'Yan Majalisar Tarayya 6 Sun Gaji da Zama a PDP, Sun Sauya Sheka zuwa Jam'iyyar APC
- Wasu 'yan majalisar wakilai shida daga jihar Rivers sun sanar da ficewarsu daga jam'iyyar PDP zuwa APC a zauren majalisar da ke Abuja
- Sauya shekar ta biyo bayan ficewar Gwamna Siminalyi Fubara daga PDP zuwa APC, a wani mataki na hada kai da gwamnatin tarayya
- A halin da ake ciki, 'yan majalisar wakilai uku daga jihar Rivers ne kawai suka yi saura a PDP, inda dukkan sauran suka koma cikin APC
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Jam’iyyar PDP ta sake fuskantar koma baya a Majalisar Wakilai bayan ‘yan majalisa shida daga jihar Rivers sun sauya sheka zuwa jam’iyyar APC mai mulki a kasa.
‘Yan majalisar da suka fice daga PDP sun aika takardun murabus din nasu daban daban ga shugaban majalisar wakilai, Abbas Tajudeen.

Source: Twitter
'Yan majalisar Rivers sun bar PDP zuwa APC
Jaridar The Cable ta rahoto 'yan majalisar wakilan da suka sauya sheka sun hada da Dumnamere Dekor, Solomon Bob, Hart Cyril, Victor Obuzor, Blessing Amadi, da Felix Nweke.
Sun kasance suna wakiltar mazabun Khana/Gokana, Abua/Odual da Ahoada ta Gabas, Degema/Bonny, Ahoada ta Yamma/Ogba-Egbema/Ndoni, Port Harcourt II da Eleme/Oyigbo/Tai.
Sauya shekar ‘yan majalisar ta biyo bayan ficewar gwamnan Rivers, Siminalyi Fubara, wanda ya koma APC a ranar 5 ga Disamba, 2025, kamar yadda Legit Hausa ta ruwaito.
Kafin ficewar gwamnan, ‘yan majalisar dokokin jihar Rivers 15, ciki har da kakakin majalisar, Martin Amaewhule, sun riga sun sauya sheka daga PDP zuwa APC.
An karanta wasikar 'yan majalisar Rivers
Kakakin majalisar sakilai, Abbas Tajudeen, ne ya karanta wasikun ficewar ‘yan majalisar a yayin zaman majalisar na ranar Talata, 23 ga watan Disamba, 2025.
Manyan shugabannin APC na kasa sun halarci bikin ficewar, ciki har da Victor Gaidam, Felix Morka, Dayo Israel, da Ajibola Basiru.
Bayan karanta wasikun, Abbas ya gayyaci ‘yan majalisar zuwa gaban zauren domin daukar hotuna na maraba da shigarsu jam'iyya mai mulki.
Korafe-korafe daga ‘yan adawa
Sai dai ficewar ta haifar da cece-kuce a zauren majalisa. Ali Isa ya yi adawa da matakin, inda ya bukaci kakakin majalisar da ya ayyana kujerunsu a matsayin babu kowa a kansu.

Source: Twitter
Haka kuma, jagoran ‘yan adawa, Kingsley Chinda, ya nuna rashin jin dadinsa da yadda aka gudanar da bikin ficewar, yana mai cewa babu wata doka da ta tanadi sanar da sauya sheka a zauren majalisa.
“Ku je mazabunku ku sanar da sauya shekarku mana,” in ji Chinda.
Sai dai Abbas bai yanke hukunci kan korafe-korafen ba, yana mai cewa majalisar za ta duba batun, a cewar rahoton Punch.
Da wannan sabon sauya shekar, PDP na da ‘yan majalisa uku kacal daga jihar Rivers a majalisar wakilai: Kingsley Chinda, Kenneth Chikere, da Kelechi Nwogu.
'Yan majalisar Rivers 4 sun koma APC
Tun da fari, mun ruwaito cewa, 'yan majalisar wakilai hudu daga Rivers sun fice daga PDP zuwa APC, a wani mataki na biyayya ga Gwamna Simi Fubara.
Wadanda suka sauya sheka sune ke wakiltar mazabun Port Harcourt 1, Ikwerre/Emuoha, Andoni/Opobo da Asari-Toru a majalisar wakilan tarayya.
Ficewar ‘yan majalisar wakilai hudun ya zo ne kwanaki kadan bayan kakakin majalisar Rivers, Martin Amaewhule, da ‘yan majalisa 16 sun koma APC.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


