"Na Cancanci Zama Shugaban Najeriya," Gwamna Ya Yi Magana kan Yin Takara a 2027

"Na Cancanci Zama Shugaban Najeriya," Gwamna Ya Yi Magana kan Yin Takara a 2027

  • Gwamna Seyi Makinde ya ce gogewarsa a matsayin gwamna da kuma ƙwarewarsa a aikin injiniya sun sa ya dace da shugabancin Najeriya
  • Makinde ya soki yawaitar sauya sheƙa zuwa APC, yana cewa hakan na barazana ga dimokuraɗiyya da drukusa adawa a ƙasar
  • Gwamnan ya bayyana cewa ba zai mara wa Shugaba Bola Tinubu baya a 2027 ba, yana mai cewa zai mayar da hankali kan ƙarfafa PDP

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Oyo - Yayin da rahotanni ke ƙara bayyana kan aniyarsa ta tsayawa takarar shugabancin Najeriya, gwamnan Oyo, Seyi Makinde, ya ce yana da dukkan abin da ake bukata na jagorantar ƙasar.

Makinde ya bayyana hakan ne yayin da yake amsa tambayoyi daga wasu ‘yan jarida a wata tattaunawa da aka yi da shi a Ibadan, babban birnin jihar Oyo, ranar Talata.

Kara karanta wannan

Tinubu ya tura tawaga Morocco yayin da Najeriya za ta fafata da Tanzania a AFCON 2025

Gwamnan Oyo ya jaddada kudurinsa na son zama shugaban Najeriya.
Gwamna Seyi Makinde ya na magana a wani taro da aka shirya a jihar Oyo. Hoto: @seyiamakinde
Source: Facebook

"Na cancanci shugabantar Najeriya" - Gwamna

Gwamnan ya jingina wannan ikirari nasa da gogewarsa wajen jagorantar jihar Oyo da kuma tarihin aikinsa a fannin injiniyanci, a cewar rahoton Channels TV.

“Bari in bayyana wannan a fili: domin yin hidima wa wannan ƙasa a matakin ƙoli, ina cancanta — kai har ma na wuce cancantar da ake bukata,” in ji Makinde.

Ya ƙara da cewa:

“Na shugabanci jihar Oyo, shi ma shugaban ƙasa na yanzu — da ya ya samu wannan matsayi? Saboda ya yi gwamna na wa’adi biyu a jihar Lagos. Da yardar Ubangiji, zuwa ƙarshen Mayun 2027, zan kammala wa’adi na na biyu a matsayin gwamnan jihar Oyo.”

Makinde ya ce tun yana matashi ya riga ya kafa kamfani yana tafiyar da shi, yana mai jaddada cewa ya fara shugabanci tun yana da shekara 29, lokacin da wasu abokansa ke ci gaba da bautar ƙasa.

Makinde ya yi magana kan goyon bayan Tinubu

Kara karanta wannan

Wani uba ya ga ta kansa a Kano, yaran da ya haifa sun kai shi kotu kan dukiyarsa

Gwamnan jihar ya kuma ce:

“Ban je NNPC ko makamantansu ba. Ina aiki ne da manyan kamfanonin mai na ƙasashen waje irin su Shell, ExxonMobil da Chevron."

Duk da haka, gwamnan ya ce har yanzu lokaci bai yi ba na fara tattaunawa kan takarar shugabancin ƙasa, ganin cewa akwai fiye da shekara guda kafin zaɓe.

Makinde ya ce ‘yan Najeriya na buƙatar dimokuraɗiyya mai ƙarfi tare da jam’iyyun adawa masu ƙarfi. Ya soki sauya sheƙar gwamnoni da manyan ‘yan siyasa zuwa jam’iyyar APC mai mulki, yana cewa hakan ba alheri ba ne ga ƙasar.

Gwamnan, wanda ke wa’adi na biyu kuma na ƙarshe a ƙarƙashin jam’iyyar PDP, ya tunatar da jama’a cewa ya dawo daga rakiyar Shugaba Bola Tinubu, kuma ba zai mara masa baya a zaɓen 2027 ba.

Gwamna Seyi Makinde ya ce ba zai sake mara wa Shugaba Bola Tinubu baya a zaben shugaban kasa ba.
Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde ya halarci wani taro da aka shirya a Ibadan. Hoto: @seyiamakinde
Source: Facebook

Gwamna ya fallasa wani asirin Wike

Gwamna Makinde ya ce ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike, wanda suka taɓa kasancewa abokan tafiya a siyasa, na iya mara wa Tinubu baya idan yana so.

Kara karanta wannan

Gwamnan da ke takun saka da Wike a PDP ya sha alwashin abin da zai yi kafin zaben 2027

“Na kasance a wani taro tare da Shugaba Tinubu, Nyesom Wike da wasu, inda Wike ya ce zai juya PDP domin Tinubu ya samu nasara a 2027, maganar ta ba ni mamaki matuƙa,” in ji Makinde.

A cewarsa, babban abin da ya fi mayar da muhimmanci a kansa a yanzu shi ne cetos jam’iyyar PDP, wadda ke fuskantar koma baya sakamakon sauya sheƙar mambobinta da dama, ciki har da gwamnoni da ‘yan majalisa.

Makinde ya watsawa Tinubu kasa a ido

A wani labari, mun ruwaito cewa, gwamnan Oyo, Seyi Makinde, ya tuna baya kan wata alfarma da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya nema a wajensa.

Gwamna Makinde ya ce ya ki amincewa da bukatar Tinubu ta ya taimaka wajen hada kan jam’iyyar APC a jihar Oyo, yana mai nuna amincinsa ga PDP.

Gwamnan jihar na Oyo ya bayyana cewa bai amince da bukatar da shugaban kasar ya gabatar masa ba saboda shi dan jam'iyyar PDP ne na hakika.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com