Abin da Talakawan Najeriya Za Su Saka Wa Bola Tinubu da Shi a Babban Zaben 2027

Abin da Talakawan Najeriya Za Su Saka Wa Bola Tinubu da Shi a Babban Zaben 2027

  • Gwamna Babajide Sanwo-Olu na jihar Legas ya ce yan Najeriya za su saka wa Bola Ahmed Tinubu da kuri'unsu a zaben 2027
  • Mai girma gwamnan ya ce matakan da Tinubu ya dauka na farfado da Najeriya kadai sun isa su sa 'yan Najeriya kara zabensa a karo na biyu
  • Ya kuma bayyana yadda APC ta samu karin gwamnoni daga 20 zuwa 29, yana mai cewa duka sun amince su marawa Tinubu baya

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Lagos, Nigeria - Gwamnan Jihar Lagos, Babajide Sanwo-Olu, ya bayyana kwarin gwiwar cewa ‘yan Najeriya za su sake zabar Shugaba Bola Tinubu a zaben shekarar 2027.

Gwamna Sanwo-Olu ya ce babu abin da 'yan Najeriya za su saka wa Bola Tinubu da shi wanda ya wuce sake zabensa a karo na biyu a zabe mai zuwa.

Kara karanta wannan

2027: Kawu Sumaila ya fadi zabinsa daga cikin masu son takarar gwamna a Kano

Gwamna Babajide Sanwo-Olu.
Gwamnan jihar Legas da ke Kudancin Najeriya, Babajide Sanwo-Olu Hoto: @babjidesanwoolu
Source: Getty Images

Gwamna Sanwo-Olu ya bayyana hakan ne a ranar Litinin yayin wata hira da ya yi a shirin Journalists Hangout na gidan talabijin na TVC.

Me 'yan Najeriya za su saka wa Tinubu da shi?

Ya ce babu shakka ‘yan Najeriya za su saka wa Shugaba Tinubu ta hanyar sake zabensa a 2027, duba da kyawawan sakamakon tsare-tsaren da ya aiwatar, wadanda suka shafi inganta ababen more rayuwa a fadin kasar.

A cewarsa, ‘yan Najeriya za su sake zabar Shugaba Tinubu ne saboda ya aiwatar da manyan sauye-sauye tare da cika yawancin alkawurran da ya dauka ga al’umma.

"Shugaba Bola Tinubu na da kyakkyawar damar samun nasara a 2027, saboda gyare-gyaren da ke cikin ajandar Renewed Hope sun yi tasiri sosai wajen inganta shugabanci da ababen more rayuwa a fadin kasar.
“A wannan gwamnati, kudaden shiga sun karu ga gwamnatin tarayya da na jihohi. Farashin kayan abinci ya ragu, ba wanda zai musa hakan.

Kara karanta wannan

'Shirya komai aka yi': An 'gano' yadda rashin tsaro ya fara a Najeriya

"Mun ga karuwar jarin kasashen waje da ke shigowa kasar. Mun ga mutane da dama na nuna sha’awar shigowa su zuba jari. Hatta ‘yan Najeriya da ke zaune a kasashen waje suna dawowa gida.”

- Gwamna Sanwo-Olu.

Ya kara da cewa har yanzu akwai kalubale, amma Shugaba Tinubu mutum ne mai basira, yana yin iyakar kokarinsa wajen ganin komai ya dawo kan hanya.

Gwamnonin APC sun karu daga 2023

A bangaren siyasa, Gwamna Sanwo-Olu ya ce goyon bayan da Tinubu ke samu daga gwamnoni ya karu, kamar yadda Leadership ta ruwaito.

Ya ce:

“Bayan zaben 2023, muna da kusan gwamnoni 20 na APC, amma a yau muna da gwamnoni 28 ko 29, wannan ma’auni ne na nasara.
"Shugaba Tinubu mutum ne da ya jajirce wajen tattaunawa kan makomar Najeriya. Zai yi nasara, kuma za mu ba shi cikakken goyon baya.
“Ina da tabbacin cewa ‘yan Najeriya za su sake zabar Shugaba Tinubu, saboda suna ganin cewa wannan shugaban ya yi aiki tukuru. Ya aiwatar da abubuwa da dama da ya yi alkawarin yi. ‘Yan Najeriya za su kada masa kuri’a.”
Shugaba Bola Tinubu.
Shugaba Bola Ahmed Tinubu yana dana wa waagoya bayansa hannu Hoto: OfficialABAT
Source: Twitter

Gwamnan Legas ya gabatar da kasafin 2026

Kara karanta wannan

Duk da samun jihohi 28, Shugaba Tinubu ya hango matsalar da ta tunkaro jam'iyyar APC

A wani labarin, kun ji cewa Gwamna Babajide Sanwo-Olu ya gabatar da kasafin kuɗin jihar Legas na 2026 mai darajar Naira tiriliyan 4.2 ga majalisar dokoki.

A jawabin da ya gabatar wa ’yan majalisa, Sanwo-Olu ya bayyana cewa.kasafin ya kunshi tsare-tsare da za su inganta rayuwa, bunkasa tattalin arziki da sauransu.

Ya ce an ware fiye da N2.18tn domin manyan ayyukan raya kasa, yayin da aka ware N2.05tn domin kudin gudanarwa na gwamnati.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262