Tsofaffin 'Yan Majalisa Sun Kawo Wanda Suke Fatan Ya Zama Gwamnan Kano a 2027

Tsofaffin 'Yan Majalisa Sun Kawo Wanda Suke Fatan Ya Zama Gwamnan Kano a 2027

  • Sanata Barau I. Jibrin ya samu goyon baya a shirin da ake ganin yana yi na neman takarar gwamnan Kano a zaben 2027
  • Tsofaffin 'yan majalisar tarayya daga Kano sun bayyana Barau a matsayin wanda ya cancanci ya karbi ragamar mulki a zabe na gaba
  • Sun kuma ayyana goyin bayansu ga tazarcen shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu domin ya cika shekaru takwas a kan mulki

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kano, Nigeria - Tsofaffin ‘yan majalisar tarayya daga Jihar Kano sun bayyana goyon bayansu ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu domin ya yi tazarce zuwa wa’adi na biyu.

Sun kuma nuna cikakken goyon baya ga Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau I. Jibrin, a matsayin ɗan takarar gwamnan Kano na APC a zaben 2027.

Tsofaffin yan Majalisa.
Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Barau Jibrin tare da tawagar tsofaffin 'yan majalisar Kano Hoto: @barauijibrin
Source: Twitter

Sanata Barau Jibrin ya tabbatar da hakan a wani sako da ya wallafa a shafinsa na X yau Juma'a, 19 ga watan Disamba, 2025.

Kara karanta wannan

Kashim Shettima ya kada hantar 'yan adawa kan tazarcen Tinubu a 2027

Tinubu da Barau sun samu goyon baya

Tsofaffin 'yan majalisar, wadanda suka yi aiki a Jamhuriyya ta Biyu, ta Uku da kuma Jamhuriyya ta Huɗu ta yanzu, sun bayyana matsayarsu ne yayin wata ziyara da suka kai wa Sanata Barau a Abuja a ranar Juma’a.

Shugaban tawagar, Hon. Umar Sadiq, wanda ya wakilci mazaɓar Kumbotso daga 1979 zuwa 1983, ya ce goyon bayansu ga Tinubu da Sanata Barau ta samu amincewa daga dukkan mambobin ƙungiyar.

Hon. Sadiq ya ce za su yi duk mai yiwuwa wajen wayar da kai da haɗa kan jama'a domin ganin an cimma burin tazarcen Shugaba Tinubu da kuma burin Sanata Barau na zama gwamnan Kano.

Ya ce:

“Wannan shi ne karo na biyu da muke nuna goyon baya ga Sanata Barau a matsayin ɗan takarar gwamnan jiharmu. Shi mamba ne a wannan ƙungiya, kuma shi ne na farko a jerin sunayenmu.
"Haka kuma, mun amince da Shugaba Tinubu domin ya sake tsayawa takarar wa’adi na biyu. Ba mu da wani ɗan takara face Sanata Barau. In sha Allahu, shi ne gwamnan Kano na gaba. "

Kara karanta wannan

Tsaro ne kan gaba da Shugaba Tinubu ya gabatar da kasafin kudin 2026 a Majalisa

Maratanin Barau ga tsofaffin 'yan majalisa

Da yake mayar da martani, Sanata Barau Jibrin ya gode wa tsofaffin ‘yan majalisar, yana mai bayyana su a matsayin ginshiƙin siyasar Kano.

“Wannan ƙungiya taku ni ma tawa ce, kuma abin farin ciki ne ganin kun mara wa wannan tafiya baya domin ceto Kano daga halin da take ciki a yanzu. Wannan tafiya ta ceto ce.
“Gazawar shugabanci ce ta jefa Kano cikin koma baya. Ana tafiyar da jihar kamar kamfani mai zaman kansa. Ba za mu zauna muna kallo abubuwa na ƙara tabarbarewa ba," in ji Barau.
Sanata Barau Jibrin.
Mataimakin shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau I. Jibrin Hoto: Barau I. Jibrin
Source: Facebook

Wani dan Kano, Aminu Sulaiman ya shaidawa Legit Hausa cewa duk wannan yunkurin da su Barau da yan tawagarsa ke yi ba zai hana su sake zaben Abba Gida-Gida a karo na biyu ba.

Ya ce sun gwada Abba kuma yana da yakinin sama da kaso 90 na wadanda suka zabi NNPP sun san kwanlliya na biyan kudin sabulu.

Kara karanta wannan

Bayan shiga APC, Gwamna Fubara ya bayyana shirinsa kan tazarcen Tinubu a 2027

Malam Aminu ya ce:

"Ba na tunanin Kanawa za mu juya wa Abba da Kwankwaso baya, wannan gwamnatin ta yi kokari kuma tana kan yi domin talakawa na amfana da tsare-tsarenta.
"Ba zan ce babu kuskure ba, amma na san abubuwan alherin da Gwamnatin Abba ke yi a Kano ya zarce kura-kuranta, don haka ni dai ba zan bar Abba na dauko wani ba, duk da Barau mutumin kirki ne, akwai taimako."

Matasa sun goyi bayan Tinubu da Barau

A wani labarin, kun ji cewa Shugaba Bola Tinubu da Sanata Barau Jibrin na kara samun goyon baya a jihar Kano yayin da ake shirye-shiryen tunkarar babban zaben 2027.

Kungiyoyin matasa daga jihar Kano sun bayyana cikakken goyon bayansu ga Shugaban Kasa, Bola Tinubu domin wa’adi na biyu a 2027

Sun kuma bukaci Sanata Barau Jibrin da ya tsaya takarar gwamna a babban zaɓen 2027 domin kawar da gwamnatin Abba Kabir Yusuf.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262