Abubuwan Sun Kara Dagulewa a PDP, Sule Lamido Ya Yi Barazanar Ficewa daga Jam'iyyar

Abubuwan Sun Kara Dagulewa a PDP, Sule Lamido Ya Yi Barazanar Ficewa daga Jam'iyyar

  • Tsohon gwamnan Jigawa, Sule Lamido ya bayyana cewa da yiwuwar ya tattara kayansa ya bar jam'iyyar PDP kafin zaben 2027
  • Lamido ya ce matukar abubuwa suka ci gaba da tafiya a haka, aka gaza samo mafita a rikicin PDP, babu shakka zai nemi jam'iyyar da ta dace da shi
  • Ya nuna takaicinsa matuƙa kan abin da ya kira ƙoƙari da gangan da wasu mutane ke yi domin lalata tare da ruguza PDP gaba daya

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jigawa, Nigeria - Babbar jam'iyyar adawa ta kasa watau PDP na iya rasa daya daga cikin manyan jiga-jiganta, wanda da shi aka kafa ta a 1998, Sule Lamido.

Sule Lamido, tsohon gwamnan jihar Jigawa ya ce da yiwuwar ya bar jam'iyyar PDP idan har ba a samu mafita ga rikicin cikin gida da ke addabar jam’iyyar ba.

Kara karanta wannan

2027: Kawu Sumaila ya fadi zabinsa daga cikin masu son takarar gwamna a Kano

Tsohon gwamnan Jigawa.
Tsohon gwamnan jihar Jigawa kuma babban kusa a PDP, Sule Lamido Hoto: Sule Lamido
Source: Facebook

Rahoton Vanguard ya nuna cewa Lamido, wanda yana daga cikin manyan jiga-jigan adawa a Najeriya, ya ce halin da PDP ke ciki a yanzu yana da matuƙar tayar da hankali.

Sule Lamido ya yi barazanar barin PDP

Tsohon gwamnan ya yi gargadin cewa idan ba a dauki matakin gaggawa na shawo kan rikicin PDP ba, hakan zai iya tilasta masa yin wani sabon zaɓi na siyasa.

Sule Lamido ya bayyana haka ne yayin wata hira da ya yi da BBC Hausa a ranar Talata, 23 ga watan Disamba, 2025.

Ya nuna takaicinsa matuƙa kan abin da ya kira ƙoƙari da gangan da wasu mutane ke yi domin lalata PDP.

A cewarsa, wasu bara gurbin 'yan siyasa sun kudiri aniyar yin aiki ba dom komai ba sai domin raunana jam’iyyar har ta kai ga rugujewa gaba ɗaya.

Abin da zai Sule Lamido ya canza jam'iyya

Kara karanta wannan

Ana wata ga wata: An cire Sule Lamido daga kwamitin amintattu na jam'iyyar PDP

Tsohon gwamnan ya ce rashin iya shawo kan rikicin da ke tsakanin shugabannin jam’iyyar da bangarori daban-daban na PDP na iya sa shi sake duba makomarsa ta siyasa.

Ya jaddada cewa idan har abubuwa suka ci gaba da tafiya ba bisa ka’ida ba, bai da wata mafita face nemo wata jam’iyya daban da za ta dace da ra’ayinsa da manufofinsa.

“Zan fara kallon Najeriya, sannan na duba jiha ta Jigawa, sannan na tantance abin nake ganin ya fi dacewa, mu kulla yarjejeniya. Amma kawance kurum zan kulla da duk jam'iyyar da na zaba."
"A yanzu ba zance ga jam'iyyar da zan koma ba domin muna da jam'iyyu daban-daban a Najeriya. Zan tantance wacce ta dace da ni mu kulla kawance," in ji Lamido.
Jam'iyyar PDP.
Tutar babbar jam'iyyar adawa ta kasa, PDP Hoto: PDP Nigeria
Source: Facebook

Ya tuna cewa PDP a da jam’iyya ce da ta haɗa kan ‘yan Najeriya daga kowane yanki da addini, amma a yanzu ta fada cikin rikice-rikicen cikin gida, rarrabuwar kai da rashin tsari.

Maganganun Lamido sun ƙara tayar da ƙura game da makomar PDP, musamman ganin cewa yana daga cikin tsofaffin jiga-jigan da suka taka rawa sosai wajen kafa da gina jam’iyyar tun daga farko.

Kara karanta wannan

APC ta yi babban rashi, jigonta kuma tsohon kwamishina yar bar duniya

Sule Lamido ya ba PDP wa'adin kwanaki 10

A wani labarin, kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido, ya koka kan rikicin da ya dade yana addabar babbar jam'iyyar hamayya ta PDP.

Sule Lamido ya ba shugabannin PDP na kasa wa’adin kwana 10 su magance matsalolin cikin gida da ya ce suna ta kara ta’azzara a jam’iyyar.

Ya kuma yi kira da a soke babban taron PDP ya gudana a Ibadan, babban birnin jihar Oyo kwanakin baya, ya na mai cewa bai cika dokoki ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262