tinubu..

Kara karanta wannan

Sanata Barau ya yi alhinin rasuwar 'yan majalisar dokoki 2 a jihar Kano

Sanata Barau ya ce kwanakin jam’iyyar NNPP sun kusa karewa a jihar Kano, duba da irin goyon bayan da jam’iyyar APC ke ci gaba da samu a jihar, rahoton jaridar Daily Trust ya tabbatar da hakan.

“Barka da zuwa jam’iyyar jama’a, APC. Kun shigo a lokacin da al’ummarmu ke ta tururuwa suna shiga tafiyarmu domin dawo da martabar Kano, inda gwamnati ke aiki domin kowa, ba don wasu tsiraru da iyalansu kadai ba, kamar yadda ake yi a yanzu."
"A karkashin kulawarmu, Insha Allah, Kano za ta farfado domin amfanin kowa."

- Sanata Barau Jibrin

Sanata Barau ya yi wa mambobin NNPP maraba zuwa APC
Sanata Barau Jibrin na jawabi a wajen wani taro Hoto: @barauijibrin
Source: Twitter

Hadimin Gwamna Abba ya ajiye aiki

Baya ga sauya shekarsa, Hon. Umar Bala Haruna ya kuma sanar da yin murabus daga mukaminsa na mataimaki na musamman ga gwamnan jihar Kano.

Ya ce ya dauki wannan mataki ne bisa ka’idojinsa na gaskiya, rikon amana da mutunta darajojin dimokuradiyya.

A cikin wasikar murabus da ya rubuta mai dauke da kwanan wata 22 ga Disamba, 2025, Umar Bala Haruna, wanda aka nada a watan Satumba na 2023, ya sanar da gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ta hannun sakataren gwamnatin jiha, kan kudirinsa na ajiye aiki.

Kara karanta wannan

Sanata ya hango abin da zai wargaza APC duk da yawan sauya shekar 'yan adawa

Sanata Barau ya taya Ganduje murna

A wani labarin kuma, kun ji cewa Barau Jibrin ya taya tsohon gwamnan Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje, murnar cikarsa shekaru 76 a duniya.

Ta bakin wani Mai magana da yawunsa, Mataimakin shugaban majalisar dattawan ya kwararo yabo ga tsohon shugaban na jam'iyyar APC.

Sanata Barau Jibrin Barau ya yabawa rawar da Ganduje ya taka a matsayin mataimakin gwamna, gwamna da shugaban APC wajen haɗa jam’iyya da samun nasarori.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng