Tura Ta Kai Bango: Gwamna Ya Yi Nadamar Marawa Tinubu Baya a 2023
- Gwamnan Oyo, Seyi Makinde, ya bayyana nadamar goyon bayan Bola Tinubu a zaben 2023 da suka yi da wasu gwamnoni
- Makinde ya ce ya mara wa Tinubu baya ne da fatan zai yi abin da ya dace ga kasa, ya hada kwararru domin gyara Najeriya
- Ya jaddada cewa Tinubu ba zai samu goyon bayansa a 2027 ba, yana kuma bayyana rikicinsa da Nyesom Wike
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Ibadan, Oyo - Gwamnan Jihar Oyo, Seyi Makinde ya bayyana abubuwan da suka faru bayan marawa Bola Tinubu baya a zaben 2027.
Makinde ya ce yana nadamar goyon bayan Shugaba Bola Tinubu a zaben shugaban kasa, yana mai cewa bai samu sakamakon da yake fata ba.

Source: Facebook
Makinde ya bayyana hakan ne yayin wata ganawa da manema labarai a fadar gwamnati da ke Ibadan, babban birnin Jihar Oyo, cewar Vanguard.
Gwamnonin PDP da suka goyi bayan Tinubu
Gwamnan na daga cikin gwamnonin PDP guda biyar da ake kira G5, wadanda suka yi aiki a bayyane da gujewa takarar Atiku Abubakar a zaben 2023.
Kungiyar G5, karkashin jagorancin tsohon gwamnan Rivers, Nyesom Wike, ta nuna adawa da takarar Atiku bisa tsarin karba-karba na yankuna.
Sun ba da hujjar cewa bayan shekaru takwas na mulkin Muhammadu Buhari daga Arewa, ya dace PDP ta tsayar da dan takara daga Kudancin Najeriya.
Nadamar da Makinde ya yi game da bin Tinubu
Makinde ya ce ya goyi bayan Tinubu ne saboda ya yi imanin cewa zai yi aiki bisa muradin kasa idan aka zabe shi shugaban kasa.
Ya ce:
“Na fada a baya, ni mutum ne, na goyi bayan shugaban kasa na yanzu duk da yana wata jam’iyya, saboda na yi tunanin zai yi abin da ya dace.”

Source: Facebook
Makinde ya soki salon mulkin Tinubu
Gwamnan ya kara da cewa ya yi imanin Tinubu zai “sake fasalin kasa” tare da hada kwararru daga sassan Najeriya domin magance matsaloli.
Amma ya ce abin takaici, abin da suke gani a yanzu bai dace da wannan fata ba, yana mai cewa yana nadamar wannan mataki da ya dauka, cewar rahoton The Guardian.
“Abin takaici, ba wannan muke gani ba. Ina nadamar wannan mataki. Hakika, na yi nadama."
In ji Makinde.
Bisa damuwa da makomar dimokuradiyya da jam’iyyar PDP, Makinde ya ce Tinubu ba zai samu goyon bayansa a zaben 2027 ba.
Ya kuma bayyana dalilin rikicinsa da Ministan Abuja, Nyesom Wike, Makinde ya ce ya samo asali ne daga wata ganawa da Tinubu.
Makinde ya ce Wike ya fada wa Tinubu cewa zai “rike PDP” domin shugaban kasa a zaben 2027 ba tare da amincewar sauran jiga-jigan jam’iyya ba.
Ya ce:
“Mun kasance a wani taro da shugaban kasa, sai Wike ya ce zai rike PDP ga Tinubu a 2027, sai na tambaye shi ko mun amince da hakan.”
'Zan yi zaben ciyamomi kafin 2027' - Makinde
An ji cewa Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde bayyana shirin da yake da shi na gudanar da zabe a fadin jihar kafin ya bar mulki a 2027.
Makinde ya rantsar da mambobin hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar Oyo (OYSIEC) domin inganta harkokin zaɓe.
Gwamna Makinde ya bukace su da su gudanar da ayyukansu cikin gaskiya da rikon amana domin ci gaban jihar.
Asali: Legit.ng


