Tinubu Ya Tuna Abota, Rikon Amanar Ganduje da Ya Cika Shekaru 76
- Shugaba Bola Tinubu ya taya tsohon shugaban jam'iyyar APC na kasa, Dr Abdullahi Umar Ganduje, murnar cikar sa shekaru 76
- Shugaba Tinubu ya bayyana Ganduje a matsayin gogaggen dan siyasa kuma jajirtaccen da ya ƙware a gudanar da mulki
- A jawabinsa, Shugaban Ƙasar ya yi addu’ar Allah Ya kara wa Abdullahi Ganduje lafiya da tsawon rai domin ci gaba da yi wa kasa hidima
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Shugaban kasa Bola Tinubu ya taya tsohon shugaban jam’iyyar APC na kasa, Dr Abdullahi Umar Ganduje, murnar cikar sa shekaru 76 da haihuwa, wanda ya yi ranar 25 ga Disamba, 2026.
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Bayo Onanuga, ya fitar, Tinubu ya bayyana Ganduje a matsayin hazikin dan siyasa kuma kwararren mai gudanar da mulki.

Source: Twitter
Jaridar The Nation ta wallafa cewa Bola Tinubu ya jinjina yadda Ganduje ya shafe kusan shekaru 50 yana hidima a mukamai daban-daban a Najeriya bisa kwarewa.
Bola Tinubu ya yabi Abdullahi Ganduje
Jaridar Leadership ta ruwaito Shugaba Tinubu ya jaddada cewa Ganduje ya taka muhimmiyar rawa a fannoni da dama na gwamnati tun daga matakin tarayya har zuwa jiha.
Ya tunatar da cewa Ganduje ya taba aiki a matsayin babban jami’i a Babban Birnin Tarayya, Abuja, inda ya samu kwarewa a harkokin gudanarwa da tafiyar da jama'a.
Daga bisani, a lokacin mulkin soja, aka dawo da Ganduje gida Kano inda ya rike mukamin kwamishinan ayyuka.
A cewar Shugaba Bola inubu, ya samu damar taimakawa wajen shimfida muhimman ayyukan raya kasa a jiharsa.
Ganduje ya kuma zama mataimakin gwamnan jihar Kano na tsawon wa’adi biyu, kafin daga bisani al’ummar jihar su zabe shi gwamna har sau biyu a jere.
Jama'a sun yadda da Ganduje - Tinubu
Tinubu ya ce waɗannan nasarorin Abdullahi Umar Ganduje ya rika samun sun nuna irin amincewar da jama’a suka yi da salon jagorancinsa.
Shugaban Kasan ya kuma yi tsokaci kan rawar da Ganduje ya taka a jam’iyyar APC, musamman a matsayin shugaban jam’iyyar na kasa.
Tinubu ya ce zai ci gaba da godiya ga abota da hadin gwiwar da ke tsakaninsa da Ganduje a lokuta daban-daban, tare da yabawa gudummawar da ya bayar wajen karfafa jam’iyyar.
A halin yanzu, Ganduje na rike da Majalisar da ke kula da harkokin Hukumar Kula da Harkokin Sufurin Jiragen Sama ta Kasa (FAAN).
Tinubu ya kammala sakonsa da addu’a, yana rokon Allah Madaukakin Sarki Ya kara wa Ganduje lafiya, tsawon rai da hikima, domin ya ci gaba da yi wa Najeriya da al’umma hidima.
Ganduje ya fusata gwamnatin Kano
A baya, kun ji gwamnatin jihar Kano karkashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf ta sake daukar mataki kan tsohon shugaban jam’iyyar APC na kasa kuma tsohon Abdullahi Umar Ganduje.
Gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta fusata ne bayan ta zargi Ganduje da yin kalaman da ka iya tayar da hankalin jama’a da kuma dagula kokarin tabbatar da tsaro a fadin jihar.
Rahotanni sun nuna cewa gwamnatin ta bukaci hukumomin tsaro su kama tare da binciken Ganduje, domin gano sahihancin zargin da ake masa da wanzar da zaman lafiya a Kano.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


