Kano: Barau Ya Zargi Abba da Take Hakkin Alfindiki, Ya ba Shi Kudin da Aka Hana Shi

Kano: Barau Ya Zargi Abba da Take Hakkin Alfindiki, Ya ba Shi Kudin da Aka Hana Shi

  • Sanata Barau Jibrin ya mika Naira miliyan 7 ga tsohon shugaban karamar hukuma a jihar Kano, Fa’izu Alfindiki yayin da ya ziyarce shi a Abuja
  • Mataimakin shugaban majalisar dattawan ya ce an riƙe kudin ne tsawon lokaci saboda tsayuwarsa kan gaskiya da goyon bayan jam’iyyar APC
  • Duk da gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta biya hakkin tsofaffin shugabannin kananan hukumomin Kano, ana zargin ba a biya Alfindiki kudinsa ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin, ya mika kudi Naira miliyan 7 ga tsohon shugaban karamar hukumar Birni, Hon. Fa’izu Alfindiki, a matsayin haƙƙinsa da gwamnatin jihar Kano ta riƙe.

An mika kudin ne a ofishin Sanata Barau da ke Majalisar Tarayya a Abuja, a gaban wasu manyan masu ruwa da tsaki daga jihar Kano, lamarin da ya jawo hankalin ’yan siyasa da masu bibiyar al’amura.

Kara karanta wannan

An saka ranar da Trump zai hana 'yan Najeriya shiga kasar Amurka

Sanata Barau Jibrin tare da Fai'izu Alfikindi
Sanata Barau Jibrin bayan ba Fai'izu Alfikindi kudi. Hoto: Barau I. Jibrin
Source: Facebook

Barau ya ce an danne hakkin Alfindiki

Sanata Barau ya wallafa a Facebook cewa an hana Fa’izu Alfindiki wannan haƙƙi ne da gangan, ba don wani laifi ba, sai don tsayuwarsa kan gaskiya da kuma kare muradin talakawan da ya ke wakilta a lokacin da yake rike da mukami.

A cewar Sanata Barau, abin takaici ne matuƙa yadda aka tauye haƙƙin Fa’izu Alfindiki saboda tsayuwarsa da jam’iyyar APC da kuma al’ummar jihar Kano.

Sanatan ya ce irin wannan mataki zalunci ne karara, kuma barazana ce ga dimokuraɗiyya da ’yancin fadin albarkacin baki.

Ya jaddada cewa tauye dan kasa saboda ra’ayinsa na siyasa ko jam’iyyar da ya zaba abu ne da bai dace ba, kuma hakan na iya raunana tsarin mulkin dimokuraɗiyya idan aka bar shi ya yi tafi.

Sanata Barau ya ce siyasa mai ma’ana, irin wadda Fa’izu Alfindiki ke yi, ita ce ginshiƙin ci gaban kasa, domin tana gina adalci da tsare muradin talakawa, ba tare da la’akari da tsoro ko matsin lamba ba.

Kara karanta wannan

Rundunar sojojin sama ta biya diyya ga iyalan bayin Allah da ta kashe a Sokoto

Barau Jibrin da Fai'zu Alfikindi
Sanata Barau Jibrin yayin ba Fa'izu Alfikindi kudi. Hoto: Barau I. Jibrin
Source: Facebook

Barau ya kara da cewa wajibi ne shugabanni su rika kare irin wadannan mutane masu tsayawa kan gaskiya, domin su ne ke ba dimokuraɗiyya karfi da armashi.

A baya an ji labari gwamnatin NNPP ta biya hakkokin tsofaffin shugabannin kananan hukumomi da kansilolin da suka yi aiki a gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje.

Duk da haka, ana zargin tsohon shugaban na karamar hukumar Birni a Kano bai samu komai ba.

Jawabin Hon. Alfindiki bayan karɓar kudin

Da yake jawabi bayan karɓar kuɗin, Fa’izu Alfindiki ya bayyana jin dadinsa da godiya ga Sanata Barau Jibrin, inda ya ce wannan mataki ya sake tabbatar masa da cewa APC jam’iyya ce da ta dace a tsaya da ita.

Ya ce tun bayan faruwar lamarin, yana da cikakken tabbacin cewa jam’iyyar APC ba za ta yi watsi da shi ba, duk da kalubalen da ya fuskanta saboda ra’ayinsa da tsayuwarsa kan gaskiya.

Kara karanta wannan

Tinubu ta nuna alhini bayan mutuwar tsohon mataimakin shugaban kasa

Alfindiki wanda ya taba zama hadimi a majalisa yana cikin wadanda suke yakar gwamnatin NNPP a Kano, ya bar ofishin ciyaman ne a shekarar 2024.

Kwankwaso ya yaba wa Abba Kabir Yusuf

A wani labarin, mun kawo muku cewa Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya yaba wa gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf.

A bayanin da ya yi, Kwankwaso ya ce Kano na kara samun cigaba a karkashin jagoranci da gwamnan ke yi a jihar.

Sanata Kwankwaso ya yi jawabin ne a wani taro da ya yi da masu ruwa da tsaki na jam'iyyar NNPP a birnin Abuja.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng