Cakwakiya: Tinubu Ya Shiga Rudani da Aka Tafka Kuskure a Taron APC a Fadar Shugaban Kasa

Cakwakiya: Tinubu Ya Shiga Rudani da Aka Tafka Kuskure a Taron APC a Fadar Shugaban Kasa

  • An tafka kuskure yayin sanya taken Najeriya a wurin taron majalisar koli ta APC a fadar shugaban kasa da ke birnin tarayya Abuja
  • Taron, wanda ya gudana a daren ranar Alhamis, ya samu halartar Shugaba Bola Tinubu da mataimakinsa, Sanata Kashim Shettima
  • A wani faifan bidiyo da ke yawo a soshiyal midiya, masu kula da sauti sun yi kuskuren sanya tsohon taken kasa maimakon sabo a taron

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - An yi wani kuskure a taron majalisar ƙoli ta jam’iyyar APC da aka gudanar a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja, a daren Alhamis, 18 ga watan Disamba, 2025.

Lamarin ya faru ne lokacin da mai kula da kayan sauti zai sanya taken Najeriya da za a bude taron da shi, sai dai ya yi kuskuren sanya tsohon taken kasa maimakon sabo.

Kara karanta wannan

Tinubu, gwamnoni, sun hallara a fadar Aso Rock, APC ta shirya muhimmin taro

Taron APC.
Shugaba Bola Tinubu, Kashim Shettima da sauran jiga-jigai a taron APC a fadar shugaban kasa Hoto: @OfficialAPCNig
Source: Twitter

The Cable ta ruwaito cewa taron ya gudana ne a babban ɗakin liyafa na fadar shugaban ƙasa, inda Shugaba Bola Ahmed Tinubu da Mataimakinsa, Kashim Shettima, suka halarta.

Wane kuskure aka yi a taron APC?

Shugaban Majalisar Dattawa Godswill Akpabio, da Kakakin Majalisar Wakilai Tajudeen Abbas na cikin manyan jagororin da suka halarci wannan taro a Aso Rock Villa.

Kuskuren ya faru ne bayan shigowar manyan kusoshi cikin ɗakin taron, lokacin da ake shirin rera taken ƙasa. Wani mai suna Okezie Atani ya wallafa bidiyon a X.

Masu kula da sauti sun fara sanya waƙar tsohon taken ƙasa na “Arise, O Compatriots”, lamarin da ya jefa Shugaban Ƙasa da sauran shugabannin jam’iyyar cikin ruɗani na ƴan dakiku kaɗan.

Bayan fahimtar kuskuren, shugaban masu kula da sautin ya yi gaggawar gyarawa cikin hanzari, inda ya dawo da sabon taken ƙasa da aka dawo da shi, “Nigeria, We Hail Thee."

Kara karanta wannan

Tinubu ya fadi alkawarin da ya yi wa Amurka da Turai kan tsaron Najeriya

Yadda Tinubu ya canza taken Najeriya

A ranar 29 ga Mayu, Shugaba Tinubu ya rattaba hannu kan dokar da ta mayar da tsohon taken ƙasar “Nigeria, We Hail Thee”, wanda aka fara amfani da shi daga shekarar 1960 zuwa 1988.

Taken da aka yi amfani da shi daga 1978 zuwa farkon 2024 shi ne “Arise, O Compatriots," amma bayan Tinubu ya karbi mulki, ya sake dawo da wancan tsohon.

Wannan shi ne taron majalisar ƙoli na APC na farko da Farfesa Nentawe Yilwatda ya jagoranta a matsayin sabon shugaban jam’iyyar na ƙasa.

Shugaban APC.
Shugaba Bola Ahmed Tinubu na gaisawa da shugaban APC na kasa, Farfesa Nentawe Hoto: APC Nigeria
Source: Twitter

Gwamnoni da suka hada da Peter Mbah (Enugu), Siminialayi Fubara (Rivers), Sheriff Oborevwori (Delta), Umo Eno (Akwa Ibom), Agbu Kefas (Taraba) da Douye Diri (Bayelsa) sun halarci taron karo na farko tun bayan sauya sheƙarsu daga PDP zuwa APC.

Sauran mahalarta taron sun haɗa da tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa Yemi Osinbajo, mambobin kwamitin gudanarwa na APC, gwamnonin jam’iyyar, da shugabannin majalisun tarayya.

Kara karanta wannan

Sarki ya hada tawaga zuwa wajen Tinubu, sun goyi bayan tazarcensa a 2027

Gwamnan Filato ya bar PDP zuwa APC

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnan jihar Filato, Caleb Mutfwang, ya sauya sheka daga jam'iyyar PDP zuwa APC mai mulki a Najeriya.

Shugaban APC na kasa, Farfesa Nentawe Yelwata, wanda shima ɗan jihar Filato ne, ya sanar da ficewar gwamnan daga jam'iyyar PDP.

Yilwatda ya ce da sauya shekar Gwamna Mutfwang, yanzu dukkan yankin Arewa ta Tsakiya yana karkashin mulkin jam’iyyar APC.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262