An Yi Baki 2 game da Sauya Shekar Tsohon Gwamna Attahiru Bafarawa zuwa APC

An Yi Baki 2 game da Sauya Shekar Tsohon Gwamna Attahiru Bafarawa zuwa APC

  • Tsohon gwamnan jihar Sakkwato, Attahiru Daljatu Bafarawa ya musanta rade-radin komawarsa jam’iyya mai mulki ta APC
  • Bafarawa ya ce ya yi ritaya gaba daya daga siyasar neman kujera, saboda haka danganta shi da wata jam'iyya ba daidai ba ne
  • Sai dai dattijon ya bayyana cewa magoya bayansa ba su daina siyasa ba, kuma kowa na da 'yancin shiga jam'iyya da ya so

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar SokotoTsohon gwamnan jihar Sokoto, Attahiru Dalhatu Bafarawa, ya nesanta kansa daga rade-radin cewa ya koma jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya.

Alhaji Bafarawa ya jaddada cewa ya riga ya yi ritaya daga siyasa, kuma ba shi da niyyar shiga kowace jam’iyya ta siyasa a halin yanzu.

Kara karanta wannan

Gwamna Makinde ya ba da tabbaci kan sauya sheka zuwa jam'iyyar APC

Attahiru Bafarawa ya karyata shiga APC
Tsohon gwamnan Jihar Sakkwato Attahiru Bafarawa Hoto: Attahiru Bafarawa
Source: Twitter

Bafarawa ya bayyana hakan ne a wata hira da BBC Hausa, bayan da aka ga dubunnan magoya bayansa sun sauya sheka zuwa jam’iyyar APC a jihar Sokoto.

Bafarawa: “Na bar siyasa gaba daya”

Bafarawa ya yi martani ga wani rahoto, wanda aka bayyana cewa ya koma jam'iyya mau mulki ta APC, da jaridar Aminiya ta wallafa.

Da yake karin bayani, Bafarawa ya ce tun da dadewa ya sanar da jama’a cewa ya daina siyasar neman kujera ko ta zabe ko ta nadi.

Ya ce wannan matsaya tasa ba ta sauya ba, duk da sauyin jam’iyyar da wasu daga cikin magoya bayansa suka yi.

A kalamansa:

“Na ce na bar siyasa, babu wata jam’iyya da zan shiga, abin da zan iya yi shi ne shiga kungiyoyin taimakon matasa da al’umma, amma ba siyasar jam’iyya ba.”

Kara karanta wannan

"Ba zan taba komawa APC ba," Sanata ya yi kaca kaca da gwamnoni 6 a Najeriya

Bafarawa ya ce masoyansa na da yancin shiga duk wata jam'iyya
Taswirar jihar Sakkwato, mahaifar tsohon gwamna Attahiru Bafarawa Hoto: Legit.ng
Source: Original

Tsohon gwamnan ya kara da cewa masoyansa ba su yi ritaya daga siyasa ba, don haka ba zai hana su neman makomarsu a siyasa ba saboda shi ya janye.

A cewarsa, magoya bayansa suna da cikakken ‘yanci su zabi jam’iyyar da suke ganin za ta amfane su, kuma su koma cikinta.

Yadda aka so Bafarawa ya sauya sheka

Ya ce wasu daga cikin magoya bayansu, wasu sun nemi shawara a wajensa kan jam’iyyar da za su shiga, amma ya ce ya bar musu shawarar da kansu.

A kalamansa:

“Na ce musu su je su yi shawara su zabi inda suke so. Daga baya suka dawo suka ce sun koma APC, sai na ce musu Allah Ya ba su sa’a."

Kara karanta wannan

Kano: Jigon ADC ya maka Ganduje a gaban kotu kan kafa Hisbah fisibilillahi

Attahiru Bafarawa ya ce kuskure ne a dauka cewa komawar magoya bayansa APC na nufin shi ma ya koma jam’iyyar.

Ya jaddada cewa tun da ya daina halartar tarukan jam’iyya ko shiga harkokin jam’iyya, ba za a kira shi dan wata jam’iyya ba.

Bafarawa ya yi martani ga Bello Turji

A wani labarin, kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Sakkwato, Alhaji Attahiru Bafarawa, ya kare kansa daga zargin da hatsabibin dan bindiga, Bello Turji, ya yi masa na danganta shi da ta'addanci.

Bello Turji ya fito tare da bayyana zargin cewa Bafarawa na da hannu wajen taimakawa ‘yan bindiga da ke addabar Arewacin Najeriya suna cin karensu babu babbaka da halaka jama'a.

Tun da farko, Bello Turji ya fitar da wani bidiyo inda ya zargi Bafarawa da wani tsohon gwamnan jihar Zamfara da cewa suna daga cikin mutanen da suka taimaka wajen rura wutar rashin tsaro a Arewa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng