Gwamnan da Ke Takun Saka da Wike a PDP, Ya Sha Alwashin Abin da Zai Yi kafin Zaben 2027
- Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, ya rantsar da mambobin hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar Oyo (OYSIEC)
- Injiniya Seyi Makinde ya bukace su da su gudanar da ayyukansu cikin gaskiya da rikon amana domin ci gaban jihar
- Gwamnan ya kuma bayyana shirin da yake da shi na gudanar da zabe a fadin jihar kafin ya bar mulki a shekarar 2027
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Oyo - Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, ya bayyana shirin da ya ke da shi kafin ya bar kujerar mulki.
Gwamna Makinde ya bayyana cewa gwamnatinsa za ta gudanar da zaɓen kananan hukumomi kafin ya bar ofis a shekarar 2027.

Source: Facebook
Jaridar Leadership ta ce Gwamna Makinde ya bayyana hakan ne a ranar Litinin, 22 ga watan Disamban 2025 yayin rantsar da mambobin hukumar zaɓe mai zaman kanta ta jihar Oyo (OYSIEC).
Gwamna Makinde ya rantsar da mambobin OYSIEC
Gwamna Makinde ya rantsar da mambobin ne a zauren majalisar zartarwa na ofishin gwamna da ke sakatariyar gwamnati a birnin Ibadan.
Ya ce jam’iyyarsu ta PDP mai adawa a Najeriya ba ta jin tsoron jam’iyyun adawa da ake da su a jihar Oyo.
A cewarsa, wa’adin shugabannin kananan hukumomi 33 da ke jihar zai ƙare ne a watan Mayun 2027, jaridar The Guardian ta kawo rahoton.
Gwamnan, wanda ya bayyana cewa mambobin sabuwar OYSIEC mutane ne masu nagarta da amana, ya bukace su da su kasance masu gaskiya da adalci a aikin da ke gabansu domin ciyar da jihar gaba.
Mambobin OYSIEC sun haɗa da Adebiyi Babatunde (Shugaba), Olatunde Theophilus, Cif Kunmi Agboola, da Sunday Falana.
Sauran su ne Remi Ayoade, Olarenwaju Emmanuel, Babatunde Ige da Adebayo Mariam.
Makinde ya ba 'yan majalisar OYSIEC shawara
"Ku mambobin OYSIEC, aikin da ke gabanku aiki ne mai matukar muhimmanci. Duk da cewa ni na naɗa ku, majalisar dokoki ce ta tantance ku."
"Akwai sunayen da ke cikin hukumar da dole ku yi koyi da su, wadannan su ne Oyo da kuma cin gashin kai. Kalmar da ta fi muhimmanci ita ce ’yanci, don haka dole ne ku kasance masu zaman kansu.”
"Za ku yi wa al’ummar jihar Oyo adalci idan kuka gudanar da aikinku cikin gaskiya da tsoron Allah, kamar yadda kuka rantse.”
- Gwamna Seyi Makinde
Me Makinde zai yi kafin ya bar ofis
Gwamnan ya ce yana da tabbacin cewa al’ummar jihar Oyo suna goyon bayan gwamnatinsa, don haka ba su tsoron zuwa zaɓe.
"Mu a nan jihar Oyo, tabbas zan gudanar da zaɓen ƙananan hukumomi kafin na bar ofis. Wa’adin shugabannin ƙananan hukumomin yanzu zai ƙare a watan Mayun 2027.”
- Gwamna Seyi Makinde

Source: Twitter
Da yake magana kan naɗin shugaban hukumar da mambobinta, Makinde ya ce mutane ne masu kyakkyawan suna da nagarta, waɗanda za su yi amfani da kwarewarsu wajen bunƙasa ci gaban jihar.
Ya kuma gode wa majalisar dokokin jihar Oyo bisa goyon baya da jajircewa wajen amincewa da waɗanda aka naɗa, yana mai jaddada cewa hakan ya nuna kyakkyawar haɗin kai tsakanin bangaren zartarwa da na majalisa.

Kara karanta wannan
Duk da samun jihohi 28, Shugaba Tinubu ya hango matsalar da ta tunkaro jam'iyyar APC
Rikicin Gwamna Makinde da Wike
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, ya yi tsokaci kan rikicinsa da Nyesom Wike a jam'iyyar PDP.
Gwamna Makinde ya bayyana cewa rikicin da ke cikin PDP ya shafi makomar dimokuraɗiyyar Najeriya, ba wai batun jam’iyya kawai ba.
Makinde ya zargi tsohon gwamnan Rivers, Nyesom Wike da kokarin kakaba jam'iyya daya a Najeriya, wanda a cewarsa, ya saba da kudurin 'yan mazan jiya.
Asali: Legit.ng

