Duk da Samun Jihohi 28, Tinubu Ya Hango Matsalar da Ta Tunkaro Jam'iyyar APC
- Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya ja kunnen jam'iyyar APC mai mulki yayin da ake shirin tunkarar babban zaben shekarar 2027
- Mai girma Tinubu ya nuna cewa duk da gwamnoni 28 da APC take da su, tana bukatar yin aiki tukuru domin samun nasara a zaben gaba
- Shugaba Tinubu ya bukaci ta samar da tsare-tsaren da za ta iya yin nasara a jihohin da ba ta da karfin iko
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi gargaɗi ga jam’iyyar APC cewa ikon da take da shi a jihohi 28 a halin yanzu ba tabbacin nasarori a zaben gaba ba ne.
Shugaba Tinubu ya jaddada cewa dole jam’iyyar ta samar da tsare-tsaren siyasa a jihohin da ba ta da gwamnoni, idan ba haka ba za ta fuskanci abin da ya kira “rashin katabus” gabanin babban zaɓen 2027.

Source: Facebook
Jaridar Leadership ta kawo rahoto cewa Tinubu ya faɗi hakan ne a taron kwamitin zartarwa na kasa (NEC) na APC da aka gudanar a cikin fadar shugaban kasa da ke birnin Abuja.
An bukaci a goyi bayan Bola Tinubu
A wajen taron, mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima, shugaban majalisar dattawa Godswill Akpabio da shugaban majalisar wakilai Tajudeen Abbas, sun bukaci shugabannin jam’iyyar su ci gaba da goyon bayan Mai girma Tinubu.
Sun kuma yi kiran a samar da haɗin kai, daidaiton kawance da kuma ƙarfafa alaƙar bangaren zartarwa da majalisa domin shirin zaɓen gaba.
Me Tinubu ya ce kan jam'iyyar APC?
Tinubu ya ce wajibi ne jam’iyyar ta kasance a ankare a jihohin da ba ta da iko a halin yanzu, yana mai nuna cewa cin zaɓen gwamna da ci gaba da rinjaye a zaɓe na buƙatar tsari mai karfi a matakin jiha, ba sakaci ba.
“Ya batun jihohin da ba mu da gwamnoni? Dole jam’iyya ta kasance a ankare kuma ta shirya samar da gwamnoni."
“Idan tsari bai yi tasiri ba, ba za ku samar da gwamna ba, kuma tasirinku zai ragu."
- Shugaba Bola Tinubu
Kashim Shettima ya yaba wa Tinubu
Da yake jawabi a wajen taron, Kashim Shettima ya yaba kan cigaban siyasar Tinubu wajen karfafa adawa.
Ya yaba masa kan samar da tsare-tsaren adawa a Najeriya tun kafin haɗewar jam’iyyu a 2013 da ta haifar da APC, jaridar The Nation ta dauko labarin.

Source: Twitter
Shettima ya ce faɗaɗar jam’iyyar da karɓuwarta a kasa baki ɗaya sun samo asali ne daga adawa da mulkin jam’iyya ɗaya.
"Ba hakanan banza kawai siyasar adawa ta tsira a Najeriya ba. Ta tsira ne saboda mutum ɗaya ya ƙi mika wuya ya bar fagen siyasa."
- Kashim Shettima
Ya kuma yi watsi da ra’ayin cewa hayaniyar kafafen sada zumunta na iya cin zaɓe, yana mai jaddada cewa nasarar zaɓe tana zuwa ne ta hanyar kawance da sahihanci.
Tinubu ya yi wa gwamnoni barazana
A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya ja kunnen gwamnoni kan kudin kananan hukumomi.
Shugaba Tinubu ya bukaci gwamnoni su rika ba kananan hukumomin kudinsu kamar yadda Kotun Koli ta yi umarni.
Hakazalika, Shugaba Tinubu ya yi musu barazanar cewa zai umarci a rika turawa kananan hukumomi kudinsu kai tsaye, idan har ba su mutunta hukuncin kotun ba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


