Bayan Ƴan Majalisar Wakilai 6, Sanatoci 2 Masu Biyayya ga Wike Sun Fice daga PDP
- Sanatoci biyu daga Rivers da ‘yan majalisar wakilai shida sun sauya sheƙa daga jam'iyyar PDP zuwa APC, saboda rikicin cikin gida
- Sauya shekar ta ƙara wa APC rinjaye a majalisar dattawa zuwa sanatoci 78, abin da ke ba jam’iyyar ƙarfi a harkokin majalisar tarayya
- Shugabannin majalisa sun ce dimokuraɗiyya na samun ci gaba, tare da ƙaryata zargin ana son mayar da ƙasar karkashin jam’iyya ɗaya
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Yanayin siyasar jihar Rivers ya ɗauki sabon salo bayan da sanatoci biyu da ‘yan majalisar wakilai shida suka fice daga jam’iyyar PDP zuwa jam’iyyar APC.
Wannan sauyin sheƙar, wanda aka sanar a hukumance a ranar Talata yayin zaman majalisun dokokin kasar, ya sake nuna girman rikicin cikin gida da ke addabar PDP a Rivers.

Source: Twitter
Sanatoci 2 sun bar PDP zuwa jam'iyyar APC
Sanatocin da suka sauya sheƙar sun haɗa da Sanata Allwell Onyesoh, mai wakiltar Rivers ta Gabas, da Sanata Barinada Mpigi, mai wakiltar Rivers ta Kudu maso Gabas, in ji rahoton Channels TV.
Ana ɗaukar dukkansu a matsayin amintattu kuma na hannun daman Ministan Babban Birnin Tarayya kuma tsohon gwamnan Rivers, Nyesom Wike.
An sanar da ficewar sanatocin ne yayin zaman majalisar dattawa, inda aka dakatar da wasu dokokin majalisa domin ba sakataren jam’iyyar APC na ƙasa, Ajibola Basiru, da sauran shugabannin jam’iyyar damar shiga zauren majalisar domin shaida sauyin sheƙar.
Dalilin sauya shekar sanatocin
A cewar sanatocin, sun yanke shawarar sauya shekar ne saboda “cigaban rikice-rikicen cikin gida” da kuma rashin warware matsalolin da ke addabar PDP.
Sun bayyana cewa yanayin jam’iyyar PDP ya hana su ci gaba da aiki yadda ya kamata domin wakiltar al’ummar da suka zabe su.

Kara karanta wannan
Tinubu ya tura tawaga Morocco yayin da Najeriya za ta fafata da Tanzania a AFCON 2025
Da wannan sauya sheka, jam’iyyar APC ta ƙara ƙarfafa rinjayenta a majalisar dattawa, inda yanzu take da sanatoci 78, abin da ke ba ta rinjaye mai yawa wajen yanke manyan shawarwari na ƙasa.
Martanin shugabannin majalisar dattawa
Duk da ƙorafe-ƙorafen da ake yi cewa yawaitar sauya sheƙa zuwa APC na iya jefa Najeriya cikin tsarin jam’iyya ɗaya, shugabannin majalisar dattawa sun musanta hakan.

Source: Facebook
Shugaban masu rinjaye a majalisar dattawa, Opeyemi Bamidele, ya ce dimokuraɗiyya na ci gaba da bunƙasa a ƙasar Najeriya, in ji rahoton Leadership.
A cewarsa, APC jam’iyya ce mai alhakin kare dimokuraɗiyya, kuma tana shirye-shiryen yin aiki tare da ‘yan adawa domin amfanin ƙasa baki ɗaya.
Sanata Opeyemi Bamidele ya ƙara da cewa jam’iyyar APC na da burin inganta tsaron abinci, kula da lafiya da jin daɗin al’umma.
Shi ma shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, ya yi tsokaci kan sauya shekar, inda ya jaddada muhimmancin adalci da dimokuraɗiyya cikin APC.
‘Yan majalisar wakilai 6 sun koma APC
A wani labarin, mun ruwaito cewa 'yan majalisar wakilai shida daga Rivers, wadanda suke goyon bayan Nyesom Wike sun bar PDP zuwa APC.

Kara karanta wannan
'Yan majalisar tarayya 6 sun gaji da zama a PDP, sun sauya sheka zuwa jam'iyyar APC
'Yan majalisar da suka sauya sheka sun hada da Dumnamere Robinson Dekor, Solomon Bob, Hart Cyril, Victor Obuzor, Blessing Amadi da Felix Nweke
Wannan sauya sheƙar ya ƙara raunana jam'iyyar PDP a jihar Rivers, tare da nuna irin tasirin da rikicin cikin gida ke da shi a siyasar jam’iyyun adawa a kasar.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
