Gwamnoni na Shiga APC, Kwankwaso Ya Yi Magana kan Abba Kabir da NNPP
- Jagoran NNPP na kasa, Rabiu Musa Kwankwaso, ya bayyana kwarin gwiwar cewa jam’iyyar za ta taka rawar gani a zabe mai zuwa
- Kwankwaso ya yaba da yadda jam’iyyar ta tsara kanta da kuma yadda ta gudanar da taron shugabancinta na kasa cikin tsari da ladabi
- Ya ce shugabannin NNPP sun jaddada hadin kai da tsayin daka, tare da cewa jam’iyyar za ta kammala manyan shirye-shirye kafin 2027
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – 'Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP a zaben 2023, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya bayyana cewa jam’iyyarsu na cikin shiri kuma tana da yakinin za ta yi fice a zaben 2027.
Kwankwaso, wanda shi ne Jagoran NNPP na kasa kuma tsohon gwamnan jihar Kano, ya yi wannan jawabi ne yayin taron kwamitin zartarwa na kasa (NEC) na jam’iyyar da aka gudanar a Abuja.

Kara karanta wannan
Duk da samun jihohi 28, Shugaba Tinubu ya hango matsalar da ta tunkaro jam'iyyar APC

Source: Twitter
Legit Hausa ta tattaro bayanai game da taron jam'iyyar NNPP a cikin wani sako da hadimin Kwankwaso, Saifullahi Hassan ya wallafa a X.
Rabiu Kwankwaso ya yaba da tsarin NNPP
A jawabinsa, Kwankwaso ya yaba da yadda NNPP ta tsara kanta tun daga matakin kasa har zuwa jihohi, yana mai cewa wannan ne ginshikin nasarar kowace jam’iyya.
Kwankwaso ya kara da cewa yadda jam’iyyar ta gudanar da tarukan zabukan cikin gida a fadin kasar nan cikin ladabi da bin doka alama ce karara cewa NNPP ta shirya tsaf domin zaben 2027.
Maganar Kwankwaso kan Abba Kabir Yusuf
Tsohon gwamnan ya gode wa gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, bisa goyon baya da kuma yadda yake tafiyar da mulki. Ya ce irin rawar da gwamnan ke takawa na karfafa jam’iyyar a idon jama’a.
Mataimakin gwamnan Kano, Aminu Abdulsalam Gwarzo ne ya wakilci Abba Kabir Yusuf a taron jam'iyyar a Abuja.

Kara karanta wannan
An gano dalilin da ya sa Buhari ya sauya fasalin Naira daf da zaɓen Tinubu a 2023

Source: Facebook
Ya bukaci mambobin jam’iyyar da su ci gaba da nuna hadin kai, fahimtar juna da sadaukarwa, yana mai jaddada cewa wadannan su ne muhimman makaman da NNPP ke bukata domin cimma burinta a zabe mai zuwa.
Vanguard ta rahoto Kwankwaso ya ce nasarar jam’iyyar ba ta rataya ga mutum daya ba, sai da hadin kan kowa da kowa da bin tafarkin jam’iyya.
Jawabin shugaban NNPP na kasa
A nasa jawabin, Shugaban NNPP na kasa, Dr Ajuji Ahmed, ya yaba da hadin kai da juriyar jam’iyyar duk da kalubalen da ta fuskanta.
Ya lissafa nasarorin NNPP da suka hada da jagoranci mai karfi, daidaito tsakanin mambobi da rikon amana ga manufofin jam’iyyar.
Haka zalika ya kuma yaba da ayyukan gwamna Abba Kabir Yusuf a bangarorin ilimi, lafiya, gine-gine da ci gaban dan Adam.
Ahmed ya bayyana Kwankwaso a matsayin jagoran siyasar Kano da kuma ginshikin siyasar Najeriya, yana mai cewa jam’iyyar ta tsaya tsayin daka a bayansa.

Kara karanta wannan
Bayan ganin bidiyon Bello Turji, APC ta hango dalilin alakanta Matawalle da 'yan bindiga
Gwamnan Filato ya shiga jam'iyyar APC
A wani labarin, kun ji cewa gwamnan jihar Filato, Caleb Mutfwang ya fita daga jam'iyyar PDP zuwa APC mai mulki a Najeriya.
Gwamnan ya koma APC ne yayin da gwamnonin PDP, Sanatoci da 'yan majalisar tarayya da na jihohi ke rububin shiga APC.
Shugaban APC na kasa ne ya sanar da sauya shekar Caleb Mutfwang yayin taron masu ruwa da tsaki na jam'iyyar a Abuja.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng