Shettima Ya Kada Hantar 'Yan Adawa kan Tazarcen Shugaba Tinubu a 2027
- Mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima, ya aika sakonni masu zafi ga 'yan adawa kan babban zaben shekarar 2027 da ake tunkara
- Kashim Shettima ya bayyana cewa akwai babban kuskure wani dan adawa ya yi yunkurin kalubalantar Shugaba Bola Tinubu a zaben 2027
- Mataimakin shugaban kasar ya kuma bayyana cewa ba a samun nasarar zabe a shafukan sada zumunta irinsu Facebook da X
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Gabanin babban zaɓen 2027, mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima ya gargaɗi ’yan adawa kan tazarcen Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Shettima ya ja kunnen 'yan adawa da kada su yi yunkurin kalubalantar Tinubu a zaɓen shugaban kasa na 2027, yana mai cewa irin wannan yunkuri na iya zama babbar wauta.

Source: Twitter
Jaridar The Nation ta ce Shettima ya yi wannan gargaɗi ne a ranar Juma’a, 19 ga watan Disamban 2025 yayin taron kwamitin zartarwa na kasa (NEC) karo na 15 na jam’iyyar APC.

Kara karanta wannan
Duk da samun jihohi 28, Shugaba Tinubu ya hango matsalar da ta tunkaro jam'iyyar APC
An gudanar da taron na jam'iyyar APC ne a dakin taro na fadar shugaban kasa da ke babban birnin tarayya Abuja.
Me Shettima ya gayawa 'yan adawa kan Tinubu?
Tsohon gwamnan na jihar Borno ya ce duk wanda ke da burin tsayawa takara da shugaban kasa Tinubu a 2027 yana shiga abin da ya kira "tafiyar da babu riba".
"Sai wawa da ya kudurta tafiya hanyar halaka ko kuma cikakken mai yaudara ne kawai zai iya kalubalantar shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu a zaɓen 2027."
"Duk da haka, muna cikin dimokiraɗiyya, kuma kowa na da ’yancin tsayawa takara.”
- Kashim Shettima
Ko da yake ba a saka shi a jadawalin masu jawabi tun farko ba, an gayyaci Shettima ya hau mumbari ne bisa umarnin shugaban kasa domin ya yi takaitaccen jawabi.
Shettima: Ba a cin zabe da hayaniya
Ya kuma yi gargaɗin cewa ba a cin zaɓe da hayaniyar kafafen sada zumunta, yana mai jaddada cewa nasara a zaɓe tana zuwa ne ta hanyar haɗin gwiwa mai karfi, sahihanci da shiri mai kyau, tashar Channels tv ta dauko labarin.

Source: Twitter
Shettima ya ce abubuwan da suka faru sun nuna cewa shahara a intanet kaɗai ba ya kai ga nasarar zaɓe, inda ya nuna cewa yin suna sosai a kafafen sada zumunta kamar Facebook da X ba tabbacin cin zaɓe ba ne.
"Ba a cin zaɓe da hayaniya ko tunanin baya. Ba a gudanar da zaɓe a Facebook ko Twitter. Ana cin zaɓe ne ta hanyar haɗin kai, sahihanci da kwarin gwiwa.”
- Kashim Shettima
Fasto ya bukaci a cire Shettima
A wani labarin kuma, kun ji cewa Fasto Ezekiel Dachomo ya koka kan yadda aka samu shugaban kasa da mataimakinsa duk Musulmai a Najeriya.
Fasto Ezekiel Dachomo ya ce abin takaici ne yadda aka samu shugaban kasa Bola Tinubu da mataimakinsa, Kashim Shettima dukkaninsu Musulmai, lamarin da ya kira barazana ga kiristoci.
Ya yi kira da a cire Kashim Shettima tare da maye gurbinsa da Kirista domin yi wa Kiristoci adalci a siyasar Najeriya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
