Tsagin NNPP na Son Jawo Matsala bayan Babban Taron Su Kwankwaso a Abuja
- Tsagin jam’iyyar NNPP a Jihar Kano ya yi watsi da sakamakon babban taron ƙasa da aka gudanar a birnin Abuja, yana mai cewa zaman bai halasta ba
- Shugaban tsagin jam'iyyar, Mas’ud Doguwa, ya ce an karya doka da ka’idoji, kuma ba za su amince da duk wani mataki da ya saɓa wa umarnin kotu ba
- Sanata Doguwa ya jaddada cewa dole ne a fara sulhu na gaskiya kafin a gudanar da duk wani sahihin taro ko tsarin jagoranci a jam’iyyarsu ta NNPP
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Wani tsagi na jam'iyyar hamayya na NNPP a Jihar Kano ya bayyana ƙin amincewa da sakamakon babban taron jam’iyyar da aka gudanar a Abuja.
Tsagin jam'iyyar da ke adawa da bangaren su Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya bayana cewa taron bai halatta ba, kuma ya saba doka.

Source: Facebook
Wannan na kunshe a cikin hira da Shugaban tsagin a Kano, Sanata Mas’ud Doguwa, ya yi da jaridar Punch awanni kadan bayan taron da su Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso suka yi a Abuja.
Tsagin NNPP ya soki taron jam'iyya
Mas'ud Doguwa, wanda tsohon Sanata ne ya ce ɓangarensa na biyayya ga dokar kasa, kuma ba zai goyi bayan duk wani aiki na jam’iyya da aka gudanar ba tare da la’akari da shari’o’in da ke gaban kotu ba.
A cewarsa, ba za a iya gina jam’iyyar dimokuraɗiyya bisa saba doka ba, domin mutunta kotu da dokoki shi ne ginshiƙin tsarin siyasa na gaskiya.
A cewarsa, taron da aka yi a Abuja bai kunshi kowa da kowa ba, kuma bai wakilci ƙasa gaba ɗaya ba. Ya yi ikirarin cewa an ware muhimman masu ruwa da tsaki daga tsarin.
Ya ce abin da aka kira taron ƙasa ba komai ba ne illa taron Kano ko kuma taron Kwankwasiyya, domin ba a tuntube su ba, ba a gayyace su ba, kuma taron ya kasance na ɓangare guda kaɗai.
Shugaban tsagin NNPP ya nemi sulhu
Sanata Doguwa ya jaddada cewa dole ne a yi sulhu na gaskiya kafin duk wani sahihin taro ko tsarin jagoranci a cikin jam'iyyar NNPP.
Ya yi gargaɗi cewa yunƙurin ɗora shugabanci ba tare da cimma matsaya tsakanin ɓangarori ba zai ƙara tsananta rabuwar kai a jam’iyyar.

Source: Facebook
A cewarsa, idan ana son zaman lafiya a NNPP, dole ne a kafa kwamitin sulhu na gaskiya tun farko, domin sai bayan hakan ne za a iya samun haɗin kai na ainihi.
Haka kuma, Doguwa ya yi watsi da jita-jitar da ke cewa ɓangarensa na goyon bayan wani ɗan takara gabanin zaɓen 2027, musamman takarar gwamnan Kano.
Ya ce 'yan jam’iyyar da dama na cikin damuwa da rashin jin daɗi, don haka babu wani dalili na goyon baya ga kowane ɗan takara a wannan lokaci.
Jam'iyyar NNPP ta yi sabon Shugaba
A baya, kun ji cewa jam'iyyar adawa ta NNPP ta gudanar da babban taronta na ƙasa inda ta zaɓi shugabannin da za su jagoranci harkokinta na tsawon shekaru huɗu masu zuwa.
Taron ya gudana ne a Abuja, babban birnin tarayya, inda wasu jiga-jigan jam’iyyar daga sassa daban-daban na ƙasar nan suka halarta domin tattauna muhimman batutuwa da zaben shugabanni.
A taron, jam’iyyar NNPP ta sake zaɓen Ajuji Ahmed a matsayin shugaban jam’iyyar na ƙasa ba tare da hamayya ba, abin da ke nuna amincewar 'ya'yan jam’iyyar da salon jagorancinsa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


