"Zan Doke Gwamna Alia," An Samu Wani Farfesa da Zai Shiga Takarar Gwamnan Benue

"Zan Doke Gwamna Alia," An Samu Wani Farfesa da Zai Shiga Takarar Gwamnan Benue

  • Farfesa Sebastine Hon ya bayyana aniyarsa ta ƙalubalantar Gwamna Hyacinth Alia a 2027, yana mai cewa takararsa kira ne daga Ubangiji
  • Ya bayyana cewa shiyyoyin A da B sun kwashe shekaru masu yawa a kan mulki, yana mai nuna rashin daidaiton tsarin karba-karba a Benue
  • Masu ruwa da tsaki a yankin Gboko sun amince cewa ya kamata kowane ƙwararren ɗan takara ya fito neman gwamna a zaɓen shekarar 2027

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Benue - Babban lauya kuma farfesan shari’a, Sebastine Hon (SAN), ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar gwamnan Benue a zaɓen shekarar 2027.

Farfesan shari'ar, ya ce babban burinsa shi ne ya karbe kujerar lamba daya na jihar Benue daga hannun Gwamna Hyacinth Alia, mai ci yanzu.

Farfesa Sebastine Hon ya ayyana kudurinsa na fitowa takarar gwamnan Benue.
Farfesa Sebastine Hon, SAN, wanda ya nuna aniyar kwace mulki daga Gwamna Alia a 2027. Hoto: Sebastine Hon
Source: Facebook

Benue: Farfesa zai fito takarar gwamna

Kara karanta wannan

Abba Gida Gida ya ba wa gwamnonin Arewa mafita game da matsalar tsaro

Sebastine Hon ya bayyana wannan babban buri nasa ne a yammacin ranar Litinin yayin wasu jerin ziyarar tuntubar jama'a da ya kai wa dangin mahaifiyarsa a mazaɓun Mbayion da Mbatiav da ke ƙaramar hukumar Gboko a jihar Benue, in ji rahoton Punch.

Farfesan ya bayyana cewa waɗannan ziyarce-ziyarce na tuntubar mutane ne kawai kuma sun dace da tanadin dokokin zaɓe na ƙasa.

Ya ce yana sane da cewa har yanzu hukumar zaɓe mai zaman kanta (INEC) ba ta ɗage takunkumin yin yakin neman zaɓe ba.

An gudanar da waɗannan tarukan ne a garuruwan Ihungwanor da Akapher, inda fitaccen lauyan ya shaida wa al'ummar cewa shawarar da ya yanke ta neman takarar gwamna wahayi ne daga Ubangiji, kuma yana da cikakken kwarin gwiwar samun nasara a zaɓen 2027.

Rigima kan tsarin karba-karbar mulki

Yayin da yake martani kan maganar tsarin karba-karbar shugananci, Sebastine Hon ya bayyana cewa an daɗe ana aiwatar da tsarin ta hanyar da ba ta dace ba a jihar.

Ya nuna cewa idan aka duba tarihin siyasar Benue, za a ga akwai rashin daidaito a raba madafun iko tsakanin shiyyoyi daban-daban.

Ya kawo misalin cewa shiyyar A, ta hanyar tsofaffin gwamnoni kamar Aper Aku, Moses Orshio Adasu, da Gabriel Suswam, ta mulki jihar na tsawon shekaru 18 da kwanaki 17, yayin da ake sa ran Gwamna Alia ma zai kammala shekaru huɗu.

Kara karanta wannan

N58.47tn: Majalisa ta fara tafka muhawara kan kasafin 2026 da Tinubu ya gabatar

Haka zalika, ya ƙara da cewa shiyyar B, wadda George Akume da Samuel Ortom suka wakilta, ta mulki jihar na tsawon shekaru 16, in ji rahoton Business Day.

Farfesa Hon. ya kalubalanci tsarin karba karbar mulki na jihar Benue.
Taswirar jihar Benue, inda wani farfesa ya nuna sha'awar yin takarar gwamna. Hoto: Legit.ng
Source: Original

Farfesa ya fara samun kwarin gwiwar takara

Farfesan ya jaddada cewa matakan baya-bayan nan da Gwamna Alia ya ɗauka kan naɗe-naɗen muƙamai sun ƙara raunana darajar tsarin karba-karba a jihar.

A taron, manyan masu ruwa da tsaki kamar tsohon kakakin majalisar jihar, Aondona Dajo, sun goyi bayan cewa ya kamata a bar kowane ƙwararren ɗan takara ya fito takara a 2027 ba tare da la'akari da shiyya ba.

Daga ƙarshe, Farfesa Sebastine Hon (SAN) ya ziyarci Majalisar sarakunan Mbatiav a Akapher don neman albarkacin iyayen kasa kan wannan kuduri nasa.

'Zan shiga takarar gwamna' - Malami

A wani labari, mun ruwaito cewa, tsohon babban lauyan Najeriya, Abubakar Malami, SAN, ya tabbatar da cewa zai shiga tseren gwamnan Jihar Kebbi a 2027.

Ya bayyana cewa kiraye kirayen da jama'a suka dade suna yi ne ya amsa kiransu yanzu, duk da cewa lokacin fara gangamin siyasa bai yi ba a halin yanzu.

Malami ya tabbatar da cewa ya yanke shawara fitowa neman kujerar gwamna a 2027, kuma babu abin da zai sanya ya ja da baya a kan kudurinsa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com